← Book details Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 92 OF 141

Sashe 92

Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya karashe yana murmushi ya fice, IMAD kuwa sai kawai ya gyada kai a ransa ya ayyana ' Eh zan je, kwarai zan je, ba normal bane wannan abin, kuma na san komai isar mutun da du wani abinda yake iya takama da shi na baiwa ko na cutarwa bai isa ni ya kayar min da gaba ba......, just yannayi ne ke zuwa a kan lokacin da nake hada ido da........da........da.......hm zan dai ga likitan'

Daga haka ya daga kansa yana kallon Anna da abinda ta riko

Mikewa yayi ya amsa ya ajiye yana murmushi ya ce" Ke kika girka Anna ?"

Anna ta yi murmushi ta zauna saboda a plate ta zubo abincin , a lokacin da FARHANA ke tafe tana turo kayan fruits da ta jero da su jus tana kallon Anna, Anna ta ce" Eh to, Farhana ce da su HALLAH "

Spoon din da ya dauka ya dan rike a hannunsa kafin ya mayar wa Anna kayanta bai ce komai ba

Ajiyewa FARHANA ta yi ta juya a ranta tana ayyana ' Yaya kenan, dama ka taba, da da wahala ka kuma cin na bangaren ka saboda ko shake Ni za'a yi na yi girki a shake nawa dai ya fi na MAZNA dadi saboda Ni ba kalar chef din da Anna bata sa ya koya min girki ba'

Anna ma murmushi ta yi ta ce" Ba zaka ci abincin y'ayana ba? Ka kuwa san bani da dar du inda zasu shiga su girka a ci na yarda????"

Fruits din nan kawai ya janyo ya shiga ci a hankali ya yi murmushi ya ce" Ci abinki Anna"

Anna ta yi murmushi itama ta ci gaba da ci har ta gama masu aiki suka kwashe saboda su Farhana sun haye sama da nasu ne

Da kula Anna ta ce" Andadi dangane da maganar Farhana ne da manemin auren nan nata nake so mu yi magana"

Da kula ya dubi Anna ya ce" Manemin auren ta?, Farhanan tana da wani saurayi ne Anna ?"

Anna ta ɗan sauke ajiyar zuciya a tausashe ta ce" Ka san yaron nan fa, inaga suna tare"

Da mamaki ya ce" wani yaron? Wanda na yi mata iyaka da shi?"

Anna ta dubi yanayinsa, ta ga kamar ransa na neman bacewa hakan ya sa a tausashe ta ce" Andadi, ka kwantar da hankalinka ka nutsu mu yi magana dan Allah, bana so ko kadan ka bata rai ko ka ce zaka yi wani abu a kan wannan lamarin, Ni na san cewa addu'ar da nake yi idan ba alkhairi Allah zai ture abin nan da kansa, tunda har Inna ta ture shekara nawa ba'a bar abin ba a yi hakuri ka yiwa Inna magana ka ce kai kace ya zo ya same ka , dan na fada mata a yau yau ya zo ya same ka , saboda na gaji ......na gaji IMAD....."

Sai Anna ta sada kanta saboda idannuwanta da suka tara kwallah

Hankalinsa ne yayi masifafen tashi

A hankali ya riko hannayen ta yana dubanta ya ce" Kuka ne kike yi? Ya Allah menene take yi yarinyar nan da ban sani ba har haka? Dama abinda Inna ke fada gaskiya ne? Ta ci gaba da ganinsa ne? Ya Allah"

Sai kawai ya nemi mikewa

Da sauri Anna ta saka hannayanta tana riko shi sannan ta saka karfinta dan ta nuna masa so take yi ya zauna

Kasa ya koma ya zauna a hankali yana daga dubansa ya saka a cikin idannuwan Anna a tausashe ya ce" Bana so ki mata kuka, idan kika mata kuka ai ta shiga uku, gwara in je in zane mata jiki in fasa mata jiki da in bari ki zubar mata da hawaye Anna "

Anna ta girgiza akai a tausashe ta ce" Ba na fada maka haka bane dan in daga maka hankali, hawayena kuwa ina yi ne a inda nake iya yi dan in ji sanyi kawai, saboda abinda ke saman zuciyata mai yawa ne Andadi......."

A tausashe ta ɗora da fadin" So nake yi ka yi mata aure, ina so a daura mata aure da shi din idan ya so sai a kaita gidanta, ina so in ga Farhana a ɗakinta, hakan ne kawai zai iya kwantar min da hankali Andadi...., plz ka amshe shi yau, ka zauna da shi, ka bashi damar turo da magabatansa, ka yi bincike a kansa......, ka san me yake yi a lokacin da ba mai ganinsa sai abokansa, ka yi bincike a kan addininsa, ba ruwana da samunsa, in dai ya fito daga gidan mutane masu mutunci ko me yake ci ta je ta ci, ta je ta yi biyayar aure ta yi bautar aure......, Andadi idan Inna tace da Farhana an fito daga yawon bana rintsawa, idan na je barci baya iya daukana, zuciyata sai ta yi ta bugawa , bana so in mutu bata shiga ɗakinta ba, bana so in mutu in bar maka ita a irin wannan halin, sam ba zasu zaunu da MAZNA a haka ba, ba zasu taba zama Inuwa daya da MAZNA ba, Andadi na gaji, na gaji sosai da damuwar FARHANA "

A hankali ya koma saman kujerar ya dora goshin Anna a kirjinsa a hankali habarsa a saman kanta, ya lumshe idannuwansa yana rike da hannunta a tausashe ya furta" In sha Allah zan amshe shi, sai dai kafin ya zo zan je in same shi, domin na san gidan iyayen sa......., ki kwontar da hankalinki in dai wannan ne an gama,"

Ya sauke ajiyar zuciya a sanyaye ya ce" Bana son in ganki a irin wannan halin.........."

Ya sake zuba mata ido a hankali ya ce" Da ace ina da dama, zan raba ki da Inna ne....., sai dai kin kiya, hasali ma kin saka min dokar kiyayar shiga lamarinki da ita............., Ama ina tsoron in gaza.........."

A hankali Anna ta ce" A'a, babu ruwanku da tsakanina da Inna, Inna uwa ce a gare ni, du abinda ta min wanda na sani da wanda ban sani Ba ma, Andadi kullum cikin yafe mata nake yi,kuma ina rokon Allah ta gama da duniya lafiya........., ka san me? Ita da kanta na tabbata irin yadda abin ke mata ciwo a zuciya ne take fadin ire Iren haka, ta haka ta iya fitar da Tata damuwar, ta haka ne kawai take iya amayar da damuwarta a rayuwa........plz Ni dai ka yi yadda ya dace, ka min abin nan yadda ya dace, ta haka hankalina zai fi kwonciya.........., a bata wanda take so din, kuma a kwana kusa"

Idannuwansa ya lumshe, tausayin Anna da Mutalab na ratsa zuciyarsa .......

Shin yaya zai yi kenan? Da farko shi da kansa ya zata kawai Mutalab yana son zaunawa ne dai, Ama a hankali ya gane da gaske yana son auren FARHANA ne....., kuma gashi yayi nauyin baki bai sanarwa Anna abin nan ba har ita ta kawo maganar nan, yanzu yaya zai yi kenan?

A hankali ya sake furta" in sha Allah, idan na yi sallar la'asar zan je da kaina , kuma ba zan je da niyar yin abinda hankali zai tashi ba........., zan sanar masa ya fito ne kawai"

Anna ta sauke ajiyar zuciya a tausashe ta furta" Allah ya maka albarka, yadda kake min biyayya ina yi maka addu'ar Allah ya baka ya'yan da zasu yi maka masu albarka"

Idannuwansa ya lumshe, yana jin addu'ar nan har cikin zuciyarsa......

Kwarai idan ya ji addu'ar nan daga bakin Anna yakan ji wani irin farin ciki na shiga zuciyarsa har ma ya ji a ransa cewar kwarai zai samu shi ma haihuwar nan, kwarai Allah zai bashi, Allah zai basu shi da MAZNA, zasu samu karuwar haihuwar nan a kwana kusa, shi ma zai rike d'ansa a hannunsa har yayi farin ciki da hakan........, shi ma zai yiwa d'ansa tarbiyya har a kai wajen da yaronsa zai masa biyayya, yana ji a ransa cewar wata rana shi ma zai samu wannan farin cikin.........

Murmushi yayi ya amsa da amen kafin Anna ta sake zuba masa ido.....a tausashe sosai ta ce" Andadi, dayar maganar da nake son yi maka kuwa a kan maganar gidan nan ne"

Yanzun ma ido ya zuba mata da kula sosai

Anna ta ce" Andadinine, ina so ka cenza min gida, Ni da Inna da Farhana, ina so mu koma wani gidan ka ji?"

Falon ya daga kai ya bi da kallo, a tausashe ya ce" wata anguwar kike so mu koma Anna ?, kin ga yanzu in ina kike so mu koma sai mu koma tunda an ga Y'ar Mama ko?"

A hankali Anna ta girgiza kai tana dubansa ta ce" anguwar nan ta min Ni ai, sosai nake son anguwar nan, bale da na ga wajen gidan su Nur sai na ji zan fara yin zumunci sosai da yan anguwar nan, idan so samu na yi ka sama min wani wajen a nan wajen din, ......."

Yanzun ma murmushi yayi ya ce" To mu koma cen Plateau mana, sai a rushe nan din ki zabi sabon ginin da kike so a yi Anna ?, Ni ma tunda na zo nake ta tunanin ya dace a sabunta gine ginen nan"

Anna ta rike hannayensa, a tausashe ta ce" Baka fahimci abinda nake nufi ba, kai kuwa Andadi gida dai gida a duniyar nan idan ya wuce wannan ai abin ya wuce ka'ida, haba sai kace wace zan dawama wannan ma dan Inna tace wallahi sai mun shiga ne na yarda muka zo ama da farko har tsoro ya bani fa........, kawai ina so ne kai ku zauna da matarka a nan, Ni kuma da ina da Farhana da Mama da Malan sai mu koma wani wajen"

Yanzu kam fuskarta ya tsare da kallon da ya sa a tausashe ta ce" Ka fahimce Ni kuwa?, takurar ta isa hakanan, ka ji?"

A hankali ya ce" Anna, me yake faruwa ne? Wace irin takura? Wani ke takura ki ne??"
Chapter 92 · 0% Book details