← Book details Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 141

Sashe 70

Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

FARHANA kam ganin abin ya fara fin karfinta ta sadado ta kama hannun Nur ta ja ta dakinta ta rufo kofar da sauri ta kai ta bakin bed din ta ta zaunar da ita kafin ta dawo da sauri ta duka ta wajen yar karamar kofar nan tana lekawa............ A kan idannuwanta Ƴaƴanta ya nunawa MAZNA hannu yayi wata magana a mugun kausashe kafin ya kama hannun Mama ya koma elevator da ita.........

Wani irin ihu MAZNA ta saka ta nufo dakin Farhana ta kama duka kamar zata bale hananyenta tana kuka tana fadin" FARHANA ki bude min in ga ubanda ya tsayawa yarinyar nan, Farhana ki bude min kar zuciyata ta buga, Farhana......"

FARHANA ta zarro ido ta mike ta juyo dan ta cewa Nur ta zauna ba zata bude ba ta ga Nur din daf da ita a tsaye, har sai da goshin su ya hade wajen yin gare

Goshi ta dafe tana furta" AUSHHHHH, ke meye haka? Ina zaki je kuma????"

Nur ta langwabar da kanta, a hankali ta kama hannun FARHANA ta dora a kirjinta ta ce" Taba kirjina ki ji, mutuwa zan yi FARHANA taba ki ji???"

FARHANA ta tabe baki tana dubanta ta ce" Zo zauna tukunan, ai ba zaki mutu yanzu ba, da wahala ki mutu yanzu, ke ki gama tashin bom din ki mutu ki bar uban wa da rigimar???, innalilahi Y'ayana kika runguma? Rungume shi kika yi??????, La'ila ha ilalahu a gaban MAZNA, MAZNA ta gan ki, ke kam gwara ma ki mutu, dan ina mai tabbatar maki in baki mutu salin alin ba MAZNA ce zata kashe ki, kin rungume mata miji, kin rungume ustazu kin cire masa mutunci ....., kandalar Anna dama ina ganin ki na gane yar balaki ce ke......, zo zauna"

Ta mayar da ita bakin gadon ta zaunar da ita, ta je wajen frij dinta ta ciro ruwa a botl ta dawo, bata yi wata wata ba ta makawa Nur shi a fuskarta har zuwa jikinta, hakan ya sa Nur sauke wata irin ajiyar zuciya mai karfin tsiya kafin ta mike tsaye tana zarro ido da karfi ta ce" Innalilahi, ke kin jika Ni, ruwan sanyi ne......Farhana kin jika ni !"

Farhana ta gyada kai tana murmushi ta koma ta dauko madara , wato yogourt ta dawo ta bude ta mika mata tana ganin yadda ta cire hijabin nan domin yayi jargaf ta ajiye shi a nan, daga ita sai rigar nan tana zarro ido Farhana ta miko mata abin nan ta ce" Sha dai ina zuwa sha"

Amsa ta yi ta kafa kai domin ta gane yogourt ce, cikin ikon Allah sai da ta shanye ta tasssssssss sannan kuma ta dubi Farhanan dake miko mata shayi irin na buzaye da ta dafa tun da safe ta cika botle din ta dan tafiya makaranta, to basu tafi ba ta dai ajiye shi, budewa kawai ta yi ta zuba wa Nur din ta mika mata, ta kuwa amsa ta sake zaunawa tana sha a hankali jikinta na saki, a hankali gajiya da ciwon kan da take ji suna barinta, a hankali hankalinta na dan dawowa jikinta, sai tashin hankalin da ya rage mata kawai a cikin zuciyarta.........

Kai ta daga a hankali tana bin dakin na NUR.....

Daki tamkar na y'ar saraki masu kuɗi ba sarautar wahala ba? Daki kamar na tatsuniya? Daki kamar ba a duniya ba?????

Mikewa ta yi da sauri tana duban Farhana da duba kamar na tsoro tsoro kamar na son ganewa

Kasa kasa ta ce" Farhana, ina ne nan din?????"

FARHANA ta bi wajen da kallo, kafin ta sake dubanta, kwarai damuwa na iya saka maye idan ta hadu da yinwa wannan haka yake......

A harhade ta ce" Dakina ne,, ke kin kuwa san abinda kika aikata? Yaya kika rukunkume kuma a gaban matarsa!"

Turus ta yi tana kallon ta, da sauri ta ce" Allah tsinewa mai karya???"

Farhana ta zabga nata harara ta ce" Ni yanzu ai ko me kika ce ba zan kula ki ba kuma, ke kam ai kin fi karfina, bosss kike sak na rantse da Allah....., Ni yanzu yadda zan yi in hada ido da shi ne damuwata, wannan abin kunya da me yayi kama, kin kama kin za bar masa da musuluncinsa a idannuwana!"

A hankali komai ke dawowa idannuwan NUR, a firgice ta saka ihu ta yi kan FARHANA tana boye fuskarta tana fadin " Innalilahi wa Inna ilaihi raj'une, Farhana na shiga uku, wallahi jikinsa na shiga, Farhana jikinsa na shiga na zata zane Ni ne zai yi, Farhana na shiga uku wannan matarsa ce? Ki bude itace ke kuka wai? FARHANA ki bude in fada mata Ni wallahi ba abinda ya haɗa Ni da mijinta, ta taimaka min ma dan Allah ta samo min yadda za'a yi ya yafewa mama, mama fa cikin fushi ne take, ba halinta bane, mama da kika gani tana da saurin yin fushi Ama kuma a kanmu tana da hakuri, kawai ita Auntynmu ce bata so, Ama idan kika cire wannan du da sauki , dan Allah bude min in fada mata Ni din banza , ina Ni ina mijinta, dan Allah ta bashi hakuri ya yafewa Mama, kin ji????"

FARHANA ta yi dariya tana girgiza kai ta gyara zama ta ce" Ta tabbata so kike ki sakani a masifa, ke ina Ni ina matarsa da har zan maki rakiya? Bama wannan ba, wai dama mahaifiyarki ce ta sace y'ar gidan mama? Ke mama fa haukacewa ta yi saboda sace Mata y'ar nan da aka yi, gaskiya ki yi hakuri with all due respect mahaifiyarki azaluma ce!"

NUR ta juyo tana duban ta, yanzun kam muryarta ta raunana sosai ta ce" Baki gane ba, ita Mama bata taɓa haihuwa ba a bayanin da suka yi na gane, shi ne dalilin da ya sa ta dauki A'isha, ba fa satar ta ta yi ba, kuma ta kula da ita sosai ko??"

FARHANA ta Dube ta ta ce" To Ni ai du kin gigitani, kin ce mahaifiyarki ce, kuma kin ce bata taɓa haihuwa ba, hala ke ma sato ki ta yi????"

Nur ta girgiza kai ta zauna da kyau tana nunawa Farhana ta ce" A'a, kin ga Ni da yaya SULaimana Auntynmu ce ta haife mi, A'isha ce kawai mama ta ara, ba sata ta yi ba"

FARHANA ta zuba mata ido na dan lokaci kafin ta ce" Wai auntyn nan da kike fada cewar ita kadai ce Maman naki ta tsana dama itace mahaifiyarki?"

Nur ta gyada mata kai a sanyaye

FARHANA ta gyada kai tana sake duban Nur ta ce" Dukan abinda zai kara tabbatar min baki da hankali sai kara bayyana yake yi, Allah sarki kandalar Anna, to wai tsaya ke in ba mahaukaciya ba kin san cewa matar nan ta tsani mahaifiyarki ama kike cewa kawai? Tsanar mahaifiyar taki ce kawai? To Ni du ubanda ya tsani Anna ai kashe shi ya zame min shahada yarinya sai dai in mun je cen a yi abinda ya dace da Ni kawai....., Ama ina ke ina cewa a yafewa wace ta tsani mamanki? Ko dai asiri ta maki ne kandalar Anna ???"

Nur ta sakar mata harara ta mike tana jan tsaki ta je inda ta ga kaya a rarataye ta shiga dubawa, kawai ta janyo abaya ta dora saman rigarta , ta dauki hijab karami ta zurma bata ce da ita ci kanki ba ta nufi dakin nan

FARHANA da ta mike tana fadin" Ke kin ga zo cire min rigar nan, du cikin kayana ita na fi kauna saboda kyautar Bos din Anna ne, zo cire min ki saka wannan, kuma wallahi idan kika fita matar shi na iya kashe ki, bata da hankali fa a kan wannan kurman mijin nata ina gaya maki!"

Nur ta daga murya ta ce" Na ki in cire din, kuma ta kashe ni in gani idan ita ta busa min rai aikin banza ki zo ki gwada min hanya kar aje ana cen za'a rufe harda Auntynmu, dan na kula ya'yan nan naki sam bashi da imani!"

Ta karashe yana bude kofar dakin

Da gudu FARHANA ta taho saboda irin yadda ta ga MAZNA da Fu'ad da Jauhara da autar su sunna rike da ita tana kuka risris tana faman fadin a barta yau ko ita ko NUR.....Ama suna kokarin ganin sun tafi da ita sai ga Nur din ta bude

Kafin Farhana ta karaso ta rufe tuni MAZNA ta yi sufa ta janyo Nur tana dauke ta da marin ba zata....

Ihu nur ta saka ta damki wuyan MAZNA itama ta dauke ta da mari ta hagu da dama kafin ta nemi matseta a jikin garu......

Da gudu Fu'ad ya karasa da nufin janye nur, sai dai Farhana ta hana ta hanyar ture shi da sauri ta nemi shiga tsakaninsu

Jauhara ce ta cire takalmin ta ta ce" Dan ubanku dukanta zaku yi? Bari ku gani....."

Ai kuwa da sauri Farhana ke jan NUR, ama MAZNA ta rike mata karamin hijabin nan, ta yi ta yi ta saki ta ki saki tana ihu tana rike da shi, sai kawai ta saka hakoranta ta gala mata cizon da ya sa ta saki hijabin tana ihu tana murzawa hadi da fadin" Ta cije Ni, maya ce, ta cije Ni......"

Da gudu FARHANA ta dana elevator ya bude ta ja Nur suka fada ta dana ya rufe yayi kasa da su........su duka suna haki, dan Nur a yanzu ne ta ji wani zuuuuuuuuu abin nan yayi da su wajen saukowar dan haka ta duke tana zarro ido ta ce" Farhana zan zubo da ya'yan hanjina.........."
Chapter 70 · 0% Book details