Sashe 83
Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sai kuma ta kamo hannun Nur da ta ɗan sake ja baya still idnanusanwa a kan fuskarsa cike da wani yannayi da ya tsaye mata a zuciya mai wuyar fasara, wanda zata iya kiransa da mugun rashin jin dadin irin yadda yace da ita wai Ke tashi daga nan........, ke tashi daga nan?, shin yana tunanin da ba Anna ce ba lafiya ba zata zo haka har ta duka inda yake? , da ba Anna ce ta samu ba lafiya ba zata duba?, shi kam shi da matarsa du haka suke ne? Me yake damun su ne? Matarsa bata da wata tarbiyya, ga raina talaka dan ita ta tabbata dan ta san bata da wanda zai rama mata ne ta zage ta har ta mare ta, da ba dan wannan ba ta san da bata isa ta taba lafiyarta ba, sai dai su sani, ita ba daya da zata ji tsoro ko ta ragawa tunda ba wanda ta zo ya bata tuwo, kuma matarsa ma ta sani wallahi idan ta kara shiga harkarta lilis zata yi mata, in takamarta tana da dan uwa namiji ita ai Sulaimana gareta mai dauko fada daga wata anguwa ya kai wata shi daya kuma ya ci fadan, sai dai a rufe shi idan aka taba ta sai ya rama mata.....................
Kanta ta dauke daga fuskarsa, a lokacin da Anna ta riko hannunta da kula ta ce " Ke taho yarinyata, jikina da sauki kawai ciwon kai ne ke damu na"
Yanzu kam muryarta a sanyaye, ba kamar yadda ta shigo da karsashi ba ta ce" Sanu Anna, Allah ya baki lafiya......"
Sai kuma ta yi shiru tana dan duban kasa kafin ta mike daga daf da Anna a hankali ta juya zata fice
Anna ta dube ta a lokacin da ta ga zata fice ta ce" Ina zaki je kuma? Ina A'ishan take ne? Ba a sake ku ba??"
HALLAH ta juyo, juyowar da ta sa ta sake sauke idannuwanta da suka dan cenza launi daga fari tatas zuwa dan ragewar haske kadan, sannan suka cika da kwallah ta sauke su fessssss a kan fuskarsa yana rike da farin kofin da ya sakawa Anna Efferalgan yana jira ya gama tafasa sannan ya mika mata ta sha , a zuciyarsa yana tunanin idan ta sha kan bai sauka ba asibiti zasu je duda bata son lamarin asibiti ama ba zai iya barinta cikin wannan yanayin ba................,
Maganar da Anna ta yi, shi ma sai ya dubi wajen , haka kawai ya ji ya dubi wajen, ba dan ya ga komai ba, no sai dan kawai ya ga inda zata nufa din......., sai kuwa idannuwansu suka shiga cikin juna a lokacin da kowanensu bai san cewa daya na iya kallon daya haka ba
A hankali ta dauke idannuwanta, ta hanyar lumshesu, a tausashe , sannan Muryar a shake ta ce" Tana kofa Anna, zan wuce gida ne "
Anna na dubanta ta ce" Gida kuma?, ba jiya a gabanki abanku ya ce idan mun tashi mu tafi da ku ku ga jikin mama ba?"
Nur ta gyada kai a tausashen nan ta ce" Eh Anna, A'ishan na waje idan kun tashi sai ku tafi da ita, ni ina son in je gida ne yanzun"
FARHANA dake dubanta a bayane ta karanci yannayinta, ba da wata hargowa ko irin yadda ta saba yi mata magana ba a gabansa ba ta ce" Hallah, me zaki yi a gidan bayan Aba yace mu je? Nan din ma ba gidan bane???"
HALLAH ta dube ta, ta sake satar duban inda yake ta karkashin idannuwanta a ranta tana ayyana ' Yaya zan bi ku bayan yayanki ya tsani gani na, kamar zan yi shishigi ne idan na takura na matsawa bin ku ma, to yaya ma za'a yi in iya bin ku bayan kamar yana min kyankyami a kallon da yake min? Ni kuma ai ba zuwa zan yi neman wani abu ba, da ace Anna bata nuna min uwa take a wajena Bama, ai ba abinda zai sa in zo inda yake!'
Anna ta dube ta da tsarewar fuska ta ce" Maza, ki min kiran A'ishan, ku zo mu harhada kayanmu mu tafi gidan, bana son wani zancen a nan kin ji ba?.........."
A hankali ta gyada kanta sannan ta juya ta fita, wanda hakan ya sa ya bi bayanta da kallo a hankali bayan ya mikawa Anna kofin nan ya maido dubansa kan hannunsa yana jin wani irin abu dake dukan masa zuciya mai kala daban daban
A hankali ya maida bayansa jikin kujerar nan ya jinginar yana fitar da wani huci a hankali....... rintse idannuwansa yayi a hankali ya dan lashi lebensa na kasa da ya bushe masa tamkar wanda yake jin kishi, bayan a makogwaronsa baya jin kishirwar..........., shin me yake damunsa ne ???????
Bayan Anna ta sha maganin nan ta dubi FARHANA da ta yi tsuru tana masa kallon mamakin da ita bata ga na meye ba, domin har dan talabe haba ta yi, sai da ta dube ta ne ta dauke kai bayan ta jijiga kan........... Dubansa ta yi a tausashe ta ce" Andadi, ban sanka da saurin yankewa Mutun hukunci irin haka ba, ban san me yarinyata ta yi maka ba, Ama na san kana mutunta du abinda na mutunta, bale mutun sukutun, na tabbata idan ka zauna da NUR zaka so ta, tun kafin in gane ba mahaifiyarta bace ke yi mata rikon KISAN MUMMUKE na gane wace take hannunta bata son ta da alkhairi, a magana da na yi da ita kawai na gane sam ba wani abin kirki da matar ke sonta da shi sai tabewa, a lokacin ma na kamu da mamaki kwarai da gaske, daga baya ne na gane cewar ba ita ta haife ta ba, haka kuma bayan wannan bata yi mata rikon amana, bata son ta da alkhairi ........Please kar ka ringa yi mata tsawa, yarinyar nan bata san tsawa ba, ta fi ganewa rarashi a kowani abu, saboda wace ta jima tana muzguna mata ta hanyar rarashi take dora ta a dakalin bera, idan ka ga ta zo inda nake wajen mamanta ta zo, kafin in samu ta saki jiki da Ni haka an jima....plz kar ka sa ta daina zuwa inda nake domin Ni ina son yarinyar nan ina son ci gaba da koyar da ita ilimi ina so in ga wata rana ta zama wata gagarumar mace a fanin ilimi............., Andadi ka ji???"
Idannuwansa da ya bude tunda ta fara maganar nan ya zubawa fuskarta ya lumshe a hankali wanda hakan ke nufin amsar kenan, saboda haka kawai wani abu ya dane masa kirji da ya shafi yarinyar nan........
A hankali ya ce" Yaya kan? Ina so ki ga likita saboda matsalar low BP din ki Anna"
Anna ta yi murmushi a tausashe ta ce" Da sauki fa, kar ka damu da sauki"
HALLAH na fita ta tsaya tana duba inda zata ga Anas ɗan abinda ya fara fada mata ya tsaye mata a zuciyarta sosai, sai dai du hangen ta bata ganshi ba, bata ga Aliyu Bama bale shi, sai kawai ta dubi A'isha da ta karaso ta ce" Ina Anas din yake ne?"
A'isha ta waiga itama kafin ta ce" Dazu dai suna nan tsaye, kuma sai na ga Aliyu ya dora hannunsa daya a kafadarsa sun yi gaba, ta yiwu sun zagaya ne"
HALLAH ta ce" Ina zasu zagaya? Ni ina mamakin Anas da yake kyale wannan Aliyun, mtsssssss yo in ma dan maganar uban gidansa ne ai ba shi yake yiwa aiki ba bale yace shi yake yiwa aiki yana tsoro ya kore shi!"
A'isha ta ɗan kame baki ta ce" Ama ke ma kin iya rigima, to in bai kyale shi ba yaya zai iya da shi? Ko kokowa zasu yi kin ga ai ba riba saboda a ido ma zaka gane ya fi karfinsa, yannayinsu ba daya ba, bale ai da gani kin san shi ma gaba yake da shi a wajen aikin......, Ni dai ba ruwana da neman fadan ki wallahi "
HALLAH ta tabe baki ta dubeta ta ce" Shi yasa ba zan taba yin aiki a karkashin wani ba, bana fatan aikin Gwamnati a rayuwa, dan baka da wani iko da kanka sai yadda aka yi da kai bale wani mai kudi , Ni gwara in siyar da kosai da in zauna karkashin wani fa, su masu kudin nan gani suke yi komai suna iya yiwa mutun a zauna lafiya, to Ni in ba katari aka yi ina jin kunyar wani naka Bama ai da tuni na mayar da abinda aka min, Ama ba komai rayuwa ce , Han kak........."
Sai kuma ta juya kai tsaye zata sake komawa ta bude kofar
A'isha ta riko hannunta da mamakin fadan da take yi ta ce" Ke da wa wai???"
Nur ta dubeta ita ma, sai kuma ta girgiza kai ta ce"Ba kowa........ Anna ta ce in kirawo ki"
A'isha ta sake duban ta da mamaki kafin ta bi bayanta suka koma office din na Anna tare
A lokacin da suka shige ma, Su Aliyu na daga baya wajen motar da yake jan IMAD a ciki
Anas na dubansa da kula ya ce" Ka ga msg din da Anna ta min, ta ce in bari lokacin da na fito in same ta a nan fa, ba da gangan na ki zuwa daukanta a cen ba"
Aliyu ya duba msg din, kafin ya bashi wayar yana sake tsare shi da kallo daga kasa har sama, a nutse ya dan kara dafa gefen kafadarsa yana dubansa da gogangen turancinsa ya ce" Ma'aikacin da ya dauki aikinsa da mahimmanci baya tsayawa lokacin aikinsa yayi bai je wajen ba........, ya dace ka kula da wannan , kar ka yi aiki da kirki uwar gidanka ka ringa wasa da aikin ka"