Sashe 68
Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Baban yara kuwa lokaci lokaci yakan dauke kwalar dake idannuwansa , zuciyarsa a raunane take sosai....., shi kadai ya san halin da yake ciki da wannan abin da ya same shi rana tsaka.....wai yau iyalinsa ce aka tirtse a gaban al'umma ake Shari'a haƙa......yau shi ne a gidansa aka samu wannan tonuwar asirin har haƙa? Yau Maman yara da ya rayu cikin yarda da ita dari bisa dari ce ta aikata haka? To bayan wannan me da me maman yara ta aikata a rayuwa? Me da me ta yi a rayuwar nan?
Kai ta dauke daga kansa bayan dogon tunani da nazarin da ta yi a zuciyarta
Shin idan har aka gane kishi ne kawai ya sa ta aikata haka ba wani abin ba zasu kyale ta su barta ne? Idan suka kyale ta suka barta ina zata nufa sama da gidan Malan?, to ai bata gama saka matar Malan a uku ba, haka kuma bata ga kukan malam saboda auren da ya jajibo mata ba, zuciyar nan Tata mai bijiro mata da wani tunanin cewa yaya zata yi in ba Malan ce ta bijiro mata da tarin abinda Malan yayi mata wanda ya sa tun a lokacin da ta yi bada kamar amsar cikin A'isha rabonta da shi har zuwa yanzu da bata bashi wani hadin kai na aurataya ba, shi zai sa ta idasa saka Malan hawaye da kuka tamkar na gidan makoki idan har ta idasa nufin ta a kansa ta hanyar NUR ya sa ta Dubi sojan nan ta ce" Daga Ni sai aminiyata muka aikata abin, kuma ita ta bani shawarar abin a lokacin da ta ga ina cikin damuwar abin!"
Sojan nan ya ce" Ki fada mana komai, saboda mu san wanda yake da laifi, sannan ku fada mana wani ne ya turo ki dan ki sace abinda matar nan ta haifa saboda a cin ma uban gidanta ko me????"
Da rashin gane abinda yake nufi ta Dube shi, sai kuma ta dubi wanda aka nuna uban gidan ko me??????
Kai ta girgiza ta ce" A'a, Ni ai ban ma san shi ba, ban san matar da kanta ba, maganar da nake maka Ni ban taba ganin iyayen yarinyar da na dauka ba, kawai dai nima bukatar haihuwar nake, na kuma gane cewar tunda ta haifa zata sake haifar wasu, kuma ba wasu ta rasa ba a gida...., kenan dan na dauka ba da nufin cutarwa ba, sai dan nima in zo dai-dai da mutuncin da Amaryar mijina take da shi a gaban mijina, a cikin dangin mijina, ya zamo Ni ma na taka wajen da ta kai duda Ni ce ya dace ace na fi ta wannan daraja, Ama rashin haihuwar nan ta sa kowa ke min wani gani gani, danginsa da abokansa munafukan ciki suka matsa masa har sai da ya dauko min kishiya, ya kawo ta cikin mu ya ajiye, ko wata biyu bata yi ba ta fara amaye amayen ciki, ina kallo a gabana ta haifi d'anta, ɗan da mijina ya sakawa sunan baffansa wanda ya rike shi har ya masa aure, ina kallo ake yi mata fifiko a kaina a abubuwa da yawa, ina kallo a gabana aka mayar da ita mowa, dalilin rashin haihuwata ake zagina, a dalilin ban hiahu ba hatta shi yi yake yi kamar ya manta da Ni.........., ..., to Ni kuwa sai na dauki shawarar kawata da take so na....., muka yi goyon cikin tsuma mu dauko A'ISHA!"
Sojan nan ya nuno ta da yatsa bayan ya mike ya nufo ta da nufin make ta ya ce" Ama lalle ke baki da mutunci, shi ne kike fada mana kanki tsaye ba wani dari dari ?????"
Hannunsa kawai ya daga ma Aliyu, shi ne ya dakatar da sojan daga nufin mauje maman yara wace tuni cikinta ya murda, dan ba zata so a taba mata lafiyar jikin ta ba.
A hankali ya dubi Anna, a tausashe ya ce" Anna, a zo min da Mama plz"
Su dukansu kallonsa suka yi, ciki harda Malan da kawai ya zubawa maman yara ido gabansa sai dokawa yake yi, haka ma auntyn yara kirjinta sai bugawa yake yi ta zuba ma maman yara ido , da kallon da bata taba yi mata ba, mai hade da tarin fargaba, tsoro, tausayi, ganin beke.
Mikewa Anna ta yi bayan ta zaunar da Nur saman kujerar ta sanar mata ta zauna tana zuwa, sannan ta wuce ta bi ta kicin ta tafi.....
A hankali Nur ta silale kawa daga saman kujerar ta sauka kasa saboda sam ba zata iya zama a sama bayan mahaifiyarta na ƙasa ba, ta sauka kasan ita ma sannan ta dago idannuwanta da suka cika da hawaye mai zafin gaske, ga mugun ja da suka yi suka kara girma ta sauke a kan Mama.......
Ya Allah, mama?
Dama ba ita ta haifi A'isha ba, kuma ta dauko A'isha ne ba dan tsananin kauna da son A'isha ba, sai dan ta samu abinda kishiyarta ta samu ita ma?
To ina mamanta mai kaunar su, da tausayin su, da kare duk wani hakinsu ta shiga????,
Shin zafin kishi ne ya sa mama aikata wannan din ko kawai son zuciya ne??
Saboda wannan kawai ta yi ko harda wani dalilin????
A hankali ta kai idannuwanta kan d'an gidan Anna
Sai kawai idannuwanta suka shiga cikin nasa , domin tunda Anna ta zaunar da ita a saman kujerar nan ta bada baya , har zai mayar da dubansa inda mutanen nan suke gaba daya, sai ya ji ya gaza duban kowa a ciki, haka kuma ya sada kai ya ishe shi sadawar, sai ya samu kansa da zuba mata idannuwan ba dan zai ha wani abu ko dan wani abin ba, no, kawai dan nan din idannuwansa suka sauka....., sai ya ga irin duban da ta daga ta sauke a kan fuskar wannan mata dake dauke da laifin nan......, duban ya matukar tsaye masa a rai har ya sa ya dan saci kallon matar....., sai ya ga ita kuma tana duban fuskar kowa ta yi magana kanta tsaye na rashin dadinta hankali kwance , Ama sam bata sauke dubanta a kan wannan yarinya ta wajen Anna ba.............
Cikin ikon Allah ido cikin idon da suka yi babu wanda ya janye nasa duban har sai da shigowar Anna ta sa suka kai dubansu kan Anna da Mama dake tafe tare da Annan .........
Ido du aka zubawa Mama a lokacin da Anna ta zaunar da ita kujerar dake kusa da ita , wace ta shiga tsakaninta da IMAD kasa kasa ta ce" A'a wani aure kuma maman IMAD, zauna ke dai mana zauna"
Ta zauna din tana murmushi sama sama ta ce" Ni ai na zata aure zamu mata mu rabu da ita daga gidan nan....., wannan tsohuwa an yi yar jaraba, kuma ta ki mutuwar ma bale mu huta in ji FARHANA"
Anna ta rasa yaya zata yi ta sa ta yi shiru, sai kawai ta sauke ajiyar zuciya ta kai dubanta kan mutanen dake wajen a tausashe ta ce" Ku yi hakuri, tana da yar matsala ne, Ama tunda Malan na wajen zata yi shiru..mm, kin ga maman IMAD dubi cen ga fa Malan cen, kin san ya hana ki magana a gaban baki ko? Yi shiru abinki kar ya jiyo ki mana"
Dubanta ta kai kan mijin nata tana gyada kai kasa kasa ta ce" Eh to bari in kyale, wancen ai maketaci ne, ko yayi ta tofa maka yawu, ko ya Barka sai dare yayi ya........."
Da sauri IMAD ya ce" Mama, yi shiru mana"
Anna kam ta gama rintse ido, dan ta sadakar cewa zata idasa zancen ta ne, haka ma Malan din da kansa har ya kuma tagumi hadi da sada kai sai Allah ya taimaka ya katse ta, kuma ta katsu din tana girgiza kafa abinta
A nutse ya maida dubansa kan Maman yara a tausashe ya ce" Kin ga wannan matar, haihuwar ta uku a duniya, na farkon ana haihuwar ta ta rasu, na biyun yana da shekara hudu ya rasu......, haihuwar kuma ta tsaya, aka yi ta addu'a da dangana har Allah ya kawo ta bayan shekaru sama da goma......"
Ya ajiye maganar ya sauke dunansa a kan A'isha, wace har yanzu bata fito da fuskarta ba, sai sake nanikar auntynsu take, kafin ya sauke dubansa a kan fuskar auntyn a tausashe ya ce" Da Allah ya karbi abinsa....., hakura ta yi, ta dangana, dan ta san daga shi muke, gare shi zamu koma....., Ama da aka dauke mata sai ta kasa hakura a hankali a hankali damuwa ta haifar mata da ciwo marar dadi, ciwo mai girma irin na tabuwar hankali, wanda muna ji muna gani du irin hanyar da muka bi dan ganin hakan bai faru ba sai da ya faru saboda koda da sauki sai kawai abin ya rikice idan ta tuna cewar wata azaluma ce ta shiga ta dauke mata abinda ta haifa ko duminta bata ji ba bale ta shayar da ita........"