← Book details Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 97 OF 141

Sashe 97

Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Har ya juya zai fice kawai ya ji to wannan yana fita fa haukan nan zai sake balewa, dan ma Allah ya sa tana dan dakatawa idan ta ganshi? Da yaya za'a yi kenan?

Juyowa yayi ya sake dawowa inda take a hade ya ce" Tashi!"

Sai da ta kikifta ido kafin ta mike din tana waige waigen dan kwalinta

Hanya ya nuna mata ya ce" Wuce!"

Inda ya nuna din ta bi sumui sumui suka je elevator din suka shiga ya dana ya rufe ba tare da ya sake ce mata ufan ba, haka kuma ya saka tazara tsakaninsa da ita , idan ka kali fuskarsa a lokacin kuwa yadda ka san kububuwa ...........

Elevator din na budewa ya fara fita, ita ma ta fito da sauri tana waige yayi gaba tana biye da shi har kofar dakin Anna, ya dakata ha buga a hankali kafin ya jira

Ba'a jima ba Anna ta bude dakin tana dubansu da mamaki ta ce" Andadi?, Nur?"

Shigewa ta yi saboda hanyar da Anna ta basu...., sai dai shi bai shiga din ba, haka kuma ya ɗan dafe kansa ya juya zai tafi

Da mamaki Anna ta ce" Andadi, zo nan"

Dakatawa yayi , sannan ya juyo ya dawo ya jingina da abun garu yana jin kamar jiri zai zubar da shi

A tausashe Anna ta ce" Me yake damun ka? Zazabi ne?, ina sauran yaran suke?"

A hankali ya sauke ajiyar zuciya a tausashe ya ce" Suna kasa, su ai lafiyarsu kalau Anna, ita ce na ga abin zai tashi na kawo maki ita"

Da mamaki Anna ta waiga, ta hango Nur cen ciki zaune, ta maido dubanta kansa ta ce" Abin zai tashi? Wani abu fa?"

Duban Anna ya yi, ya ce" ciwon ta mana Anna, manta hulata na yi na dawo dan in dauka na same ta tana burgima da ihu, shi ne na kawo maki ita"

Anna ta zarro ido ta rage murya sosai ta ce" Wai, kana tunanin Nur bata da hankali?"

Shi ma da mamakin da ya dan kwonta a saman fuskarsa ya ce" Anna, if tana da hankali ne.... Zata ringa abinda take yi?......., a inda suka je fa yau sun tarda yaron nan bikin aurensa ne ake yi, kawai ta cire takalmi ta shiga tsakiyar maza tana ihun a barta ta yi kokowa da shi"

Anna ta zarro ido tana kama baki ta ce" Wai Nur din?"

IMAD ya gyada kai da tarin takaici ya ce" Wancen yarinyar, abinda na ga ta yi ba na mai hankali bane....., ta yiwu baki sani bane Anna "

Anna ta yi mumushi tana dubansa da mamakinsa

Anya zata tuna lokacin da ya shiga harkar da bata shafe shi ba har yayi ta magana mai tsayi haka a kan lamarin

Cabdijan shi fa sam bashi da time da shiga abinda bai shafe shi ba......, Ama gashi yau da yin doguwar fira a kan yarinyar da take tunanin ba abinda ya shafe shi da ita haka??

Murmushi ta yi, a tausashe ta ce" Lafiyarta kalau, tana da rigima ne kawai, shi ma idan an taba ta ne fa........na tabbata bata basu shawarar su je wajen yaron nan ba sai dan su sanar masa da sakona, kar ka ji haushin su ka ji Andadi?, ka musu uzuri ka yi hakuri .........."

Idnanuwansa kawai ya lumshe bai ce komai ba

Anna ta ce" Yauwa, ina son zuwa wajen Aban yaran nan in an jima "

Dubanta yayi da kula ya ce" Lafiya dai ko?, Ni ma yanzu daga asibiti in sha Allah zamu wuce cen din"

Anna ta gyada kai ta ce" Lafiya kalau fa, ka ga magana ce mai girma wannan, ina so mu je tare , ko kuma ka je Ni ma in je, ka ga ba umarni ba fa zamu basu, shawararsu zamu yi idan har suna da tsayayu su fitar su yaran, idan basu da shi ita Farhanan sai ka yi mata, wai ita din waye zaka bata???"

Murmushi yayi yanzun ya ce" Zaman Mutalab fa nata ne"

Anna ta zarro ido ta ce" Mutalab dai?, a'a, a'a, idan ka ba Mutalab ita zaka lalata zumuncinku "

A tausashe ya ce" Dukan abinda ya dace ya sani, ya sani, shi ne yace ya ji ya gani, kar ki damu da wannan Anna "

Anna ta sauke ajiyar zuciya a tausashe ta ce" To shiKenan, Allah ya tabbatar mana da alkhairi, wai me yake damunka zaka je ganin likita? Na ga jikinka ba zafi, ko wani abin ne ban sani ba?"

IMAD yayi dan shiru, kafin ya sauke wata ajiyar zuciyar a tausashe yana duba agogon hannunsa ya ce" Ina yawan bugawar zuciya ne kwanakin nan, zan je ne kawai a duba , likitoci na fadin kar a yi wasa da lamarin zuciya"

Anna ta gyada kai ta ce" Allah sarki, ko in zo mu tafi ne?"

Kai ya girgiza da dan sauri ya ce" No, ba fa ciwo nake ji ba, kawai control zan yi Anna"

A tausashe, da kula sosai Anna ta ce " Allah ya sa ba komai bane, plz ka yi kira na idan ka ga likitan , sannan idan zaka fito ka sanar min mu hadu a cen din "

Kai ya gyada kafin ya juya a nutse ya nufi corridor..........

Ido Anna ta zuba masa har ya shige ya rufe kafin ta sauke ajiyar zuciya ta yi mumushi tana sake kallon hanyar da ya bi ta ɗan sake kifta idannuwanta kafin ta juya tana rufe kofar tata ta ga Nur zaunen nan tana kallon ta fuska tamkar ta yara ta yi tsuru tsuru

Murmushi ta yi ta zauna tana nuna mata kusa da ita

Zuwa NUR ta yi ta zauna kanta a kasa, a hankali ta ce" Anna, dan Allah ki yi hakuri, kar ki yi fushi da mu, kuma du laifina ne Anna, Ni ce kadai za'a hukunta Anna"

Anna ta yi mumushi tana dubanta ta ce" Ke ce kadai ya dace a kora ko?"

Nur ta ɗan kalli fuskar Anna ta kasa amsawa

Anna ta sake yin murmushi tana duban nata dai ta ce" Ke ya dace a kora, tunda ita Farhana nan gidansu ne, ita ma A'isha nan gidan su ne Ama ke ba haka ba ko ?"

Yanzu kam sai ta ji kamar ta kwala wani rashin kunya mai girman gaske......

Anna ta yi mumushi ta ce" Dube Ni"

Nur ta dago tana duban Anna a raunane, da alamun zata yi kuka

Anna ta ce" Tun kafin in san A'isha, ke na sani....kuma tun a lokacin sai Allah ya saka min kaunar ki a rai na, ......kin san me?????"

Nur ta girgiza kai tana duban Anna

Anna ta ce" Ina jin ki a raina kamar yadda nake jin IMAD da FARHANA......., tunda na ganki a jardin na ji a raina Allah ya baki y'a....., sai dai ban san ba ke ko kin dauke ni uwa kuwa Nur?"

A hankali NUR ta gyada kanta zuciyarta na tsinkewa, a raunane ta ce" Anna, ke mamana ce, har zuciyata ke mamana ce"

Anna ta yi murmushi ta ce" to kin ga, idan ka yiwa iyayenka laifi, hukunci suke yi maka, wanda zai sa gobe ka kiyayi yi musu irin laifin nan......, kun bata min rai da baku zo kai tsaye kuka fada min abinda yake faruwa ba , cewar ba'a same shi a waya ba, da Ni da kaina zan sa a nemo shi, sai kula tashi kuka je inda yake, kin kuwa san yaron nan shi ne ya horewa Farhana kune a lokacin da muka ki tarayyar su yake daukanta a duk inda ya samu su tafi? Hakan na nufin baya daraja mu, baya mutunta mu, ko me ya samu kuma zai iya yi mata harda ku, yanzu da kuka je da ace wani abu ya same ku fa?, yaya zan yi kenan?....., samarin zamani mararsa ji babu abinda ya gagare su , su karyawa mutun kara a ido ba zai ce musu komai ba....., a halin da muke ciki a yanzu Bama bukatar wani abin irin wannan, ran yayanku ya ɓaci sosai har yace ku fitar da miji a muku aure, shi ne hukuncin da ya rigayeni yankewa wanda ba zan Musa masa kai tsaye ba, kuma ina mai tabbatar maki su ma su abanku ba zasu musa ba saboda kun isa a muku auren, kawai sai dai idan ba tsayaye sai a hakura, wannan shi ne abinda zamu je mu zanta da su......, ko baki bamu izinin haka ba???"

Nur ta dago da sauri ta dubi Anna

A hankali ta matse wajen da ya rage tsakaninta da Anna kafin ta yi saurin ɗora kanta a saman cinyar Anna tana girgiza kai a sanyaye ta ce" A'a, ban hana ba, ki yi hakuri annata, ki yi hakuri ......., dama.......dama tsayayyen ne bamu da shi mu duka, na so a zane mu shiKenan, Ama kuma yadda kika ce Anna haka za'a yi"

Anna ta yi murmushi tana duban kan Nur din a tausashe ta ce" To tashi dauko litafinki mu yi karatu"

Mikewa Nur ta yi, ta nufi hanya dan zuwa dakin FARHANA ta dauko kayanta

Tana fita daga dakin ta shige na Farhana da tarin takaicin wannan bawan Allah ta dafe kai a zuciyarta ta ayyana ' Auren zaka min?, to kai me hadina da kai da zaka min aure? Na zata na rabu da yayu masu cin zali, ashe SULaimana ya tafi Imadu ya dawo? Kai wa ya maka auren dolen? Dadin abin za'a tambayeni ne ke Hallah shin da gaske kina son Anas ?, zan ce ne eh, ai Anas ya isa a so shi, kawai damuwata daya ce jalllll, gaskiya a duba a barshi ya girma, dan ya san ciwon kansa, kukan da Anas yayi yau ko mamanshi ta rasu in da kunya da tawakali kato kamarsa zai hadiye yayi a zuciya, Ama ka zube ka hade hannaye kana rusa ihu? Hum!'
Chapter 97 · 0% Book details