← Book details Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 141

Sashe 23

Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mikewa ta yi tana nufar kayanta ta dauko ta shiga kabewa da nufin sakawa ranta na neman dagulewa....., shima likitan sai a lokacin ya tuna ya dauke ka sa yana dan shafa bayan keyar sa...............................................

Saudiyya💅💅💅💅💅💅💅💅💅💅
*KISAN MUMMUƘE*
💅💅💅💅💅💅💅💅💅💅

_PAID BOOK_

*BY*

_SAJIDA NIJAR_

*Yan Naija Mutanen mu 1k ne a kan wannan account number 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank* sai a bani shedar biya ta layi na kamar haka +22793811618

*Yan Nijar mutanen mu zaku turo da hoton kati ta airtel ta dala dari , wato 500francs cefa a kan Numbarna kamar haka +22793811618*

*Na gode, sai kun zo.....taku ce SAJIDA NIJAR*

Tallah, tallah, tallah

*12*

Zaune suke a katon falo, irin falon nan mai girman gaske wanda ke dauke da kayan alatu kala kala, da ƙatuwar TV hadi da kayan shayi a gefe wanda suke anfani da shi

Tun da safe suke gidan, sai dai har yanzu sir SAWIRIS bai shigo ba saboda yana hutawa ne

Sai kusan karfe uku na yama har sun fito daga masallaci sun ci abinci sun dora da wata firar, ciki har Abdul Fatah ya yi barci, sai sauran ke fira tsakanin su sannan ya shigo falon da Salama da shi da yan uwansa har mutun biyar

Gaisuwa irin ta larabawa suka shiga yi gaba dayansu harda wanda ya saje a cikin su tamkar shi din ma jinin larabawa ne.

Da kula sosai mahaifin nasu ya dubi fuskar Abdul bassit yana fadin" Shi kuwa me aka masa? Habiby me yake faruwa?"

Abdul bassit ya dubi uncle din sa yana sake shagwabe fuska ya ce" Ya abiey, ashe wai IMAD komawa zai yi zama kasar Nijar?"

Uncle Muhammad ya ce" Eh haka ne, me yake faruwa ne?"

Abdul Fatah ya zauna da kyau yana yin kalar bacin rai shima ya ce" Yaya za'a yi ya tafi ya bar mu? Me zai nema a cen?"

Da mamaki mahaifinsu ya ce" A kasar da mahaifiyar sa, kakar sa, matar sa, kanwar sa, dangin sa suke ne kake cewa me zai nema? To ko bashi da kowa a duniya ai ƙasar haihuwa daban take, bale ya jima yana min biyayya a kan tsarina, Ni kuwa ina kara jan komawarsa ne dan akoy wajen da nake so ya kai da harkar dukiyarsa.....a yanzu kam na gamsu na kuma yarda da kwazonsa sai dai in masa fatan alkhairi, ba fa zaku hana shi tafiya ba, sai dai ku yi hakuri"

Kasancewar idan ya yi magana babu wani dake kara musawa ya sa du suka yi shiru, sai IMAD din da ya yi murmushi kawai....m
Shi da kansa ba zasu gane bane irin yadda zuciyarsa ke masa radadin rabuwa da su

Ama lokaci ya yi da zai je kusa da ahalinsa dan ya kula da su su ma

Abinda idan sun yi niyar haduwa ba zata gagara ba da yardar Allah??????

A tausashe uncle Muhammad ya ce" Aliyu ya same ka da maganar sa?"

IMAD ya dubi uncle Muhammad ya ce" Eh abiey, sai dai na fada masa sai ummi ta zauna da iyalansa idan sun yarda zasu iya rayuwa a cen din ne sai a shirya musu tafiyarsu mu je gaba daya, "

Abiey ya ce" Ai in dai kai ka amince wannan ba damuwa, domin mun yi magana da ita da kaina, ta nuna min du inda mijinta ya je zata bi shi ne......"

IMAD ya gyada kai, a ransa yana jin kwarai da sai ya fi kowa farin cikin hakan, saboda Aliyu ya fi kowa saninsa, mutun ne jajirtace da amanarsa da rikon gaskiyarsa suka sa ya shiga jikinsa sosai

A nutse ya mike ya nufi waje saboda yana son kiran Anna dan su gaisa

Tana fara ringin Anna ta daga tana furta" Habiby"

IMAD ya furta" Ummi, Barka da warhaka"

Anna ta amsa da kula sosai, sannan ya ce" Ya gida, yaya mai jiki? Bana samun wayarta ko har yanzu bata huta da tafiyar nan bane???"

Anna kanta ya daure, da kula ta ce" Waye ba lafiya? Wace tafiya fa?"

IMAD ya yi dan shiru, kafin ya ce" UMMI, MAZNA ko? Tace ta yi jinya sosai ciwon ciki , shekaran jiya da ta zo take fada min, Ama yanzu da sauki ko?"

Anna ta ce" Aya, Subahanalah, ai ban sani ba, Allah sarki, yanzu yaya jikin nata? Ina fata ka kaita ta ga likita?"

Wannan karon kam sai da ya sake bude idannuwansa da kyau, a hankali ya ce" Anna, me yake faruwa ne?"

Anna ta itama ta saka yannayin serius ta ce" wani abu ya faru ne?"

Kai ya girgiza ya ce" Anna, kwananta biyu yau da sauka a Nijar ai, kuma kamar baki sani ba, kamar ma baki san ta zo nan din ba, wai tana ina, a bani ita plz wannan wanni irin rashin hankali ne take yi a rayuwa?????"

Anna sai yanzu ta gane komai sala sala, sai dai bata yarda maganar ta yi nisa ba ta ce" Kana ji, zan kiraye ka, ka san yanzu wuni nake yi a makaranta, gashi lokacin sallah ya kusa ban gama yin salatil ala nabiyi (s.a.w) dina ba, zamu yi waya idan na je gida"

A dole suka yi Salama, shi ya dan jima rike da waya a hannu kafin ya shiga msg ya rubuta mata msg cewar ko me take yi ta yi kiran shi zuwa dare kafin ya koma ciki suka sake nutsuwa kan maganganun shirye shiryen tafiyarsa da duk wani abin bukatarsa bar sai da lokacin Sallah ya yi suka fice gaba dayansu

Bayan sun fito daga sallar ne ya shiga gabansu su uku yana dubansu ido cikin ido kafin ya yi murmushi ya ce" Ok, na ba kowane minti biyar ya fadi abinda yake nufi da wanda yake so, zan bashi amsa da kuma dubawa in sha Allah"

Abdul bassit ne ya fara dubansa a tausashe ya ce" Na zata zamu yi ta zama da juna, zumuncin mu zai dore har kiyama, na zata muna tare da kai , kana gani da yawa basu san cewa kai ba jinin mu bane, shin kai baka dauki haka ba?"

IMAD ya Dube shi cikin ido ya ce" Dan kawai na koma kasata, dan in je in tallafa da dukan gudunmuwar da ta dace, dan in je kusa da Anna in dafa mata a kan shige da ficen yau, dan in kula da shige da ficen FARHANA, dan in zama kusa da matata sai zumuncin mu ya lalace?, dama zumuncin sai ina nan kake nufin za'a iya yin sa?"

Da sauri Abdul bassit ya ce" Ba haka nake nufi ba, Ama ka ga kullum muna tare fa, ama yanzu hakan zai gagara......?"

Abdul Fatah ya dauki maganar da fadin" Zumuncin mu ba zai taba katsewa ba, saboda idan baka zo ba ma mu ma je, broth.......juste zamu yi missing din ka fiye da tunaninka....., kai ne ke taro mu a tafiyar mu, kai ne ke mana fada, kai ne ke tsayawa a kan lalle sai mun kiyaye abubuwan da ba kyau, du kana yin wannan ne da kana nan......., yanzu idan ka tafi yaya zamu yi kenan?????"

IMAD ya sauke ajiyar zuciya a tausashe ya ce" Kuna tunanin Ni ba zan yi missing din ku ba?, zan yi missing din ku sosai........, jini ne kawai ban hada da ku ba, Ama du wani launi na zumunci tsaftatace da ku na gina shi..........plz kar ku sa tafiyana na yi ta ba karfin zuciya......"

Ya karashe a hankali yana sake dubansu a tausashe ya ce" Na zata sai kun fi kowa murna......, na zata zaku so in zauna waje daya ko Allah zai sa in sake samun wata haihuwar ma......., "
Sai kawai ya dan shafa gaban goshinsa ya girgiza kai ya juya zai yi tafiyarsa

Da sauri du suka karasa suka zagaye shi, kasancewar runguma a kasar Larabawa ba laifi bane tsakanin namiji da namiji ma, sai du suka rungume shi suna kara tabbatar masa kwarai zasu taya shi, zasu zamo masu bashi kwarin gwuiwa, harma zasu yi masa rakiya, kuma zumuncin ba zai taba lalacewa dan kawai ya dawo kasar sa ba.

Daga nan suka wuce gaba daya, masu nufa gidajensu suka nufa, masu zuwa wani wajen suka tafi

IMAD na shiga Mota Aliyu ya ja kiran MAZNA ya shigo

A hankali ya furta" Aliyu samu waje ka tsaya, zan amsa waya"

Cikin girmamawa Aliyun ya tsayar da motar a inda ya dace sannan ya fita ya yi dan nesa da motar

Wayar ya daga yana jin Salamar da ta yi

A hankali ya amsa kafin ya ce" Kina ina"

Irin yadda ya yi tambayar ya kara tabbatar mata ransa a bace yake, saboda tun Dazu da message din sa ya shigo suke kiciniyar hada call din ta yadda ba zai taba gane a inda take ba

A tausashe ta ce" Ina gida, nan plateau, na zo ne in harhada abin shinfida da kayana in saka a mashine in kara kwashe su kaf, dan rabona da su tun da na zo nan"

Bacin ransa yake ta danewa, domin bai cika son saurin nuna fushinsa ba, ama ta muryarsa ta gama gane sam baya cikin dadin rai

A hade ya ce" Yaushe rabon ki da Anna "

Sai da ta zarro ido, a hankali ta ce" Anna kuma Akul?, Anna Dazu ma na hango ta za'a fita da ita zuwa makaranta, ka dan anna yanzu bata zama sam, ba'a cika samunta ba , koda yaushe tana makaranta ....."

"MAZNA, mahaifiyata?, mahaifiyata ce zaki ce kin hango ta? MAZNA mahaifiyata ce zaki taho Saudiya ki koma bata sani ba? Mahaifiyata ce zaki yi jinyar da kike nufin ta wahalar da ke sosai Ama na tambayeta jikin ki bata san da baki da lafiya ba????" Ya katse ta yana ɗan daga murya, wanda hakan ya sa ta zabura ta zauna jikinta na son daukan rawa ta ce" Khalb, tsaya ka ji abinda ya sa Anna bata sani ba.....ka san cewa bana son daga mata......."

Kit ya katse kiran gaba daya yana rintse idannuwansa wani bacin rai da ya shafe ta na neman rufe masa kofofin hanci........

Yaya za'a yi yarinyar nan dan ta raina shi ta kawo masa wani uzuri?

Wani irin uzuri ne zata fada ya karba?
Chapter 23 · 0% Book details