← Book details Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 141

Sashe 38

Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya Allah, duk wata damuwarta ta kau, idan yana nan hatta kakarsa na jin kunyarsa bata zaginta ko zagin FARHANA a gaban shi, in yana garin Farhana tana zamowa irin ya'yan da take so, wato nutsatsiyar yarinya mai kiyaye harshe da duk wani abu marar dadi....., idan yana nan karya ne ka ji bangarenta yayi shiru, to ko matarsa da kannenta suna cika musu wajen nan all time, koda yake kannen nata idan yana nan a nan bangarensu suke a dakunan su, dan kowace da dakinta, namijin ne nasa dakin a baya yake shima baban waje da aka gina masa hadi da duk wani abin bukata....., kai idan yana kasa hatta shukokin gidan nan sun fi shudi saboda an fi basu kula kulun ta Allah......, hum idan fa yana nan NUTSUWA bata taɓa gushe mata sai abinda ba za'a rasa ba.........

A hankali ta sake shi saboda kunyar jama'ar dake falon kar su yi mata wata fasarar

Su Abdul bassit kuwa normal ne ai, mahaifiyarsa ce fa, wace ya jima bai gani ba, tana sakinsa Abdul Fatah ya karaso yan uwansa na biye da shi, suma suka ringa zuwa da daidaya Anna na kama hannayensu da mana musu kis a goshi fuskarta dauke da matsanancin farin ciki , idannuwanta cike da hawayen farin ciki.........., dayan hannunta rike da nasa, shima sai sake leka fuskar nata yake murmushi kwonce saman fuskarsa.............

Dukawa MAZNA ta yi har kasa ta furta" Barka da warhaka Anna"

Anna fuskarta bata gushe da fara'a ba ta furta" Barka da sauka yarinyata....., fatan kina cikin koshin lafiya?? Yaya sauƙin jikin ki??????"

Cikin FARHANA dama du a kule yake, sai kawai ta yi murmushi ta furta" Alhamdulilah.........." Zuciyarta na ta bugawa

Anna ta mika mata dayan hannun a zuciyarta tana tunanin 'Au haba gaske na ga shirun nata yayi mugun yawa, ashe tana wajensa ne...., Allah sarki, Ama kamar ta rame ma baiwar Allah ko dai wata kama ce da ita????'

Daukowar ranta ya dade a karo na biyu ya sa Anna sakin murmushin da bata shirya ba, domin kuwa harda su nikaf Farhana ta daura a fuskarta abinta , hijab din kuwa tamkar zai tadeta ya yada ita kasa ne , ta fito a hankali murya a kasa cen ta furta" ASALAMU ALAIKUM wa rahamatullah"

Anna ta sake sakin murmushi ta daga dubanta ta sauke kan FARHANA da kanta ke kasa, sannan ta kalli ƴaƴanta da yanzu ya bita da kallo daga sama har kasa kafin ya saki murmushi ya furta" Farha, ta'al khalby....."

Daga dubanta ta yi ta kalle shi, sai kuma ta karaso din fuskarta dauke da fara'a ta kame hannunsa da ya miko mata ta kai wajen goshinta a hankali ta goga a tausashe ta furta" Yaya, na yi missing din ka sosai"

Anna ta sake sakin murmushi tana kallon su, kafin ta ce" Masha Allah, ku zo mu karasa ku zauna in taso mutane a sama muku abinci da abin sha da komai da komai, .....ya Allah me yasa kake son yi min zuwan ba zata, yanzu fa sai kun jira abinda zaku ci ko?"

IMAD ya riko hannun Anna ya ce" Ummi, ummi plz..., zo mu zauna , ki bar su MAZNA su kawo abin shan, Ama abinci sai da muka cika cikin mu kafin mu karaso dan na san dare ne ba zan kawo maki aiki ba....., kuma a bar masu aiki zamu hade da safe in sha Allah, MAZNA da FARHANA sun isa su bamu kulawa"

Yana fada suna karasawa saman kujera ne, Anna ta zauna , kafin ya zauna daf da ita yana rike da hannayanta

Anna ta ce" Ama yaya za'a wahalar da ita baiwar Allah a gajiye? "

Da sauri MAZNA ta ce" A'a Anna ina iyawa, ba komai....."

Da sauri ta yi hanyar kicin dan a ciki manyan frij suke dauke da kayan sha, haka kuma a ciki kayan fruits suke...............

FARHANA ta yi dan tsai ta bita da kallo kafin ta yatsina baki ta juya ta bi bayanta dan ba zata ce mata komai ba gani zata yi abinda zata dauka ita sai ta dauko wanda ba shi din ba

Murmushi yayi yana tunanin gajiya? Ko wani aiki suka yi a gidan? Ko kuwa ta leka makaranta ne itama yau?, Ama yadda ta nuna koda a gajiyen take zata iya yi ya birge shi har ya saka yayi murmushi kafin ya sake duban anna a tuasashe ya ce" Ni ban ga su JAUHARA ba, ko sun yi barci ne???"

Anna ta dube shi, kafin ta dubi su Abdul Fatah da suke ta doka murmushi, saboda irin yadda zakin su ya zama wani dan shagwaba a gaban anna, a yanzu kam sun gama gane cewar kwarai yana da bukatar kasancewa daf da gida,

Anna ta ce" Tambayoyin lauyan nan basu gushe ba a bakinsa kenan?, ka bari ka huta du sai mu yi ta tambaya da amsa din ko?........"

Murmushi yayi yana sake riƙe hannun Anna a hankali ya bi MAZNA da kallo lokacin da take ajiye kayan motsa bakin da ta jero saman table din da ake turawa ta turo......................

Ajiyewa ta yi , sannan ta juya ta amshi na hannun Farhana ta ajiye , ta yi niyar zaunawa idannuwanta suka shiga cikin nasa

Da kula ya mata alamun ta hau sama, ko ta koma ɓangaren su, hakan ya sa ta dubi Anna da girmamawa ta ce" Anna, bari in je , sai da safe in sha Allah, brothers Allah ya hutar da gajiya"

Anna na murmushi ta ce" Amen yarinyana, Allah ya hutar da taki gajiyar , mu kwana lafiya"

Daga haka ta juya da dan sauri ta yi waje, ya rage FARHANA dake dan cicira ido tana ayyana magana kamar haka' to ai ya dace nima gayar sodi in bace a wajen nan, tunda matar OGA ta tafi ai nima tafiyar kawai zan abina '

A hankali ta mike tana dan satar kallon Anna , murya a matse dan gudun ta yi laifi ta ce" Zan, zan shige, Allah ya hutar da gajiya yaya"

Dubanta yayi ya dubi Anna ya ce" Wai Anna cenza maki y'a aka yi hala???"

Anna ta Dube shi, ta dubi Farhana,
Dariya ta yi tana dubanta ta ce" Hum, ladabin kunama ake yi nan da ka ganta, ai bata san da zuwanka ba ta yiwu da tardowa zaka yi tana ta karatu ko auta???"

FARHANA ta turo baki abin shagwabar nan, bata ce komai ba kanta a kasa ta juya dai zata bar wajen suka yi ido hudu da Mutalab......, wanda du wannan shagali da ake yi shi shagalinsa a nan ya kare, kallonta kawai yake yana murmushi ........, ya Allah gaskiya FARHANA ta girma, rabonsu da ita an jima, an jima sosai, katari ake yi idan ƴaƴanta zai zo ita bata kasar , idan ya tafi tana nan, sai ya zama suna ta saba kiwo tsakaninsu........

Kai ta dauke ta karasa elevator ta dana ta shige abinta ta wuce dakinta tana zaunawa ta rafka tagumi da tunanin yadda zasu kwashe......, wannan dariyar da yake mata ta tabbata kafin ta yi laifi ne, ga Anna kamar zata tona mata asiri fa, Anna kamar zata ce bata ji, bayan ita ba abinda ta yi tunda ta zo, laifinta daya ne wanda ta sani shine tunda ta zo bata gaishe da tsohuwar cen ba, bayan wannan ba wani abin da ta yi gaskiya, shima kuma zata gyara zata je ta gaisheta da duku duku tun kafin kowa ya farka, yanzu haka in ba dan gudun kar aje ta tashe ta ta gaisheta matar nan ta ja mata wani sharin ba ai da ta je ta tashe ta, to yanzu abin alkairi zai koma na tsiya in ta tashe ta, gwara su hade da duku dukun safiya!

A kasa kuwa Malan ne da kansa ya nemi izini ya shigo ya sanar cewa an gyara komai na bangaren baki, saboda a rufe yake ne ma ya sa suka je yanzu harda shi malan din a tsaye a kansu aka gyara komai aka CENZA labulaye aka wanke bayi.........

Godiya ya yiwa Malan din, wanda ya ji dadi har ransa....., hakan na cikin abinda ke saka shi kara girmama uban gidan nasa..... Sam dukiyar IMAD bata haukata shi ta yadda zai wulakanta mutane ba......., to ko matarsa fa shi gani yake yi da sauki, saboda ba zata shiga harkar ka bama bale har ta wulakanta ka, ba bin didigi, ba wani shiga hurumi, ai kuwa da sauki kan wasu iyayen gidan da suke hana mutun motsin kirki dan mijin su ke kawo shinkafa ..........

Anna ta Dube su da kula ta ce" Ka ga, ka tashi ku je su sauka a bangaren su, kaima ka je naka ka huta ka ji? In sha Allah zamu hadu da safe"

Mikewa yayi yana sumbatar bayan hannun Anna a tausashe ya ce" Allah ya hutar da gajiya Ummi, Allah ya tashe mu lafiya....., kar ki sanarwa anmy na zo plz"

Anna ta yi murmushi tana gyada kai sannan ta mike tana kallon su har suka wuce zuciyarta fari kal da farin ciki mai girman gaske

Sai da ta kashe komai sannan ta shige elevator ta haye sama

Direct dakinta ta wuce ta gama abinda zata yi ta zauna bakin gado tana karanta Alkur'ani Farhana ta buga dakin

Bayan ta bata izinin shigowa ne ta shigo da abin rufar ta, ta haye saman gadon Anna tana fadin" Anna, na kasa barci a cen"

Anna ta yi murmushi tana dubanta a hankali ta ajiye litafin ta shiga dan shafa kanta ta ce" kin ga kuwa ashe MAZNA bata zo bama, ashe sunna tare har nake ta tunanin ya aka yi bata zo ta gaishe Ni ba"

FARHANA ta ɗan daga kanta ta dubi Anna kafin ta ce" lah wai wannan matar? Tana gidan nan tabbas, na ganta da idona, idan dare yayi sosai take fitowa ta zagaya a kafa ban san tafiyar me take yi ba, ita da kannin, Ama kam tana gidan nan zuwa ne bata yi ta gaishe ki ba gaskiya"

Anna ta zuba mata ido, haka kawai ta ji zuciyarta na son cinkushewa da jin wannan batu........

A hankali ta dauke idannuwanta daga kan FARHANA batm tare da tace komai ba............
Chapter 38 · 0% Book details