Sashe 119
Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Haka kuma shigowarta da du abinda take yi a kan idannuwansa...............................
Ido ta zarro hadi da fadin" Innalilahi, innalilahi, innalilahi, ina kayanka???????"
A gigice ta kashe fitilun bakinta bai daina fadin Innalilahi ba, ta kuma juya a gigice da nufin neman hanyar fita, wanda hakan ya saka shi da tarin takaici ya ce" Kika yarda kika fita kina ihn ina kayana har kika da aka yi tunanin kin gani zirrr sai na saba maki HALLAH!"
TURUS ta tsaya saboda cen ciki yayi maganar, Ama kamar muryarsa a gajiye take sosai
Kasa kasa ta ce" Yayan FARHANA to ina ka ga suturar? Na rantse baka da kaya!"
'innalilahi' ya Ayana a karkashin zuciyarsa, kafin ya dauko kafaffuwansa a hankali ya mike ya nufi inda yake ganinta , saboda shi a duhun ya wuni ya kwana ko a kashe yana ganin abinda ke nan bale da hasken bayi fa, ba wai durum bane....., wanda ya shigo ne dai baya ganin komai.................
Inda take ya karaso, sai dai bai matse mata waje ba, ya tsaya a hankali yana duban ta, murya cen ciki ya ce" Me ya kawo ki dakina?"
A hankali ta juyo inda take jin muryarsa kasa kasa ta ce" Ka saka sutura?"
Yanzu kam da takaici ya ce" An fada maki Ni ke ne?"
Nur ta ɗan ja baya kadan tana turo baki ta ce" Ni ai bana zama ba riga, kuma me yasa ka kwana a nan ne? Yaji ka yi??????"
Lamarin yarinyar nan ya girmama, ................., lamarinta yana daf da fin karfinsa .............
Kai ya girgiza ya juya inda dardumarsa take dan a nan ya ajiye jalabiyar ya dauka ya zurma yana sake hade fuska ya ce" Ki yi tafiyarki"
Nur ta koma inda fitilun nan suke ta kunna hadi da rintse idannuwanta a hankali ta ce" Ba inda zan je, abinci na kawo maka, ci zaka yi ka bani in mayar da kwanonin kicin ya'yan FARHANA "
Yanzu kam sai kawai ya zauna bakin gado ya zuba mata ido , ya kasa bude baki yace da ita A, gaba daya furucin da take masa kanta tsaye ya fi bashi mamaki, kuma a yanzu ma doguwar riga ce jikin yarinyar nan mai siririn hannu, sai wata hula mai gashi dake kanta kamar hular sanyi sai dai ba ta sanyin bace............ Mai ruwan pink mai haske sosai, hakan ya sa ta yi mata kyau sosai a kanta
A hankali take dan Bude idannuwanta
Ganin ya saka riga ya sa ta saki murmushi ta nufo shi hankali kwonce, ta karasa ta zauna daf da kafafuwansa ta bude basket din ta ciro kayan abincin ta dago tana dubansa a hankali ta ce"
😍😍😍😍😍😍🤣🤣🤣Kisan mummuke page 76_77
Tana dubansa a hankali ta ce " wai hala tunda ka shigo jiya baka fita ba?, yayan FARHANA mata fa ke buya, su ne suke yin yaji, yaya za'a yi ka zo nan ka boye Fisabililahi, sai ta yi tunanin tsoronta ake ji ma ai"
Ajiyar zuciya ya sauke a hankali kafin ya koma ya kwantar da bayansa hadi da kai hannayensa wajen goshinsa a hankali yana shafawa
Ganin ya kyale ta ya sa ta ɗan tabe baki, ta zuba abincin a plate din sannan ta mike tana kiyaye zuba masa ido din nan ta ce" Ka tashi mana dan Allah, ka gyara ka ji?"
Dagowa yayi ya dube ta a hankali ya ce" Wai ba cewa na yi ki yi tafiyarki ba?"
Zaunawa ta yi bakin gadon , hakan ya sa ya zarro ido ya matsa yana nuno mata hannunsa ya ce" Tashi ki yi tafiyarki, bana son takura tashi tashi tashi!"
Mikewa ta yi da sauri, sai kuma ta ɗan ja baya tana murza hannunta , lokaci daya kuma ta dafe goshinta ta dube shi a hankali ta ce" Ka san me matarka tace da ni ? , ya Allah ko tana tunanin wai dan ta ga irin haka? Ka san Allah Ni fa kamar yayana Sulaimana nake kallonka, shi yasa nake iya wasu abubuwan a gabanka, ama shi ne matarka take zagina?......Allah zai saka min ne, ci abincin yayan FARHANA in tafi ka ji?"
Ita da kanta ke fadin abu, kuma tana ƙaryata kanta, to ƙaryata kanta mana, tace kamar ƴaƴanta take kallonsa, kuma tace wai yayan FARHANA, yarinyar nan shi bai ma san yaushe ta samu sakewa da shi irin wannan ba, ko dan ta daku matarsa take tunanin karfinsu daya da shi ma? To karfinsu daya mana, yanzu abincin take tunanin saka shi ci dan dole ko yaya? Ai sai ya ga ta yadda zata saka shi cin
Jujuya abincin ta ringa yi, a hankali ta kai cokalin bakinta ta taɓa
Sai kawai ta ji dandanon ya mata dadi a bakinta, hakan ya sa ta kara cokali daya, tana taunawa ta shafa cikinta ta ji a cike fa yake , ya dace ta bari hakanan
Ciko wani ta yi a nutse ta nufi bakinsa da shi, a tausashe ta ce" Ka yi hakuri ka ci abincin nan plz"
Hannunsa ya saka ya tare cokalin yana kallon cikin idannuwanta a hankali ya furta" Bana jin yinwa NUR"
Nur ta girgiza kai, a tausashe ta furta" Idan baka ci ba, ba lalle hankalina ya kwanta ba , plz ka ci"
Idannuwan yarinyar nan a cikin idannuwansa.......
Ta dawo din bakin bed din ta zauna, haka kuma ta debo abincin a cokalin ta nufo bakinsa da shi......ya Allah
A hankali ya dauke dubansa, kirjinsa na neman curewa
Cen wani tunani ya ringa yawo a cikin kwakwaluwarsa mai zafin gaske
Sake duban hannun nata yayi, a hankali ya ce" Haka kike yiwa duk wani saurayin ki?"
A hankali ta sake duban fuskarsa da take yi mata dadin kallo, muryarta kasa da tasa kwarai ta ce" Saurayina kuma?"
Sake saka idannuwansa yayi cikin nata ya ce" Eh, zaki iya fitowa gaban kowani namiji da shiga kowace iri ce?, zaki zauna haka daf daf wanda ba muharaminki ba? Zaki iya yiwa Anas haka kenan?"
Da sauri ta girgiza kanta tana mikewa hadi da sake ajiye masa abincin a nan
A hankali ta ce" Ka san me yasa na zo nan a yanzu? Nauyi kayan suka yiwa annata, shi yasa na amsa , kuma umarnin da ta bani shi ne ka ci kafin in kawo mata kwanonin.....da ba dan wannan ba, babu abinda zai kawo Ni nan, bale har in zauna in nemi ganin ka ci ....., hankalina da zai tashi kuwa ba a kan komai bane sai a kan kar in koma mata da amsar baka ci ba......., ina girmama du wani abin da ya shafe ta, ama idan har haka zai sa ka yi wani tunanin a kaina ka yi hakuri"
Daga haka ta juya da nufin tafiya
Haka kawai, yana zaune, shi da yake fushi da ita, ya samu bakinsa da budewa ya ce" Nur, dawo nan"
Dakatawa ta yi , ta juyo tana dubansa, haka kawai hawaye ya bale mata, tana tsaye ta shiga shashekar kukan da ya saka shi zuba mata ido a hankali ya furta" Menene na kukan?, zo nan"
Dawowa ta yi din, sai dai ta ki zama, kuma ta budi baki cike da sakalci ta ce" Ce min ta yi karuwa fa, kai kuma kace wai a gaban samarina ina iya fitowa haka?, ina iya ba saurayi abinci? To ka tambayi Anas Ni ban taba haka da shi ba, saboda bana sakin fuska wa kartin banza, kai ai ba wannan tsakaninmu yaya kake a waje na, .........shi yasa har , har ma na baka abinci ko?"
Agogon dake hannunsa ya ringa murzawa, kirjinsa na dokawa
A hankali ya ce" Sit......"
Inda ya nuna ta kalla, sai kawai ta noke kafada ta zauna a kasa ta ci gaba da shashekar kukan
Idannuwansa ya dan rintse, kafin ya dauki abincin a hankali ya ce" Zan ci, stop scrng........"
Dan dagowa ta yi , rana dubansa, ta ga yayi Bismillah ya deba ya kai bakinsa....a hankali ya sake duban ta hadi da yin dan murmushin da ya sa ta sauke ajiyar zuciya tana sada kanta hadi da share hawayen nata a hankali ta sake bin hannunsa da kallo ya sake diba ya kai bakinsa ya ci gaba da taunawar.......
Murmushi ta yi, ta ɗan langwabar da kai, shi kuwa a hankali girarakinsa ke yamutsewa......, sai kuma ya dauke dubansa da sauri ya ci gaba da cin abincin har ya kai cokalin dan sak dibowa ya ji wayam ba komai
A hankali ya dubi plate din, ya juyo zai Dube ta ya ga ta ciro ruwan dake cikin gora ta bude masa ta miko masa hadi da sake yin murmushi
Amsa yayi, yana mika mata plate din, a nutse ya kafa kai ya sake shanye ruwan yana jin zufa na karyo masa..........
"Baka amshi karatun nawa ba, da kace zaka amsa jiya..... Ka kuwa san ina tsoron ka kore Ni daga makarantar?" Ta fada a cen kasan makoshinta tana sake dubansa
A hankali ya ce" Ba zan iya korar ki b..........................."
Hadiye sauran maganar yayi, kafin ya sake duban ta, saboda yana dubanta yana dauke idannuwansa ne,
Kasa kasa ya ce " Zaki dage ko?, zaki dage Sosai, idan aka zo da tambayoyi sai ki bada amsa yadda ya dace , kin ga kuwa ai ba za'a kore ki ba ko?"
Kai NUR ta gyada a hankali kafin ta yi murmushi tana harhada kayan ta mike hadi da dauka a hannunta
"Tafiya zaki yi?" Ya samu bakinsa da sake furta wa
Nur ta juyo tana dubansa, a tausashe ta ce" Zan kaima Anna kayan, wanki zata yi dan in amsa in yi"
"Wanki?" Ya fada da mamaki, domin ya san a gidan nan AKOY mashine na wanki a kowani bangare ......., me zai hada Anna da wanki kuma?
Nur ta gyada kai ta ce" Eh, kayan Inna zata wanke, bari in yi sauri kar aje ma ta fara....., am, yaya nace yaya maganar ta Mama?"
Idannuwansa ya dan fitar, a hankali ya ce" Ba zaki bar maganar ba?"
Nur ta yi tukuf tukuf da fuska hadi da neman fashewa da wani kukan ta ce" Yaya kake so in hakura da maganar matar da ta raine Ni?, ka yafe mata dan Allah "