Sashe 66
Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da sauri ta juya ta duka ta dauka zata mayar jikin nata Anna dake kallon su da son cewa dama cewa aka yi shi mala'ikan mutuwar yanka mutun ne yake yi? Ta yi tsittt saboda kwasar diban albarkan da suka yiwa hijabin da kuma yadda ta duka ta dau abinta sai ta samu kanta da sauron duban inda IMAD yake da bakinsa ita ma, sai ta ga bakin yake kallo da Aban yara wanda ya dafe gaban goshinsa, da kuma Malan na Magarya da ya saki baki yana duban HALLAH, domin su kam basu da yinwa bale ƙishirwa, saboda an basu abinci harda shayin Bugaje , da Aban yara ya so kar su ci ma, shi ne ya nuna masa ko kabari zaka shiga idan ka san lokacin ai gwara ka je da guzuri bale rikicin duniya, yayi hakuri kawai ya ci abinci koda shayin ne ya sha, ai kuwa ya dan taba shayin ama shi kam ya ci abinci sosai da sosai kafin a fara tashin tashina ne ya ce" Auta? Gidan ku, dama kin san nan kenan???"
Innalilahi, su suke ta rigar da ta wuce gwuiwa da kadan......, mai shafuwar azara'ilu hijabin a hannunta ta yi wajen su aban ta tana kwalalo ido ta karasa ta mika hannu ta dafe haba ta rike hijabin a wajen kugunta ta ce" La'ila ha ilalahu, sulaimana yace kuna garkame, Aban Magarya ashe kana gidan mu????"
Yanzun kam kafaffuwanta da take ta hardewa kamar mai jin fitsari , masu haske tasss da cika irin ta mutun mai dan jiki haka ya zubawa ido kafin ya dan daga dubanta dan ya ga wai fitsari take ji ne ya sa take wannan abin ko menene? Sai dai abinda shedan ke ta buri ne ya nemi samun idannuwansa a lokacin da ya sauke dubansa a kan iya tsayin da rigar ta tsaya da kuma yadda take ɗan sake dagewa daga jikin nata , sai dai duda haka ba wai zuwa ta yi har wajen cinyoyinta ba, no, kawai dai ta matukar fitar da surar ta ne .......
Mikewa yayi a hankali dan ya koma wata kujerar saboda kusan a gabansa take tsaye, sai dai a lokacin da ya mike din, ita kuwa ta yi dan taku biyu ta baya dan a lokacin ne tace ai bari kawai ta sanyo su auntynsu dan su daina kuka da damuwa domin ga abansu nan kalau cikin hayacinsa, sai kawai ta ɗan bige gefen hannunsa na hagu da bayan ta..............., hakan ya sa da sauri ya janye hannun nasa yana jimke shi......ya koma saman kujerar da ya so mikewa gaba daya dan barin wajen ya zauna din yana kai hannunsa wajen gaban goshinsa, dayan hannun kuwa ya jimke shi da yanayin da ba wanda ya gane na tarin bakin ciki ne ko jin haushi............kai Subahanalah!??
Da dan razana Farhana ta zarro idanu ta ɗora hannunta a kai ta yi baya baya kafin ta ce" La'ila ha ilalahu, to ai shiKenan bari Ni in koma , dama tsautsayi ya fito da Ni innalilahi yarinyar nan sai ta ja min masifa......"
Aban yara ne ya janyo hannunta da dan karfi yana sakar mata harara dan ya dawo da ita hayacinta........fuska a hade ya ce" Saka hijabin mana, kuma bakya ganin manya ne da baki gaishe da kowa ba????!"
Da sauri ta dubi hijabin, lokaci daya ta saka tana dan sakin murmushi domin baba na Magarya cewa ya yi" Yi mata a hankali mana, auta jaja manya, baka ganin kamar a firgice take, bata a hayacinta mana, na san basu kwonta ba jiya, kin ga bari Elhaji ya bada dama a sanyo auntyn naku kin ji? Ku daina kukan haka mu a cikin aminci muke kuma asirin uwarki munafuka kam ya tonu kin ga uban A'isha nan"
Jiki a sanyaye ta dubi Aban Magarya, ta yi dan raurau da ido, kafin ta dubi wanda aka nuna din.......mutun a Hakimce cikin shiga ta manyan sutura kamar wani gwamna sai kanshi yake yi.........., ta dubi mahaifinsu ta ga shi ma nasa jikin ya kara yin sanyi kalau..... Ta turo baki ta ce" Baba na Magarya, ai A'isha bata da baba sama da Aban yara , ko sabon baba?????"
Malan mijin mama zuwai yayi dariya yana dubanta ya ce" Kwarai kuwa yata wannan haka yake"
Ajiyar zuciya ta sauke tana murmushi ta sake kallon Malan mijin mama dake murmushi shi ma ta ɗan rage tsayi ta ce" Ina kwana baba???"
Amsata ya yi da kula sosai yana murmushin nan........cike da gannin yarinyarta a bayyane
Sai kuma ta juya dan a yanzu ta ga kaffafuwan mutun , duda a cikin Safa ne ta juyo sai ta ga ya dafe gaban goshinsa yana dan murzawa........., kamar farin mutun ne tassssss, ama kuma ya sirka da ja saboda wannan kam ja ne, ko ya aka yi ya dauki ja haka fatarsa? Dama akoy kan mutun? Gaskiya ba fari bane tassssssssss.............., a hankali ta dubi Anna da ta mata alamun ta zo ta gyada kai ta ɗan sake dubansa sai kawai ta karasa wajen Anna kasa kasa sosai Anna ta ce" Baki gaishe da yayanku ba fa"
Da sauri ta juya inda Anna din ta nuna........
Kai, wai dama shi ne?
To ya aka yi yau ta ga ya zama ja bayan jiya jiyan nan fari ne tasssssssssssssss?
A hankali ta lumshe idannuwanta tana neman nutsuwa, gaba daya jiya zuwa yau idan aka ce ta samu tabuwar hankali ma ba zata yi mamaki ba domin ba abinda bata ji na émotion ba........
To ga dayan ai, sam fa bata ga bawan Allahn nan ba, ashe shi ne a zaunen nan yana murza gaban
goshi??????
Sai kuma ta ɗan dubi Anna saboda wani tunani da ta yi......
Wajen da yake zaune ai yanzu ta fito daga nan, kuma a lokacin da ta je rigar nan dake jikinta ne kawai a jikinta ba hijab din.........
Tsoro da kunya suka sa ta sake duban Anna, kasa kasa sosai ta ce" Anna, yanzu ya shigo ne? Ko ya jima a nan????" Dan kuwa amsar da Anna zata bata na tafe da nutsuwar da take iya samu harma ta iya gaishe shi ko akasin haka.......
Anna ta dube ta da murmushi a fuskarta domin sarai ta gane sai yanzu ta dawo hayacinta......., gashi sun ci gaba da bayanin nan , Aban yara na fayyace masa komai da komai, Malan mijin mama na gyada kai, Malan na Magarya na kara zuba jus yana kurba yana dan murmushi , shi kuma tunda ta bar gaban nasa sai ya dan daga idannuwansa ya bi iyayen nata da kallo cike da jin nauyin su, ya sake duban hannun nan nasa ya girgiza kai yana jimke hannun hadi da samun tabatuwar kwarai mahaukaciyar jiya ce, to a jiyan ma ai daga ita sai sket da riga take yawo a gaban maza bale yau kuma, wannan ta yiwu fa in zata makarantar da kyar ake saka mata hijab..... Allah sarki
Idannuwansa ya lumshe kafin ya cije lebensa na kasa kadan...... ya gyara zamansa da kyau ya dan kai hannun nasa kusan sajensa ya dan shafa a hankali hadi da yin sama da hannun wajen girarsa kafin ya basu hankalinsa gaba daya yana sauraron su har Aban yara ya dasa Aya, da kula ya ce"Page 39 and 40
A nutse bayan ya gyara zamansa ya bi su Aban yara da kallo irin na tsanaki......, kallo irin na ya kara gaskata maganganun sa,
A gaskiya a yanayin Aban yara sam bai ji zuciyarsa ta nuna masa rashin yarda da kalamansa ba, sai dai dan Adam na yanzu ba kowa bane mai gaskiya, masu rashin gaskiyar da suka iya kalamai sun fi yawa a cikin al'umma fiye da masu gaskiyar
A nutse ya ce" Dama idan mace ta haihu, ana iya rayuwa da ita ba tare da an gane ba? Idan har ta yi boyon ciki na tsayin shekara guda cirrrrrrrrrr bata samu sa'ar satar d'an wani ba, yaya bayan haihuwar ta idan har jinin haihuwar ya dauke a kwakwaluwarka kai mijinta....., a lokacin da ka gama zuwa dakinta baka samu tunanin cewa anya matar nan ce ta haihu ba?????"
Ido malan na Magarya ya zubawa wannan bawan Allah, a hankali zuciyarsa ta fara hasko masa anya ba cikin ruwan sanyi ne za'a hade su a maka su a gidan yari ba kuwa?, saboda nutsuwar mutumen da tambayar da yayi bayan dogon bayanin nan sun tabbatar masa ba lalle dan kawai an ga yarinyar nan ya yafe bacin ran da aka saka shi ba, to ai a yadda ma sam ya ki a kirawo mahaifiyar yarinyar sannan ya ki sam a yi a shigo masa da yarinyar sun isa shedar ba gagawa yake ba, ko ina za'a taka kuma ya fi su karfin takalmin zuwa.........
Da sauri ya kalli Aban yara da ya gyara zama zai yi bayanin wannan a tausashe ya ce" AHMADU, bayanan nan fa zan so a yi su gaban shedu!"
Aban yara ya zuba masa ido, saboda da hannunsa dake cikin rigarsa ya mintsine shi, haka kuma yayi magana a tausashe ama fuskarsa dauke da yannayi ne na tashin hankali
A hankali ya kai dubansa kan fuskar IMAD
kwarai ya tsinci yannayi na bacin rai a kan fuskar bawan Allahn nan mai tsananin gaske, domin harta idannuwansa sun yi ja , haka kuma yanayin fuskar tasa ta dauki daurewa mai karfin gaske.......
"Anna, su Auntynmu fa, a wajen da suke tare ne suke da polisawa tamkar sun yi wani laifi ne, dan Allah ki sa a shigo da su Anna" Nur ta fada a hankali tana rike hannun na Anna
Anna ta dubi fuskarta, a hankali ta sauke ajiyar zuciya cike da jin wani yannayi kala biyu a irin wannan lokacin.....
Abinda ya zaunar da ita tun Dazu dan ta tabbata yaronta bai dauki mummunan matakin da zai iya janyowa kansa hukunci a wajen Allah bane, domin kuwa ita aka fara fadawa bayanan nan kafin ta je ta kirawo shi a bangaren sa yau din nan tunda safe..........