← Book details Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 112 OF 141

Sashe 112

Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Anna ta bi Jauhara da kallo, haka ma ta bi IMAD da kallo

A tausashe , cike da jin nauyi ta ce" Ka dawo ka zauna Andadi "

Kwarai ta ji nauyi ya kamata, nauyi mai girman gaske,
Imad d'anta ne na farko fa, ina ita ina jin magana irin wannan? In banda abin MAZNA ma dan abinku ya haɗa ki da mijinki na lokaci daya kin hana masa hakinsa sai kin zo kin fada????......abinda Anna ke ta cicirawa a cikin zuciyarta kenan

Zaunawa yayi ya mayar da kansa jikin kujera ya jinginar ya fara dan Kada kaffafuwan nasa

A tausashe Anna ta dubi MAZNA ta ce" MAZNA, me yake faruwa ne?, idan ma AKOY wata damuwar da bata taka kara ta karya ba kawai ku yi magana tsakaninku ku shirya kanku kin ji y'ata? Shekara nawa da aurenku yanzu? Ai ina ga kun wuce matsayin ku ringa irin haka ko?..... Kun wuce matsayin a ji kanku haka da dauki haka y'ata........., ku iya zaunawa ku sasanta kanku komai girman laifi kafin wani ma ya ji tsakaninku kin ji ko???"

MAZNA ta gyada kai, a sanyaye ta ce" Anna, muna sasantawar, wannan din nake so ki shiga"

JAUHARA cike da takaicin irin yadda bata lankwasa harshe idan zata yiwa Anna magana ta sakar mata harara......., kai Subahanalah wai auntynta kalau take kuwa? To Anna ko ba maman IMAD bace ai ta kai matsayin da zata tausasa mata harshe kafin ta mata magana ko?, haba dan Allah....wani abin ai ba dadi Fisabililahi yaya za'a yi ace ba zata karyar da murya sosai ta yadda Anna din zata mugun jin tausayinta ba? Ita fa bata ma gane girman laifinta ba ga dukan alamu, wallahi kuwa tana cikin matsala saboda laifin da ta aikata Bama iya na taba lafiyar jikin ta zai sa ya yi fushi da ita ba kamar na wanda yayi mata aikin.....hum.

Anna ta ce" To shiKenan, ina sauraronki"

Kame kame ta shiga yi, ta kama nan, ta kama cen ta kasa fitowa sak ta yi maganarta har sai da Anna ta nuna mata cewar ta fa yi maganarta ba wani abu, sannan ta sake dubansa tace da shi tana mai umartarsa ko menene ya zauna kar yace zai tashi yayi tafiyarsa ba'a gama magana ba

Ajiyar zuciya ta sauke a raunane ta ce" Anna, wata goma da sati biyu kenan da na yi tafiya tunusia dan gyaran jikina.........., Anna na jima ina sport, ina shan du abubuwan da zasu iya taimaka min dan ganin na rage tumbin da nake fama da shi, da kirjina, Ama kamar kullum karuwa suke yi, har rashin lafiya na yi likita yayi ta fadan ina barin kaina da yinwa ne , da na fada masa dalili yace ai ba zan taba ramewa a yanzu ba, wata kibar halitta ce da damuwa ko kiyayewa ba zai sa ta ragu ba sai shekaru.....ko wata babbar cuta, sau kuwa idan Surgry aka yi......."

Ta yi dan shiru tana kallon sa ta ga bai dago din ba dai

A hankali ta ce" Anna, shine ya sa na nemi hanyar da za'a min aikin yadda ya dace kawai na je na yi ......."

Anna a hankali ta furta " Subahanalahi, wai kina nufin Surgry din ne da gaske kika yi? ......"........

Sai kuma ta dube shi saboda hannunsa na hagu ya daga ya kai wajen gashin kansa

Murya na rawa MAZNA ta ce" Anna, wallahi wallahi ban san abin nan zai dauki dogon lokaci irin wannan ba tare da na warke ba, Gayanan har ina neman daukan shekara ban warke ba kuma ban ba mijina hakins..........

"MAZNA!" Ya fada da karfin da ya sa ta zabura a tsorace tana zaunewa a wajen gaba daya maimakun dan tsugunon da ta yi........

Da sauri Anna ta saka hannunta ta rike nasa da jikinta da ya fara rawa, ta Dube shi, ta dubi MAZNA

Cikin kakkausar murya ya ce" Idan kin zo kin sa wace ta isa da Ni zaunawa in saurareki......, ki yi iya yinki ki kiyaye furucin da kike yi a gaban mahaifiyata..... MAZNA ki yi rspctng dinta!"

MAZNA na gyada kai da sauri ta furta" Ka yi hakuri dan Allah...., ban fada dan in raina Anna ba, na fada ne dan ina so Anna ta san girman laifin da na maka ta taya Ni baka hakuri dan Allah!"

Anna na dubanta ta ce" Ya Allah, MAZNA me ya aike ki zuwa ki taba lafiyar jikin ki?, me ya shiga kanki da har zaki je ki lalata lafiyarki? Kin kuwa san a long terme abin nan na haifar da damuwa irin na cuta kala kala?, kin kuwa san da yasa idan suka yi abin nan a cikin matsala suke kullum suna kai kawo ganin likita saboda idan yau nan bai haifar da wata cutar ba, gobe cen zai haifar?, MAZNA kin kuwa san cewar abin nan na iya haifar maki da ciwon da zai dame ki? Allah ya kiyaye ba fata na maki ba kin san da har Cancer yake haifarwa?, menene ya maki dadi a duniya da har zaki taba halittar da Allah ya maki da tabawa irin wannan?, na san ana gyara, ana gyara sosai, Ama me yasa ke naki gyaran kika yi irin wannan? Ko laifinka ne?, kai ka sa ta yi?, kai ne kake kushe halittar ta bayan ka san me ka aura har ka sa ta je ta aikata irin wannan danyan aikin dake iya lalata mata komai nata mai kyau?, IMAD????"

Idnanuwansa da suka yi jajajir ya kai kan ANNA, kafin ya maida kan MAZNA..........

Da kyar ya iya hanna kansa watsewa da bacin rai ya ce" Ni na aike ki yin wannan abin?, da kika yi saboda wa kika yi?, dama tafiya kika RINGA yi mai tsayi daga nan har tunusia dan kawai a maki wannan abin ba tare da izinina ba?, idan bakya tsoron ciwon dake iya kama ki zuwa gaba Bakya tsoron Allah ne?, ki fada min da kika je aka maida maki ciki haka baki da niyar haihuwa da Ni ne?????????......"

Ya rintse idannuwansa da suka masa nauyi ainun.....kafin ya dubi Anna murya a shake sosai ya ce" Ina iya tashi?"

Anna ta rasa eh zata ce masa ko a'a, ganin yadda matarsa ke kuka kamar ana yankata har ma kukan ya da Nur fitowa a gigice , haka ma FARHANA dake daf da kofar dama ta shigo da gudu a tsorace tana kallon MAZNA

MAZNA ta kama ƙafarsa ta ce" Akul plz"

Hannun Anna ya rike da dan karfi kadan ya ce" Anna.....plz"

A birkice Anna ke gyada masa kai, hakan ya sa ya mike tsaye.......

A rikice ta tashi ta rukunkume shi ta baya tana fashewa da wani kukan da ya tashi Inna tana salati da karfi kafin tace" Uban waye ke kuka!"

Hannayensa ya da ya bambareta daga jikinsa sannan ya ture ta gefe....., sai dai ta ki ta hakura ta sake komawa ta rike shi da karfi

Yanzun bayan ya cire ta daga jikinsa sai da ya tsaidata ta hanyar kama hananyenta yana duban cikin idannuwanta a kausashe ya ce" Idan kika yarda kika bi Ni inda zan je, sai na fito da hanjin dake cure maki daga jikinki MAZNA!, idan kika matse min waje ba zan taba tausaya maki ba!, MAZNA namiji ne ya Miki aikin nan ko?, namiji ne ya Miki?, MAZNA zuwa kika yi gaban wani namiji kika tube ya yi zane zane a jikinki kafin ya maki aiki???, MAZNA Ni kika wulakanta kika wulakantarwa igiyar aurena dake kanki........? Na taba nuna maki ina da bukatar ki rame ko kuwa na taba gajiyawa da ke???, tunda baki da kunya bari in taya ki idasa rashin kunyar , AKOY ranar da na zo maki ban baki abinda kike so ba?????, ko kuwa kadan na maki ban sani ba da har kika je kika sa aka rage ki??????"

A gaskiya zuwa yanzu Anna ta kai duke daga saman kujera ta rufa hijabinta kirif a saman kanta ta rufe ido, kunya fa tashin hankali sun mata yawa..............

Farhana kam hanyar da ta maidota ta mayar da ita salin alin

Kai harta Jauhara ta sada kai cike da jin nauyinsa, domin tunda take da shi bata taɓa ganinsa a irin yanayin nan fa furucin da yake fada ba

A rikice, kuma cikin matsanancin kuka MAZNA ta ce" Akul, dan ALLAH ka yi hakuri...... Akul ka yi hakuri dan Allah, duka ba daya, Akul ba daya, kawai na yi ne dan in sake birge ka!"

Kasa kasa , cikin bacin ran nan ya ce" ki birge Ni?, ta wace fuskar? Ta hanyar zuwa ki tube a gaban wani, ko kuma ta hana min hakina?...., MAZNA kin fita daga raina......, bana tunanin in zan iya ci gaba da zaman aure da ke........"

"Wayo Allahna kar ka sake Ni dan girman Allah "

Da sauri Anna ta mike tana nufar su ta ce" ANDADI!"

A birkice Ya sake ta daga rikon da ya mata........., yana kara matse mata waje ya ce" Maganar auren da nace maki zan yi, wallahi sai na yi.................."

Daga haka ya juya yana neman hanyar da zai bi ma, domin gaba daya wajen sai ya rikice masa ya rasa hanyar bi, karshe dai kicin din da Nur ke kofa tsaye ya durfafa......., bayan ya kara jaddada mata idan ta yarda ta bi shi wallahi dai ya zazago mata hanjin nan nata ta kasanta!

A rikice take son kubcewa daga hannun Anna, tuni ta cire hijabin, kuka take yi kamar ranta zai fita

Jikin Anna na rawa bayan ta kubce mata saboda karfin ba daya ba ta ce" MAZNA, zo nan, ki taho nan kar ki bi shi!"

Mazna na kuka ta ce" Wallahi sai dai ya kashe Ni Anna, sai na bi shi, sai dai ya kashe Ni, da ya min kishiya ko yayi tunanin wani abin dan kawai namiji ya min aiki gwara ya kashe Ni, na san idan gawata ya gani zai dangana ne!"

Ta nufi hanyar kicin din da ya bi ya shiga.......
Chapter 112 · 0% Book details