Sashe 116
Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A hankali Malan ya ce" Ikon Allah, Allah ya gafarta Malan, shin ina zan ga Elhajin ne?, ka kai Ni in duka in yi godiya, kuma ka sanar masa koda wani aikin karfi zan yi dan in dan fanshe abinda za'a min na alkhairi a bani dama, koda aikin gadi ne zan zage in yi mudin raina, in dai za'a yiwa AUNTYn yara daki sabo"
Sai kuma ya ɗan dafe baki yana murmushi hadi da shafa kai saboda ido ta zarro tana furta" Aban yara"
Anna kuwa me zata yi banda dariya cike da fara'a ta rike hannun AUNTYn yara ta hanata guduwa ta ce" Ina zaki je? Zaunawa zaki yi ai"
A dole ta zauna kanta a ƙasa cike da jin kunya, mama ma dariya take yi cike da tsari da kiyaye harshe
Malan na dariyar shi ma ya ce" Elhajin ne ban ganshi ba, rabona da shi dai da ya leka maman nasa dazu da safe............., ama a JIYA da safe yake fada min abin allhairin maganar zai je ku zauna ma kan maganar yara ko?, Allah dai ya nuna mana ya tabbatar mana da dukan alkhairan dake cikin wannan tarayya, kuma daga Ni har Mama bamu da ta cewa a kan lamarin y'arka, abinda ka yanke mu masu murna ne"
Aban yara ya dubi Malan da yanayin neman karin bayani ya ce" Maganar A'i? Wace magana?"
Anna ta Dube su da kula, sannan a tausashe ta ce" Ai basu riga sun yi firar ba , mun je ne muka same ka ba Lafiya, .......ai abinda ya kai mu gidan naka zuwa yayi da maganar yaran nan ne dama, ya je ne dan ya fada maka idan har yara nada tsayayu, a yi kokari a hada aurensu da na yar uwar tasu, wato FARHANA nan da sati biyu in sha Allahu.............., to kuma sai muka tarar ba damar maganar "
Malan ya jinjina kai , da kula ya ce" Allah sarki, Allah sarki, "
Yayi dan shiru kafin ya sauke ajiyar zuciya ya ce" To, a da dai, ita Auta tana da tsayayyen, domin ya matsa ma kan a bashi dama ya fito a yi a gama ......, Ni ne nace a bamu dama nan da shekara daya haka, ta yadda zamu kara sanin wanene shi, kuma mu yi tanadi irin na amfanin gona da sauran su, in yaso sai a sa bikin, kamar yadda shi ma babansu ya fada cewar zuwa lokacin shi ma ya gama nasa shirin , to kuma sai........sai"
Malan ya sada kai, kafin ya dago a tausashe ya ce" Sai na fuskanci mahaifiyar yaron bata son lamarin, Ni da kaina a yanzu ina jiran haduwata da yaron ne dan in fada masa ya bar maganar, domin ba zan taba bashi Auta ba, .............sai dai idan Allah ya fido wani sai a yi, ita kuma a'in babu tsayayyen itama , Ama fa a sanina, A'i ko AKOY wasu da kuke kulawa wa'inda ban sani ba? "
A'isha da sauri ta sada kai, cike da tsoron bayanin abansu......wani irin bata da , to jama'a to ya'yan fa?
AUNTYn yara ma a zuciyarta abinda take kai kawo kenan, sai dai ta san in dai har sulaimana bai nutsu ba, Malan fa ba zai taba bashi A'isha ba, hakan ya sa bata ce komai ba, kanta kawai ke kasa
Anna da mamaki ta ce" Aban yara, yaya maganar wajen ƴaƴansu ne?, ina ce an ce shi ne ke son A'isha?"
Aban yara da mamaki ya dubi Anna, ya ce" Hajiya wai shirmen na Sulaimana?, Sulaimana ai bai yi tsayuwar da kafafuwansa ta yadda za'a bashi aure ba, sulaimana baya ji Hajiya ai ba zan dauki y'a in bashi haka ba, yaron da yake yawan jaye jayen fitina?, ai da ace ma sulaimanan ya nutsu ne......"
"Abanmu, yaya ai ko yana yiwa kowa banda Ni, kuma ai yanzu baya yi din ma Abanmu........sannan yayan ai bashi da wata makusa Abanmu, dan Allah Abanmu ka......"
"A'i?" AUNTYn yara ta fada a tausashe tana katse mata hanzari
Da sauri ta zarro ido hadi da kame bakinta, kafin ta mike da gudu ta nufi wajen matatakala, saboda bata iya daidaita harkar elevator ba ta shiga haurawa a guje gumtse da bakinta cike da jin matsananciyar kunya.
Shi din ma idannuwan waje ya rakata da kallo kafin ya maido dubansa ya ga sunna dariya harda Mama wace abin ya bata dariya kwarai da gaske......., a tausashe ta ce" Ya'yan yanzu Allah ya shirya mana, to abansu kaine baka ganin nutsuwar ƴaƴansu, y'arka kam ta gama gani"
Aban yara sai kawai ya yi murmushi yana girgiza kai a tausashe ya ce" In sha Allah zan yi waya da baban nasa, abinda yace sai in zo in sanar ko in fadawa ita AUNTYn yaran, da yake yana cen wajen sa, idan har yace kwarai a yanzu yana iya rike gidansa shiKenan sai a yi , Allah ya zaba mana abinda ya fi zama alkhairi"
A tausashe Anna ta ce" Amen ya Allah, Allah ya aminta, ita ma yarinyar tawa, Allah ya tsayar mata da nata mai alkhairi.....ya bamu Aron kwanaki ya sa a yi da mu"
Du da amen suka ringa amsawa kafin Malan ya mike yana yiwa Aban yara Bismillah, hakan ya sa suka mike suka tafi bangaren da Malan ya musu jagora, shi din ma yana nuna musu ya musu Salama ya tafi, ya rage Aban yara da AUNTYn yara, domin Mama dama bata bi su ba tace a barsu su huta ne
Bayan tafiyarsu, Mama da kula take tambayar Anna inda danta ya shige ne? Domin bata ganshi ba ita, da suka je bata farka ba, abin maganin da take dauka barci yake saka ta mai zurfi, sai a yi abu ma a gama bata sani ba
Anna ta sauke ajiyar zuciya tana sake yarda da nutsuwar Mama, cewar a yanzu kwarai Maman zata iya jin abinda yake iya zama sirri ba tare da ta fada da bakinta a inda ya dace da inda bai dace Bama, hakan ya sa ta sauke ajiyar zuciya a tausashe ta shiga labartawa Mama abinda yake faruwa, har ma da wanda ya farun a yau, ta ɗora da fadin" yanzu nake cewa zan je in ga itama MAZNA halin da take ciki, saboda hankalinta a tashe yake sosai, shi kuma ya haye sama , kuma ba dakina yake ba tunda na kule dakina yau, ta yiwu yana dakin Inna ko kuma ya shiga wani dakin"
Hankalin Mama ya tashi sosai, ta mike da sauri tana girgiza kai, a tausashe ta ce" wani dakin ya shiga? Dakin a gyare Anna ?, idan AKOY kura fa ta kama shi? Ya Allah Ni na san yarinyar nan wata rana sai ta hadasawa yarona bacin rai mai tsananin da hankalina ba zai iya dauka ba, Anna halin da take ciki? Ta jima bata shiga wani halin ba, kawai shiKenan yarinya kullum cikin halaya mararsa dadi? Kullum cikin fitina da raina mutane? Ko yanzu ta daina raina lamarin ki?, Ni fa ba zan yarda ba, idan ta manta halayata ta da to yanzu na dawo hayacina , ba zan taba yarda da iskancinta ba Allah daya kenan!"
Anna ta riko hannunta saboda ta rasa ina zata nufa ta mayar da ita kujerar da kula ta ce" Ki yi hakuri mamansa, kin san irin zaman da nake yi da ita, Ni ba zan matse mata wajen da zata raina ni bama, idan kina tune tun tana amarya na yi iya yina dan ganin mu'amalata da ita ta yi karkon da ya dace, Ama da take ta turewa a dole na koyi hakuri da dangana, na kama girmana na kuma iya rayuwa da su a haka....................."
Mama cike da tarin takaici da kuma bacin rai saboda du abinda ya shafi d'anta kai tsaye yake gigita mata tunani ta ce" Anna, wani irin dogon lokaci ne na dauka a cikin jarabawar nan?, Innalilahi wa Inna ilaihi raj'une, Anna wace irin rayuwa ce yarona yayi da yarinyar nan?, wace irin rayuwa kika yi da ita???????, dama tunda na kali yarinyar na karanceta na gane cewar da wata a kasa, a cen ma dan kin hana ni fada masa ne, da tuni an wuce wajen, yanzu yarinyar nan bata tsoron ciwon Cancer?, bata tsoron wata fitinar?"
Anna ta sauke ajiyar zuciya ta yi murmushi a hankali ta ce" Ai ya'yan zamani, da wasu sakarkarun datijan suna tunanin duniya wajen zama ce, sun ki yarda cewar waje ne da aka zo a wuce, tafiya ce ake yi dan isa inda za'a zauna zama na dindindin, sukan manta cewar tafiya da ciwo baban tashin hankali ne bale da kaya a saman kai......, kuma basa ji basa ganewa sai idan duniyar ta sanar musu..........., kin ga abinda ya fi damuna kin san halinsa idan ya shiga baban abin da ya taba masa zuciya da karfi har haka........, baya ci, baya sha, yakan kilace kansa ne ya Boye, babu mai ganin fitar sa bale shigowarsa............., kuma idan ka ce ku yi maganar da shi a haka , sai dai ka kara tada wata fitinar..............., Ama yaya za'a yi? Dole za'a yi maganar da shi, dole za'a bashi hakuri a kuma taushe shi, dole za'a hana shi sakin yarinyar nan, saboda ita da yan uwanta basu da wasu yan uwan da suka rike mu'amala da su, suna da dangi Ama basa mu'amala da kowa, shi ne dangin su, shi ne komai nasu........, ba zan so duniya ta ɗan basu da wannan kariyar a tare da su ba...., ba zan so aurenta ya rabu saboda wani laifi da ta yiwa kanta, na tabbata taba son yaron nan, domin ita du abinda zata yi saboda shi ne zata yi, wannan na sani na yarda har zuciyata, .................., du tsoronta kar mijinta ya ga wata, tsoronta kar mijinta ya kula wata, gashi nan abu na neman zama fitinar da bata yiwa kanta tunanin ta ba!"