Sashe 89
Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
MAZNA da ita ma abinda ya sa ta yi dan tsai kenan ta dubeta ta ce" dazu fa ya fita ai, ya zo ya ga jikina lafiya kalau ya fita, bari in leko shi"
Mikewa ta yi ta nufi bangaren nasa ta bude har dakin da yake shiryawa ta ga bayi a rufe ruf hakan ya sa ta zauna tana jiran fitowarsa, ita kuwa JAUHARA ta yi zamanta bata wani tashi ba.
Ya jima kafin ya fito yana goge sauran ruwan da bai goge ba a jikinsa ya nufi inda kayansa suke a nutse ya ciro wani lalausan yadi mai kahirin shiga zuciya a kallo daya idan ka masa, mai ruwan baki sidik , da hular da zata tafi da shi ya ajiye ya fara bin jikinsa da turare sosai sannan ya shiga sakawa ba tare da ya kula inda take Bama bale har ya nuna ya san da wanzuwar ta a wajen
Hakan ya sa ta gane eh ransa a bace ne, dan haka ta shiga kokarin ganin ya kula ta, da tarin tambayoyin wani ya bata masa rai ne? Har ya gama shiryawa yayi mugun kyan da ya sa ta zuba masa ido a raunane ta ce" Akul, me yasa yanzu ka cika fushi da Ni ne? Me yasa yanzu kake fushi to? Me na yi?"
Zuba mata ido yayi, duba na yan lokaci kafin ya juya ya fita
Da sauri ta bi bayansa tana kiran sunansa har suka fito falo, hakan ya sa ya dakata ya juya yana kallon ta saboda ganin Jauhara na falon har ma ta juyo tana dubansu, bayan a cikin abubuwan da ya fada mata ko da wasa su kiyaye harda yin maganar da ta shafe su a gaban kowani bakon halittar da ba su ba, ko waye!
A hankali ta ce" Me na yi maka nake son sani dan Allah"
Agogon da ya daura a hannunsa ya gyara saboda bai dauru da kyau ba, a hankali ya furta" ba abinda kika min"
Daga haka ya juya ya fice a falon gaba daya
Jiki tamkar kwai ya fashewa kaza ta koma ta zauna tana hada tagumi hannu bibbiyu ta ce" Du idan ya yi irin wunin nan da mahaifiyarsa sai ya shigo min a birkice, Allah ya rabani zama da matar nan!"
Jauhara ta Dube ta, kafin ta dage kafadu, domin ta gaji da fadawa auntynta gaskiya tana takewa........, ta yi abinda ta ga dama, ita gabanan ba abinda zata ce mata Walahi!
A duniya tana mamakin soyayyar da auntynta ke yiwa mijinta, soyayyar da sam bata son mahaifiyarsa, in ba rashin tsoron Allah ba yanzu AUNTY ce zata ce wai Anna na hadata da mijinta? Anna fa? Hum ta dai ci gaba da yin abinda take yi, wata rana sai labari.
_______________________________
Tunda suka shanyo kwanar gidan su Jafaru Farhana ta zubawa bangaren gidansu ido da mamakin taron da aka yi, alamu ya nuna kauyawa party ake yi, wanda hakan ya sa ta sake zuba ido kida na tashi sama sama ga DG a tsaye da lasifika yana gabatar da nasa aikin dake karawa lamarin kaimi
Motar ya tsayar , hakan ya sa suka fito su ukun sunna kallon yadda yan mata ke rawa irin ta gada, abin ban sha'awa du sun sha ankon zani daban da riga mai dauke da hoton amarya da ango wanda FARHANA ta kurawa hotunan jikin rigunansu ido gabanta na faduwa da karfin gaske...........
Abinda ya sa ake ganin filin ƙarara saboda irin yadda masu kidan suka gyara wajen an bar gaban a bude ne sai kujeru da suka zagaye wajen , mutane na daga ɓangaren kofar gidan su JAFARUN ya zamo sosai ake ganin filin da kyau da kyau
Dg ne ya daga murya yana fadin" Wannan biki na yan gata, biki na dan gata ne, isashe ne wanda ake so, in ba karfin soyayya ba yaya za'a yi a wannan zamanin ka aure kawaye biyu, ku tafawa ango dan Allah, ango mai capacity ya shigo fili da amaransa su cashe, kar a manta idan aka shigo filin nan dan a yi liki ne kawai, capacity capacity..... capacity capacity Yauwa....."
Hannun HALLAH Farhana ta damko da karfi a lokacin da angon ya fara shigowa yana bin kidan capacity din nan yana rawa hadi da daga Babar rigar da ya saka shi da abokansa anko yana rawa hadi da juyi ana ziga shi ana masa kidan capacity capacity.....amaren kuwa su ma kawayensu suka musu rakiya aka bar su a filin angon na casu suma suna yi kowace na son nuna itace ai asalin capacityn
Muryarta na rawa ta ce" Nur, Jafar ne nake gani ?....."
Nur na son kallon inda ta nuna din, kawai FARHANA ta janye kujerar dake gabanta ta shiga ta nufin inda ango ke juyi yana kwaso shoki ana tafa masa.........
Da sauri Nur ta bi bayanta , haka ma A'isha dake waige waige dan bata gane komai ba, su ai ba saninsa suka yi ba bale su iya sheda shi......
ANAS da mamaki ya sa ya fito daga motar ransa bace da nufin kiran su su taho su yi tafiyarsu ne, yana fitowar zai taka ya karasa tafkekiyar motar nan ta parke a Daf da shi, a irin pakawar da tsayuwarta ta gama matse masa wajen da ko shi aljani ne ba zai iya bacewa ba...........
A haukace ya dafe kirjinsa, jikinsa ya dauki rawa a lokacin da idannuwansa suka sauka a cikin na Ogansa , ya masa kallo daya kafin ya mayar da idannuwansa inda yake hange a lokacin da DG ya dakatar da kidan yana fadin" To fah, me yake faruwa angonmu mai capacity jikinsa ke rawa? Ango me ka gani haka ne ? Ga wata tsaleliyar budurwa mai suna capacity a kusa da wannan balarabar......, kar dai ku ma kuna cikin soyayyar angon nan??????"
FARHANA dake dubansa cikin ido a lokacin da ya furta " Bab" ne ta sada kanta wasu irin hawaye suka bale mata ta sake bin yan matan nan da kallo , ta gane yarinyar da yake ce mata kanwarsa ce, wace idan suka zo daukan sako take fitowa ta yi ta hararanta ta dake dubansa lokacin da ya miko hannu zai kama mata hannu ta daga hannun ta cire shi da mari rai bace ta ce" Idan ka yarda ka taba min hannu sai na batar da kai a kasar nan Jafar!"
Budurwar nan da du ta fi dayar rawar kai ta zaburo zata mari FARHANA, Nur ta rike hannunta da karfi ta watsar da shi ta duka ta cire takalmin nata mai tsini ta juya inda ango da abokansa suke rike shi suna tausarsa ta ce" Dan iska mayaudari, bari ka gani sai dai a maka auren da ido daya yau"
Da sauri Aliyu ya juya da nufin neman izinin zuwa ya taho da su, sai dai yana juyawar ya ga ya bude ya fita daga motar, a lokacin da daya daga cikin abokan angon nan yayi raf da takalmin daya na Nur yake kokarin yi mata zobe dan ya kwace takalmin ya tatakata a wajen domin ya gane yar geto ce a daku ba zai ce mata komai ba, ya karaso da saurin da shi da kansa bai san yana da shi ba!
Yana zuwa dayan takalmin da ta wawuro na A'isha bayan tace mata" Indo ba zaki bani takalmin naki ba,? Dan iska ya fasa Ni da kai, sake min takalmina....."
Tana dagowa ta ji an kama hannun nata daya, mai dayan takalmin an masa matsar da ya sa ta sake shi, dayan da ta duka ta dauka kuwa an yiwa hannun irin dokewar nan dake sakawa a saki abu ba'a shirya ba, sannan aka hade hannayen nata biyu a waje daya aka yi musu curewar da ta sa bayan tsoratan da ta yi itama na ganin wanda ke yi mata wannan aikin, har azabar hakan ya sa ta duke tana fasa ihu bayan ihun da Farhanan ta saka , A'isha kuwa ta zangaya a guje ta nufi motar da suka zo da ita ta shige baya ta boye kanta jikin ta na rawa........
Tisa keyar Farhana Aliyu yayi, wajen kuwa tunda suka ga iko suka shiga watsewa, ciki harda angon da ya gudu a lokacin da ya ga Sir IMAD a filin nan, jikinsa na rawa kamar zai suma.........
A duke take, jikinta na rawa, gaba daya tana neman fita a hayacinta saboda bata taɓa ganin fuskarsa na huci irin haka ba sai yau..........
Aliyu da ya kai Farhana mota ne ya juyo dan tisa keyar wannan jarabawar ta ogansa, a lokaci daya ya ja ya tsaya yana zarro ido sakamon abinda idnanuwansa suka gani, a lokacin da kamilin, ustazun ogansa ya daga yarinyar nan ya loda a kafada sannan ya juyo ya nufo motar da ita a lokacin da take ihu tana haharba kaffafuwa , a lokacin da ya karaso inda Aliyu ya bude masa a tsorace, ya dana ta cikin motar , sannan ya duko inda take ihun nan da kakkausar Muryar da bata taba sanin tasa bace ya ce"
Innalilahi, ku zo mu je mu taya amshe ya'yan Anna, wayo yau mun higa taraKISAN MUMMUKE PAGE 54
Farhana tana harararta ta nuna mata yatsa ta ce" Kandalar Anna kar ki min rashin kunya, kin san me nake ciki ne? Kin san halin da nake ciki ne? Kar ki yarda ki bata min rai? Ki bari idan kika san soyayyar sai mu yi maganar nan da ke!"
HALLAH ta doke yatsar itama tana harararta ta ce" Na makin, na fada maki in dai soyayyar da zata sa in yi fito na fito da iyayena ne bana son ta, kada Allah ya haɗa ni da ita......, FARHANA ke yanzu ko kunya bakya ji kike kiran kakarki da tsohuwar nan, mata saliha mai tsoron Allah irinta?kina so ta mutu dan ki aure namijin da ke da kanki kika san cewar baya wani son ki?"
FARHANA na dubanta ta ce" Baya so na?, lalle ma yarinya, ke yanzu kin san meye so din da har zaki dubi soyayyar da ta dauki lokaci irin tawa da shi ki ce baya so na?"