← Book details Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 117 OF 141

Sashe 117

Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mama ta girgiza kai, a hankali ta ce" Ita ai bata taɓa ganin irin darajar da Allah yayi mata a rayuwa ba, bata tunanin komai dai kanta......, Mama zan iya daukan komai ne banda abinda ya shafi taba masa zuciya....., kuma kar ya ga wata? Ai sai dai ta yi haukanta ta gama na rantse ba zai yiwu ya kara yin zaman jinyarta na shekara da shekaru ba, dan wa ya san wace jaraba ce ta janyowa kanta kuma?, ko ya je ya samo mace ko ni in samo masa ne, da N
ni take zancen.......aikin banza aikin wofi"

Du irin yadda Anna ke cikin mutuwar jiki da tunani sai da ta gyara zama tana ba Mama hakuri haka kuma lokaci daya tana tuna a da kafin mama ta shiga wannan halin fa har tsoronta Mazna take yi kamar me, saboda haka kawai Maman tace ita sam bata son yarinyar nan dake zuwa wajen sa da nufin zumunci, ba ajinsu daya ba, ba shekarunsu daya ba, ita ba namiji ba, gaskiya a daina......, to da ya tafiyarsa Saudiya abin ya lafa, da kuma maganar aure ta tashi aka ji ita ya gabatar Maman cewa ta yi ta rantse ta tabbata yarinyar nan dama abinda take so kenan, ita bata son mutun marar kamun kai, sai da Anna ta hana ne har maganar ta yi karko, kuma tana da tsohon cikin nan sam basa shan inuwa daya ita da ita, bayan ta haihu ta fada halin nan kuma a cikin yanayin nan ma idan daya ta zo waje daya tashi take ta bar wajen, bata san ya aka yi sam basa shan inuwa daya baKisan mummuke page 74_ 75

Haka dai mama ta sha fadanta, hadi da yiwa Anna tambayoyi, ama ko kadan Anna bata sanar mata maganar NUR ba, dan ta san wace mama a kan lamarin IMAD, du take so a barshi da kansa ya sanar da abinda ke ransa Mama ba zata iya yin hakuri ba, ita da kanta zata je ta nema masa auren kuma ta ki yarda ya sha wahala , ta san halinta ne, shi yasa ma ta kiyaye wannan da kuma wasu abubuwan da ba anfani fadin su, daga karshe ta sa sai ta tashi sun je duba MAZNA, ama wannan karron mama sai ta wuce kicin da sauri tana fadin" Anna ai ba za'a bar falon haka ba, ba'a san fitowarsa ba, bari in je in masa girki da kaina mu gani ta yiwu zuwa sallar la'asar ya sauko"

Murmushi kawai Anna ta yi ta fice ta nufi bangaren nasu

A lokacin da ta je, autarsu kadai ta samu a falon a zaune tana kallon TV

Gannin Anna ya sa ta yi murna kwarai, saboda a rayuwa Anna bata taɓa hantararta ko korarta ba, da fara'a ta ce" Anna, ke ma kin zo ganninta ko? Koro Ni suka yi suka ce ko wa ya zo kar in saki in bari a san tana nan, aunty taba ta kuka tana ta kuka, kuma nan dinta ya lotsa, ama sun yi kiran likitanta wai yace maza maza ta tafi, Ni dai ban san abinda yake faruwa ba sai kuka take tana cewa itace ajalin yarinyar nan, Anna wace yarinya ne shin?"

Anna dake kallon auta bata iya bata amsa ba, sai kawar da maganar ta yi ta ce" Ki ce Ni ce na zo"

Gaba ta yi tana dan gudu ta haura sama, ta bar Anna na kallon kada hadi da afkawa dogon tunani

Bata jima sosai ba sai ga JAUHARA na saukowa , da dan sauri ta karaso tana duban Anna a tausashe ta ce" Anna sannu da hutawa, ki taso mu je ciki auntyn ba zata iya saukowa yanzu bane" ta fadi haka dan ta san da wahala ita kam ta iya cema Anna ta tafi ba zata iya saukowa ba, bayan abinda MAZNA tace kenan

Anna da kula ta ce" Subahanalah, jikin nata ne?, JAUHARA ko asibiti zaku kamo ta mu je ne?"

A hankali JAUHARA ta sauke ajiyar zuciya a raunane ta ce" Anna, ai abin nan da ta yi ne , na bayan ne ya juye , kuma likita yace zai taso da kansa ama sai ta jima a kwance sannan zai daga, to shine , sai kuma kukan da take yi kan ran yaya a bace tana so ya yi hakuri.........., dan Allah Anna ki yi hakuri, ki yafe mata, wallahi aunty ka wasu abubuwan du dan gudun bata maki ko batawa yaya ne, bata san hakan zai sa ta bata din ba......, dan Allah Anna kar ki bari yaya ya daki aunty, saboda Ni na san da wahala ta rayu in ba shi"

Anna dake kallon JAUHARA a hankali ta furta" JAUHARA"

Jauhara ta dago tana kallon Anna idannuwanta cike da hawaye

A tausashe Anna ta ce" Ba zai sake ta ba, in sha Allah, kuma ki fada mata ta sassautawa kanta da kanta, saboda saka damuwar a rai sosai bata da wani anfani..........."

JAUHARA ta gyada kai tana dauke ajiyar zuciya hadi da goge idannuwanta

Anna ta mike tana jan mayafinta da kyau, har zata juya ta dakata ta kara duban JAUHARA tana jin tausayin yarinyar na ratsa zuciyarta..............

A gaskiya zata iya cewa mai halin MAZNA kai tsaye namijin ne, domin ko JAUHARA kwarai tana girmamata a rayuwa, dan da wahala JAUHARA bata leka ta ba kullum ta Allah in dai suna cikin gidan nan,

Murmushi ta yi mata a tausashe ta ce" ki yi iya yin ki, ki rarasheta, sannan ki nuna mata girman abinda ta yi, zan so ta gane girman laifin da ta yi wanda ke iya hana mata zaman lafiya da mijinta, JAUHARA ki fada mata a yanzu ba lokacin ta yi ta abubuwa kamar marar kamun kai bace, ba lokacin ta zubawa wata laifinta bane, lokaci ne da zata gane laifinta ta sada kai ta yi hakuri ta jure duk wani hukunci da zai mata har su daidaita, lokaci ne da ya dace ace ko me take ji ta mayar gefe ta fuskance shi....., JAUHARA ki fada mata cewar idan AKOY abinda zai kara gigita zuciyar musulmi mai kishin iyalinsa shi ne tunanin wani namijin ya ga abinda yake hankalinsa, ke ba yarinya karama bace, idan ban fido maki komai dala dala Bama na san zaki fahimci girman yadda yayanku ya tsani fitowarta ba nikaf, bale har a kai cen, abu ne an yi, sai a yi kokari a gyara kin fahimta"

Kai JAUHARA ke gyadawa a ranta tana ayyana' Anna, da kin san abinda nake kwasa da ita , da kin gane idan da tana daukan maganata da bata kai wannan halin da take ciki ba a yanzu......, Anna da ace kin san irin yadda nake fama ba dare ba rana kan daidaituwar wasu halaya nata, da kin Sara kuma kin fahimci aunty soyayar kawai ta iya, daga wannan babu wani abu da zata yi dan kiyaye zubewar soyayyar ko kara mata kwalliya....., sai hakuri ai lamarin'

Haka Anna ta tafi, ita kuma ta koma saman ta zauna tana ci gaba da sauraron fada, kuka zage zagen auntynta, ba tare da ta katse ta, ko ta bar wajen ba, domin shi ma ƴaƴanta yana nan, sai idan yinwa ta ishe su suke neman wani dan abin su taba....., kuma cikin ikon Allah har dare ya tsala bai shigo ba, du yadda take jiran shigowarsa har karfe dayan dare ta yi a dole ta koma ta kwanta tana ji kamar duniyarta ta gama karewa, kiyamarta ta gama tsayawa.............., komai na kara fita daga ranta, tsoro na maye gurbi, yana ina ne? Me yake yi ne?, wani hali yake ciki ne? Basu taba samun sabani ya bar mata ɓangaren nan ba sai yanzu, ko dai ya gama zama da ita ne??????

A bangaren su Mutalab su ma haka suka yi ta kai kawo bangaren Anna, sai dai amsar daya ce bai sauko ba, kuma Anna ta hana kowa tarda shi, hatta uncle sai da ya shigo dan yana ta tambayar a wani hali yake? An kasa bashi gamsashiyar amsa, sai dai ko shi da ya je, bai samu ganin nasa ba, haka ma Malan yakan leko ya koma, ya fi a irga, uwa uba Aliyu dake fushi kamar shi ne aka yiwa laifin, a karshe dai a dole kowa ya tafi bangarensa aka bar Mama da Anna, wace ita ma ta rarasheta ta da ta tafin saboda ba yadda za'a yi ta bari ta kwana a nan bayan Malan na nan, a dole ta tafi , ita ma ta je nata dakin ta hau nafila zuciyarta a cinkushe , cike da tunanin shin komai ba zai fito ya ci ba?, a ciki yake Sallah? Ya Allah.

Washe gari tunda duku duku ta gama yi masa girki, tana zaune tana tunanin yanzu kam tarda shi zata yi ta yi masa wankin baban bargo, ta da ya sauko ya mike ya ci gaba da harkokin rayuwarsa ne Mama ta shigo da Malan suka gaisa , suna tambayar an ji motsinsa kuwa?, Anna ta girgiza kai tana sada kai hadi da boye yan kwalar da suka tarun mata a ido......., haka ma AUNTYn yara ta shigo dan ta gaishe da Anna, kuma Aban yara na baya yana gaisawa da du Wanda ya hadu da shi ne da kyau da kyau shi yasa ta yi gaba ......., nan ta samu kowa a yanayin ba dadi a dole ta zauna dan bata ma san abinda yake faruwa ba............

Ba'a kuma daukan lokaci ba baki suka shigo gaba dayansu , tare da Aban yara dake dariyar firar da Mutalab ke kokarin yi masa, shi a dole shi ya jima a kasa ya fara iya Hausa, ya zamo ya hade da Hausar da Larabci yana kara gaishe da Aban yara, wanda hakan ya saka shi jin nishadi a ransa yana duban samarin da mamakin wai yaya aka yi du basu da girman kai ne?????

Su ma sun samu baban falon cike, hakan ya sa du aka shiga gaisawa, Uncle da kula ya dubi Anna ya ce" Madame, yaya yarona ne? Bai fito ba? Har yanzu komai bai ci ba?, ya dace a fito min da shi yau fa"
Chapter 117 · 0% Book details