Sashe 15
Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A zahirin gaskiya mu Hausawa muna da matsalar rasa abokin rayuwarmu, ya zamo ya ga wata ya juya mana baya, ko wata ta fi birge shi fiye da mu a duniya, hakan na gigita duniyar mu sosai da sosai, shi yasa a duniya kullum MAZNA cikin neman hanyar da idan suka hadu da mijinta zata sake haukata masa lisafi ta kowani fani, dan kuwa kafin ta gane shi ne ya dace da ita sai da ta kara yarda bayan kyau, isa, takama, aji, hatta dukiya ya dame ta, sai ta sakawa zuciyarta shi ne ya dace da kalar Tata sarautar har zama ya yi tsayi haka tsakanin su
MAZNA itama a Tata duniyar mace ce da duban mata ke mangari suna jin inama ace sun samu kadan daga cikin damar da take da ita? Kai da sun dama abin a zo a gani na mamaki.......,
MAZNA ko a lokacin yarinta bata yi ƙawance da wa'inda ba tsarin tafiyarsu daya ba, idan har iyayenki ba wasu bane ai Bama zaku iya tafiya tare ba, in har ke din wace ilimin ki ne ya kai ki inda ita ya'yan banki suka kawo ta sai ta baki azabar da baki taba tsamani ba, idan har ba jajirtaciya bace ke, sai ta sa kin ki makarantar saboda tsangwama da tuna maki cewar ke fa kaskantaciya ce, kin shigo ajin manya ne ta alfarma ba dan kin isa ki baje ya'yan banki a dube ki ba !
MAZNA ta dauki kyanta da mahimmanci, haka kuma har ta shige daga ciki a matsayin mace mai daraja matar aure bata taɓa yin soyayya da wanda ta fi kyau ko kudi ba
MAZNA na iya kashe kudade masu masifar yawa dan ta gyara fuskarta
MAZNA na iya yin tafiya mai nisan gaske dan ta je a yi mata gyaran fuska da jiki.........
Ya zamo ta samu yannayin jiki irin na mahaifiyarta, sakaken jiki, sai take boye shi cikin abaya budadiya a kowani lokaci, manyan abaya ko ɗinki baudade sosai wanda ke sakawa a yi mata duban du halayanta tana da mutunci akoy son rufe jiki.
A lokacin da ta samu ganin IMAD bayan ya zo hutu a gidan su dake cen plateau anguwar gima giman masu kuɗin Niamey sai da ta ji numfashinta na iya barin gangar jikinta idan har bata amsa sunan matar jaruminta ba,
Kwarai sai da ta shige jikin kanwarsa FARHANA ta kara samun abubuwan da bata sani ba a kansa sannan ta yi hakuri ta jirayi lokaci bayan ta isar da nufin ta har hakonta ya cimma ruwa.
Sam bata daukan lamarinsa da wasa
Babu wata hanya da za'a iya bi a ga gazawarta a aikace a kansa, domin mace ce mai boye da iya kisa na tashin hankali wanda hakan ya sa sai wanda ta yiwa zai iya gane wacece ita......Ama lokaci zai bayyana mana abinda ke duhu a tare da ita koda akoy shi..........
Hannunsa ya mika ya dauko tawul din da ya gani a rufe saman abin kanshi a nutse ya ware shi ya nada a kugunsa sannan ya karaso ya tsaya kofar bayin yana jira har sai da ta gama dukan abinda zata yi ta yi wanka ta dauro tawul bayan ta saka abinda zai tare mata jinin dake zuba a jikinta sannan ta nufo waje tsaf cikin shirin abinda zata bashi amsa da shi idan har ya yi mata tambayar abinda yake faruwa
Tana buɗe bayin idannuwanta suka fada cikin nasa, lokaci daya gabanta ya buga har sai da ta so komawa , domin wani tsoro ya kamata lokaci daya, sai dai tuna cewar idan fa ta kuskura ta aikata lamari irin na ta ji tsoro tabas zata jazawa kanta baban tashin hankalin da kanta ba zai iya dauka ba.
Kallonta yake yi yana karantar ta.
A nutse ya saka hannunsa ya dauke ta cimak ya nufi wajen doguwar kujerar abin turaruka dake jere ya ture su sannan ya ajiyeta a sama ya dan ja baya ya sake zuba mata ido sannan ya nufi bayi da hannunsa yana mata alamun minti biyu , wato yana zuwa
Tunda ya shige bayin sai ta ringa maimaita abinda zata fada masa a cikin zuciyarta tana sake sanarwa kanta abinda take da bukata a yanzu shine jajircewa, idan har ta yarda, in ta yarda ta nuna tsoro ta mutu ta lalace, tabas sai ta saka kanta a halin kaka naka yi da bawan Allahn nan.......
Ya dauki lokacin da yana fitowa yayi dai-dai da lokacin Sallah, sai kawai ya sake tsayawa ya dubeta sosai ya ga a zaunen take bata murkususu bata komai, hakan na nufin yana iya zuwa ya gabatar da sallah ya dawo cikin nutsuwa, sai ya mata Salama ya fice daga dakin da dan hanzari
Da sauri ta sauko daga saman kujerar nan ta karasa da sauri ta dauki wayarta lokaci daya ta nufi wajen kofar ta rufe da ky sannan ta dawo ta shiga dana Numbar likitan da ya yi mata aiki a Turkiyya
A kira na biyu ya daga, saboda a zaman da ta yi a wajensa sai da ta mugun shiga jikinsa har suka yi sabo na mamaki
"Mrs IMAD...." Ya fada a tausashe
A hankali MAZNA ta furta" Docter na shiga uku....., docter jini da ciwon ciki , jini docter"
Likitan ya dafe gaban goshinsa ya ce" Ina fata ba sex kika yi hvng da wuri ba, bayan na fada maki a kala sai kin kai wata shida baki yi sex ba, zuwa lokacin kin samu lafiya sosai komai ya zauna yadda ake buƙata?"
Shashekar kuka ta kama yi yannayinta na nunin tashin hankalin da take ciki ta ce" na so hakan docter, na so hakan, OGA ne ya nemi in sauka a jidda kwana uku da suka wuce , yace in zo ya gani in koma, shi yasa dole na taho, kuma kuma.......ban san haka jini zai iya zuwar min ba......"
"Mrs IMAD, aiki uku fa na miki a lokaci guda wanda da ba dan kin saka na ji a raina eh zaki iya kula da lafiyar ki ba, da sai kin yi wata uku a wajena....., MAZNA an Miki abdominoplasty or tummy tuck fatar jikin ki ta cikin ki da kitsen dake cikin cikin ki ne muka kwashe muka rage girman tumbin ki muka maida shi madaidaici ta yadda idan kika koma cin abinci cikin ki ba zai taba zama kato ba, an maki buttock lipofilling wace ke sakawa a kara maki girman duwawu ta hanyar daga su, a daidaita su a saka musu kitse, sai ta mama wato Breast lift wace muka daga mamanki muka rage bajewar da suka yi muka saka musu implan madaidaita suka tsaya...., kin kuwa san girman hatsarin aikin nan? Kin kuwa san ba dan in maki surutu bane nace dole ki yi hakuri da mijin ki har sai kin warke? Why kika yarda kika bashi kanki da wuri haka ko wata biyu ba'a yi ba? Kin kuwa san abinda hakan ke iya haifar wa.....??????"
Hankalin MAZNA ya idasa tashi, sai kawai ta fashe da kuka tana fadin yaya zata yi??????
Docter ya ce" Ki saurara, ko me kike yi ki dauko jirgi ki dawo gobe in duba ki, duka aikin da na yi zan duba sannan sai an sake wata jinyar daga farko, zan fada maki ba ke ba namiji sai kin warke, zan sake fada maki ki kula, dan hakan na iya taba ranki....., a cikin magungunan ki akoy baki shi zaki sha har ki zo nan, zai tsaida zubar jinin ya kuma hana ciwon cikin dan ciwon cikin murdawar zubar jin ne kin fahimta??????"
MAZNA jikinta na rawa ta mike tana duba maganin, ta dauka ta hadiya hadi da fadin zata yi kiransa kar ya kirayeta .
Daga haka ta ajiye komai cikin saurin tsiya ta shiga saka tufafi , ta fesa turare , tana cikin daure gashin kanta ya dan buga kofar, saboda sai da ya yi sallar isha'i sannan ya nufo dakin
A nutse ya shigo bayan ta bude masa tana bashi hanya
Karasawa yayi ciki ya fan riinga kai kawo kadan kafin ya juyo ya sake zuba mata ido
A tausashe sosai ya ce" Me yasa yannayin ki ya yi kama da idan baki da gaskiya? Me yake faruwa ne?......"
Da sauri ta girgiza kanta tana jure murdawar cikin, a harhade ta ce" A'a, ba rashin gaskiya bane, banda lafiya ne"
A hankali ya zuba mata ido, sannan ya karaso ya kama hannunta suka karasa saman lalausar kujera mai girman gaske suka zauna, yana rike da hannun nata a tausashe ya ce" Me yake faruwa?, "
"Fama na yi ta yi da ciwon ciki, to kwana biyun nan na damu sauki sosai fa, ban san me ya dawo da shi yanzu ba" ta fada tana dubansa da kyau da son ya yarda da bayanin ta
"Subahanalah, ciwon ciki.....????????, kin ga likita? Me ya ce????" Ya fada a nutse yana sake zuba mata ido
A tausashen itama ta ce" Eh na ga likita, yanzu haka da maganina ina sha na ji sauki kana gani da sauki, sai dai périod dina ya zo min a ba zata......"
Idannuwansa ya lumshe kadan, sai kuma ya bude ya zuba mata su, a hankali ya ce" Dama ba sai 05 kike périod ba?"
Gabanta ya sake faduwa, ta dan daburce kafin ta sauke wata irin ajiyar zuciya a boye, ta yi mugun kalar tausayi a birkice ta ce" Ka san tunda aka samu matsala wajen haihuwar yaran nan menstru dina ya rikice, ban kuma samunsa dai-dai ba, ai ka ga likitan da nake gani dan maganar haihuwar ta yi bayanin wasan da yake min yanzu ya sa ba'a samu wani cikin ba....."