← Book details Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 78 OF 141

Sashe 78

Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da sauri Anna ta zo dan ta kamata ta zaunar da ita, sai dai ina ta ki haka ta hanyar bige hannun Anna ta tashi da kanta ta je bakin gadon ta ta zauna jiki na mata rawa rawa irin na abin shekaru ta dubi Anna ta ce" Mi kike tunani, a tunanin ki dan kin wuni baki zo inda nake ba mutuwa zan yi? Kina tunanin rayuwata a jikin taki take ta yadda zan kasa kula da kaina? Na rasa d'ana ma na rayu bale ke da ya gani a gari ya dauko min? Ni na san wata rana sai kin gaji da Ni, na sani cewar wata rana sai kin gaji da Ni a duniyar nan, sai gashi da wuri haka har kin tsane Ni kina min wulakanci"

A tausashe Anna bayan ta zauna tana cenzawa ina Safar kafarta ta ce" Aya ina ki yi hakuri dan Allah, ba mantawa na yi da ke ba, ina ce mai kula da ke ta sanar maki abinda ya dauki hankalina? Ama duda haka a raina kike ina, dan Allah ki yi hakuri"

Bude kofar yayi ya shigo a nutse da Salama a bakinsa ya karaso yana kallon Anna,

A hankali ya duka ya karbi kafar ta ina ya saka mata sabuwar Safar sanan ya dago yana kallon kukan da ta fashe masa da shi

A tausashe ya ce" Me kike yiwa kuka ne?"

Ina ta ja hanci tana dubansa ta ce" Menene ma ba zan yiwa kuka ba ? Yanzu ace a duniyar nan kaf in rasa mai leko Ni a gidan nan? Dama ita ai na san sai ta gaji da Ni wata rana, Ama ace wai a ga y'ar wajen yarinyar cen da ta haukace Ama ba wanda ya kirayeni na ganewa idannuwana abinda yake faruwa? Wuni na yi a dakin nan babu wanda ya fitar da Ni, da na ce Zan fita aka ce ba kowa a gidan sai matarka kadai, Ni kuwa har ga Allah tsoro nake ta min shaƙar mutuwa ta kashe Ni, saboda tunda na sake cewa ban yarda da duwawun nan nata ba take hararata, na fadawa sirikarta tace in yi hakuri, Ni damo ce da kowani shege zai min iya shege ace in yafe masa?, Ni ai ina tsoron hakurina ya kai wasu wuta a gidan nan, ka duba ka gani tsabar ta raina Ni sai yanzu ta shigo dakin nan, Allah da ya sa ai ina iya kulawa da kaina, ba sai na jira komai daga wajen kowa ba ehe!"

Dubanta yake yi da fuska a hade, ya ce" Wai du waye kike ma haka din yanzu? Kawai shiKenan idan kin tashi abinki sai a kan uwata zaki sauke???"

Anna ta Dube shi da sauri ta ce" Kai, bana so, kar in ji"

Ina ta tare goshi ta fashe da kuka ta ce" Barshi barshi ya zane Ni, ai du duniya dama ke kadai ke tausayina kike lalaba Ni, yaron nan in aka bar Ni daga Ni sai shi sai ya zane Ni , Ni fa du hankalina da ya tashi ba komai bane sai tunaninki, ina kike me kike yi? Ama ba damar in jajanta zai a min alamun za'a dake ni?"

Anna ta ce" Yi hakuri ina, shi din banza ya dake ki? Yi hakuri ki kyale shi, me yake maki ciwo ne yanzu???"

Ina ta kama hannun Imad ta kai wajen kirjinta ta ce" Nan dina, a nan dina nake jin haushin ban ga yarinyar nan ba, ina matukar jin haushin haka, bale da tace min su biyu ne sai na ji raina yayi bakin kirin da ba'a neme Ni suka kawo min gaisuwa ba!"

Murmushi Anna ta yi tana kallon tabe bakin da Imad ta yi a tausashe ta ce" Ai zasu zo su gaishe ki, tana da yar uwa da kuma dan uwa namiji ina"

Ina ta ce" To fa, dama mahaukaciyar uku ta haifa kuma aka sace? Na so in ga barayin nan da yau ban san yaɗa zan yi da su ba, dan Ni suka hada da alkakai da suka sace ya'yan nan basu hada da ita ba, suka bar Ni da balakin makar nan, kulun fa sai ta kayar min da gaba in ta shigo, zuwa take kai tsaye ta kai hannu kusan hancina tace wai dan ta ji ko ina numfashi ko na mutun ta huta, har tsoron jin motsinta nake yi , idan na hangota na san kafin in buya ta tardo Ni sai kawai in yi barcin gangan, ta gama abinta ta tafi dan an daure mata a gidan nan idan na yi wasa yaron nan sai ya kai Ni a rufe saboda matar nan"

Murmushi kawai ya yi a ransa yana Ayana ' Hum, in dai mahaukata ne ai ina ga kima da farin jinin janyo su jikinki ne , zaki yi bayani idan wace Anna ta samo maki ta maki tsaye zir a gabanki....kai innalilahi wa Inna ilaihi raj'une yau Ni na ga tashin hankali kala kala, mtssssssss Allah ya bata lafiya, Ama wannan kam ai sai a hankali'

A bayane kuwa sai ya gyara mata kwonciyarta ya ce" Yanzu dai mu yi addu'ar barci, ki kwontar da hankalin ki zata zo ki ganta be ai, ki yi hakuri haka"

Tana gyada kai tana kallon Anna ta idasa gyara mata komai harda ajiye mata ruwan da take sha cikin dare kafin ta basu waje,

Imad na rike da hannayanta yana sauraronta bayan sun yi addu'a kuma ya sanar mata ta yi shiru, Ama ta ci gaba da yar mitar ta da fadace fadacen ta a dole yayi shiru ya kyale ta har sai da barci ya dauke ta sannan ya rage mata hasken dakin ya bar mai dan duhu duhu kafin ya ja komar ya kuma nufi dakin Anna suka yi sai da safe sannan ya fito ya sauka ya nufi bangaren sa cike da gajiya, sai dai abinda ya fi gajiyar tuko shi baya tunanin in har zai bar shi ya iya rintsawa a yau ba tare da ya sauke shi ba!

Yana shigewa elevator Farhana dake gadin ganin ya bar wajen ta fito da dan sauri ta fada dakin anna da bargonta wanda ke nufin kwana ta zo ta rufe kofar tana nufar dakin barcin Anna dan ta tabbata tana cen

Ai kuwa tana shiga ta same ta tana shafa dadadar humura har ta yi shirin kwonciya

Murmushi take yi tana kallon Anna ta ce" Anna, ya gajiya"

Anna ta dube ta, sai ta yi murmushin itama a nutse ta ce" Wayon ne zaki yi dan kina son kwonciya a dakina ? Farhana ki kwaso kayan ki ki dawo nan kawai sai a rufe dakin ki mana"

FARHANA ta haye saman katon bed din Anna tana jefa bargonta hadi da kara gudun ac sannan ta dafe habarta da hannayenta biyu a tausashe ta ce" Anna, wai kin san me ya faru yau a nan corridor?"

Anna ta girgiza kai tana duban ta

Farhana ta yi murmushi ta ce" A lokacin da kuke da baki a kasa fa, Hallah da MAZNA fada suka yi, har Hallah ta saka ta kuka"

Turus Anna ta yi tana dubanta ta ce" Ban gane ba, me ya haɗa auntynki fada da Hallah kuwa karamar kanwarta?, me ya faru ne?"

Farhana ta yi murmushi tana jin dadin zata fadi abinda ke ranta cikin Salama ba tare da an ce ta yi tsegumi ba

A tausashe ta ce" Hum, Anna Ni ai yau abinda na gani ba kadan bane, kin ga dai ai Yaya ya hayo da Hallah , ban san me yasa ba dai, Ni dai ina tsaye ina jira yace ta zo wajena kawai sai ganin MAZNA muka yi, wai kin san maganar da MAZNA ta fada Anna a kan d'anki ko? Zuciyarki ba zata so ji ba, Ni maganar har kunya take bani....."

Ta karashe tana wani sune kai kai ka ce da gaske take

Anna ta zuba mata ido, da kula ta zauna bakin gadon ta ce" Zaki fada min ko sai ranki ya bace "

FARHANA ta girgiza kai ta ce" Zan fada, Anna dai kawai sai MAZNA ta fara zage zage, tace yayana ashe munafurci yake mata da HALLAH? Wai to kenan a Boye kila aura masa Hallah?, mtssssss ke dai tsoro ya sa Hallah rukunkume yaya, ruf ta rukunkume yaya, aka juya aka juyo da kyar na bambarota tana ta kuka a tsorace, kai Anna yau yarinyar nan sai da idasa tabbatar min bayan rashin tarbiyya da raina maman mijinta da ta yi harda zargin mijin nata take yi, ta Tsorata yar mutane ta saka ta kuka, da kyar fa na rarashi Hallah ta hakura tace ita ba komai ke ai mamanta ce, dan yaya ya rungumeta kuma ai ba komai ta san ba zai cutar da ita ba...., ita kuma yarinyar nan sai da na kara raina mata wayo....., baki ji haushin da na...."

"Kina nufin, MAZNA ce ta cewa yayanku Ni na aura masa Hallah, tace ya munafurce ta?"

Anna ta fada a hankali tana nuna kanta

Farhana ta yi dan shiru tana maimaitawa kanta maganar ita ma, dan har ga Allah sai yanzu ta ji kar dai Anna ta yi kuraya a ci mata uwa a gidan nan

Gyada kai take yi cike da tabbatarwa ta ce" Anna sai in rantse maki da Allah in kina so, abinda a nan aka yi a gaban yan uwan ta har suka shigar mata fada ?, sam basu da tarbiyya!"

Anna ta yi shiru tana kallon farhana

Bata tunanin Farhana zata yi karya mai girman wannan, to idan ta tuna ma da abinda ya ki fada mata a kicin ta yiwu maganar rungumar ce ko kuma ta fadan , dan idan daya ne a ciki ma ba zai fada mata kansa tsaye ba saboda yana iya jin kunyar hakan.....
Chapter 78 · 0% Book details