← Book details Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 88 OF 141

Sashe 88

Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

To ai ko a lokacin da yake nesa da ita zuciyarsa na da nutsuwa da tunanin MAZNA na daf da ita, zata share mata kuka, yata rarasheta, zasu yi hakurin rashinsa a kusa da su a tare......

A hankali ya duba time a wayarsa kafin ya mike ya nufi bangaren Mama dan ya ga jikinta sanan ya fadawa Malan abinda yake faruwa kafin sallar la'asar kuma su fita shi da Aliyu Dan zuwa inda yaron nan yake.

A dakin Farhana kuwa, bayan sun gama cin abincin hade kwanonin suka yi a basket Farhana ta yi kiran mai aiki ta sauke su kicin ta wanke sannan suka shiga fira

Fira suke ta hankali, fira suke yi ta karuwa, fira ce ta karawa juna ilimi da wayewar duhun kai, wace a cikinsu kowace da kalar baiwar da Allah yayi mata

Farhana ce ta dubi A'isha ta ce" A'isha wai ke waye saurayinki? Ni ban taba ganin ki da saurayi ba"

Nur ta yi murmushi ta ce" Wa ta ba fuska? A rashin ba samarin fuskar da take yi gashi nan sulaimana ya balo mana aiki, Allah ya sa Malan na Magarya ya tafi da shi ai da mun ga fitina "

A'isha ta harareta tana duban FARHANA dake tambayar wai dama ba soyayyar suke yi ba?

Murmushi ta yi tana sada kanta a hankali ta ce" Anya akoy gayen da zan iya so sama da yaya SULaimana?"

HALLAH dake shan ruwa ce ta kware, tsakani da Allah ta kware ta shiga tari da kyar ya tsaya mata tana duban A'isha ido waje ta ce" me kika ce? Innalilahi wa Inna ilaihi raj'une, wannan wani irin rashin sanin ciwon kai ne? SULAIMANA? Ke yanzu ko daura maki shi aka yi ai kya kunce ki fita da gudu, gidan duka, namijin dake dukan ki tun a waje zaki ce kike so, ina ke ina SULaimana?"

A'isha ta harareta ta ce" Kin ga bana son neman masifa , kuma wallahi kar ki saki ki zage shi ,kin san ba kyale ki zan ba, tam, kuma maganar wai wani wai mai duka ke da kanki kin san ni baya duka na, ke ce ke masa rashin kunya ya dake ki ke kadai, kar ki saki ki zage shi na fada maki"

Nur ta sake tafa hannu tana karkatar da kai ta ce" shiKenan, Ni kam zuwa yanzu zan fara yi maki addu'ar Allah ya yaye maki wannan damuwar ,saboda gaskiya kina cikin matsala, cabdijan "

FARHANA ta harareta ta ce" ki mana shiru, ke da baki san darajar soyayya na baki da abin fada a nan, ......sis A'isha fada min, wai dama ke ma kina son sa?"

A'isha ta yi murmushi tana sune kai, kafin ta daga ta dubi FARHANA a tausashe ta ce" a da, da nake masa kallon yayana, ban taba kawo haka a raina ba, sai soyayar yan uwantaka wace a kullum nake fatan Allah ya sa ya rage jin haushin mu ya ja mu a jiki, bale Ni bai taba daga hannunsa a kaina ba Farhana, kin ga mai janyo shi nan kuma mama ta shigar mata su bata masa rai su sa ya bar gidan......., Ama daga bakin lokacin da maganar nan ta fito, sai nake ji a cen karkashin zuciyata Bani da wani da zai iya birge Ni sama da shi a duniya......, ya zamo in dai zan kadaice kaina to tunaninsa zai fi komai yawa a zuciyata "

Nur da karfi ta furta" Astagfrullah, Astagfrullah Astagfrullah Astagfrullah Astagfrullah Astagfrullah!"

FARHANA ta cila mata karamin filon da ta rungume tana harararta,

A'isha kuwa kawai murmushi ta yi dan ba zata iya rikicin nur ba, ta tabbata yanzu da sun yi ido hudu zata ja mata a'uziya, ita kuma iya gaskiyarta ta fada, har tsoron abinda auntynsu tace take yi, da tace su saka mama a addu'a, sannan su yi ta rarashin mama ta nan gidan da yaya wai, dan a saki Mama, ko ba komai mama Maman su ne, tana tsoron mama ta dawo ta hanata auren yaya Sulaimana gaskiya!

Shigowar Anna ya sa suka bi ta da kallo suna yi mata sanu da shigowa

Murmushi yake yi tana bin su da kallo bayan ta zauna a tausashe ta ce" Fira kuke yi?"

FARHANA ta ce" Eh Anna"

Anna ta ce" Masha Allah, a riinga yi ana ƙoƙarin yiwa yata lesson, kafin in samu Aban naku in sanar masa ina so a bani ita na kwana biyu sosai in mata lesson saboda wannan Tantancewa da yayanku zai yi na bani tsoro, domin Fisabililahi shi da larabawa ya saba karatu, da wahala ya kyale min dalibai a cikin nutsuwa

Nur ta rafka tagumi cike da tsoron kar aje ya Koreta

FARHANA ta yi dariya hadi da A'isha

A'isha ta ce" Ai kam Anna, gwara dai ku dage"

Anna ta yi yar dariyar ita ma, a tausashe bayan ta mike ta ce" Ku tashi ku shirya ku je saloon din nan, a yi shigar mutunci idan kun je a wanke kai yau, in yaso in aka kwana biyu sai a koma a yi kitso, ga katina a yi anfani da shi, zan shiga in yi barci sai kun zo"

Godiya suka ringa yi, Anna na fita Nur a hankali ta ce" ku yi maza ku shirya mu je, wallahi yau sai mun samo inda yake mun fada masa sakon Anna, "

Farhana ta zarro ido kasa kasa ta ce" wai da gaske kike? Bakya tsoron asirin mu ya tonu?"

HALLAH ta tabe baki ta ce" Mu je dan Allah, idan Anas na so ya zo ya fadi inda ya kai mu, in ba sai na fasa aurensa ba ubana goma, kuma bayan wannan ai ba yawo zamu je ba, sakon Anna zamu isar tunda mun kasa samunsa a waya"

Gaba daya shawarar nan ta musu, hakan ya sa suka shiga shiryawa da gagawa kafin su fito su sauka su samu Anas da ya gyara mota ya loda su suka dauki hanyar saloon, wanda suna tafe Nur na dan jan shi da firar da har ga Allah bai taba ganin tana masa irin sauƙin kan nan ba, su kuwa sun yi gum kowacce na tunani har suka iso saloon din , ya zamo su biyu sun fita daga motar , Nur ta fito ta koma gaba tana murmushi ta Dube shi ta ce" Ya Anas, idan muka fito plz zaka kai mu gidan su iyayen saurayin FARHANA zamu sanar masa sakon Anna ka ji? Please yaya Anas ban taba tambayarka komai ba sai yau, dan Allah ka min"

Anas na kallonta yana murmushi , duda karkashin zuciyarsa cike da tunanin gidan su saurayin FARHANA kuma? Sai dai shagwabar da aka yi masa ta yau ta gama halaka masa tunani, hakan ya sa yana doka murmushi yana duban ta tamkar ya janyo ta ya rungume yake ji ya ce" Lafiya dai ko? Ina fatan sakon mai mahimmanci ne"

Nur ta kara shagwabe fuska ta ce" Sosai, sakon na Anna ne ai"

Ya gyada kai yana tafka murmushi ya lalubo aljihunsa ya ciro kudi ya ce" To shiKenan, zamu je ama minti biyar zan baku ku fada mu wuce kin ji?, ga wannan na gyaran kan ne amaryata"

Fyskarta ta rufe da hannayenta kafin ta fita tana dariya ta ce" A'a, Anna ta bamu, na gode yaya Anas"

Ta yi gaba da dan sauri irin ta ji kunyar nan tasa , wanda hakan ya sa ya sake lekawa yana washe baki hadi da sake sakin murmushi soyaya na yawo da shi a gajimare ya wani gyada kai yana jin a duniya a yanzu ai shi lafiya lau yake, komai zanzan , Nur ta fara kaunarsa, a yanzu kam ya yarda ta fara son sa......

Sunna shiga aka fara yi musu gyaran kan, Nur na sanar musu yadda suka yi kafin ta dubi A'isha ta ce" ikon Allah, ashe haka mazan suke? Kawai kato da kai daga yi maka alamun zan yi kuka sai ka amsa cewar zaka yi? Lalle maza zasu shiga uku a hanuna, to ai Ni gabanan harta abanmu alamun zan masa kukan nan zan yi in zan roki kudi, ta yiwu a dace"

A'isha ta gyada kai ta ce" Madallah, shagwaba kike yi, dama ai kina yiwa Aba, Ama gaskiya yaya Anas bashi da wayo"

FARHANA ta yi dariya ta ce" Dan Allah ku bari a min gyara mai kyau Ni da zan hadu da masoyi, in Anas ne? Ai haka yake a lamarin mata"

Kallonta nur ta yi da alamun son karin bayani, sai dai Farhana ta dauke kai, dama da biyu ta fada, kuma ta tabbata sakon ya je inda take so domin yannayin fuskar Nur ya nuna tana son karin bayani, ita kuma ba zata bata karin bayanin ba, karshe ma sai ta sa a fara wankewa NUR din kaffafuwa da gyaran hannu harda su saka gashin ido domin ita ne tace a yi mata dan Allah dan ta ga kalar da zata koma.
________________________________

IMAD bai koma bangarensa ba sai da aka yi sallar la'asar, ya salata Sannan ya nufi bangaren , har yanzu fuskarsa ba sakewa ko kadan, domin ko da ya je wajen Malam yayi ta yi masa tambayoyin lafiya dai ko? Ama ya nuna masa kalau, daga baya ma sai Malan din yayi tunanin dan Anna tace masa ya yi hakuri ya zauna da saurayin FARHANA ne ransa ke bace har yayi ta kara yi masa nasiha da sake nuna masa mahimmancin yiwa mahaifiyarsa biyayya da kuma nuna masa a yi ta addu'a alkhairin kenan, karshe ya baro bangaren nasa bai ma ga mama ba domin barci take yi sosai na magungunan da aka bata , ko Anna bata ganta ba haka su Farhana basu je Bama domin Anna ta sanar musu su bari ta farka.

A lokacin da ya shiga ya samu Jauhara da MAZNA ke falon baba suna kallon séries a Babar tv din dake falon.

Bayan Salama da yayi, bai tsaya ba ya wuce bangarensa, wanda hakan ya sa Jauhara duban MAZNA dake dan fama da kanta wuni guda tana ta fama da shan magani ta ce" kamar fuskar big broth a daure, lafiya kuwa?"
Chapter 88 · 0% Book details