← Book details Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 141

Sashe 50

Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Takan rasa hasken da fuskar mamanta ke mata na menene, haka kuma lokaci daya ta ji idan bata sanar mata abinda yake faruwa ba wa zata sanarwa??????

A harhade ta ce" Yaya za'a yi mama ta dauki kafa ta je gidan su mutumen da bamu ma san waye shi ba ta nuna ina nan ina kukan kin amincewar abanmu da kasantuwarsa mai zuwa zance wajena,?? Yaya za'a yi mama ta sake fitowa da maganar satar waya a kanki a gaban mutumen da kunya ya dace ace ta wanzu tsakaninsa da ita har karshen rayuwarmu ?????, yaya za'a yi mama ta dage kan maganar satar waya a kan ki?????" Nur ta karashe tana dafe kanta dake ta sara mata, ga tsufan da kitsonta yayi dan har tsagar ta bace......

Aunty dake dubanta a sanyaye sosai ta ce" To ke kin yarda Ni na saci wayar taki???"

Har sai da Nur ta zabura, ta dubi aunty,

Ta langwabar da kanta a raunane sosai ta ce" Ya Salam......, ba zan taba yarda cewar ke aunty zaki dauki abin kowa ba a duniya"

Auntyn yara ta lumshe idannuwanta tana dauke ajiyar zuciya

A tausashe sosai ta ce" Nur, ki share hawayenki......, ki mike ki fito ki kamama yar uwarki aiki, maganar waya ki ajiyeta a nan, idan mamanki ta kaita wajen mahaifinku zan iya kare kai na....., Ni ba barauniya bace, ban dauki abinda na san kansa Ba ma sai waya? In kirayi wa?, in sha Allah Allah zai sake kare mai gaskiya a tsakanin mu, ........."

Aunty ta ajiye zancen a hankali kafin ya ɗora da fadin" Nur ramin karya shi ne kurare, ba ramin gaskiya ba,......., kuma ki yi kokari ki ganar da shi baki aika mamanki ba, daga haka ki daina korarshi....masoyi ba zai taba zama makiyi ba kin ji????, haka kuma daga yau kar na kuma jin maganar kin amshi abin hannunsa kin fahimta?????"

Nur ta ringa gyada kai tana kallon auntynsu, har ta gama ta mike ta yi mata murmushi ta fice...................*JAMA'A NAZOMUKU DAWANI TSARI NASAMUN KUDI TA HANYAR AMFANI DA WAYAN HANNUNKU
WANNAN TSARIN SHINE METAFORCE

MENENE KASUWANCIN METAFORCE* ????

*Metaforce kasuwancine ingantacce halattacce Wanda yake biya 100 💯 Wanda ake Gudanar dashi da wayar hannu,METAFORCE is also a part of network marketing,is a 100 percent decentralized project da aka daurasa Akan Blockchain technology Wanda babu wani mahalukin daya Isa YAYI editing,hacking ko deleting wani abu acikin sa,Kuma yanada matakai yanada rassa Wanda kowane reshi ka rike a METAFORCE to ka samu GUDUMAR DUKAN TALAUCI*🌎

METAFORCE ANASAMUN KUDI ACIKINSHI SOSAI MATUKAR ZAKAYI ABUNDA AKEBUKATA

zaku iyahada miliyoyin kudi aranadaya acikin wannan kasuwanci me albarka in sha Allah

Duk wacce tashirya zata iya tuntubanmu akan wannan number
09136899615
Hajja Data

30

Nur ta ringa gyada kai tana kallon auntynsu, har ta gama ta mike ta yi mata murmushi ta fice

Ajiyar zuciya Nur ta ringa saukewa tana ganin fuskar aunty a idannuwanta haka kuma tana auna ta mama a zuciyarta......

Yaya aka yi a rayuwa mama take iya zaman awa daya tana kwatanta mata irin hatsarin aunty da irin yadda aunty ke son kasheta da yadda burin aunty ace bata da wani anfani a duniya......, ama a kwanakin nan da suka samu kusanci da aunty a yan mintuna ƙalilan sai ta ga babu abinda ya kawo ki, ko neman rai, ko neman ganin an tabe an lalace a furuci ko aikin aunty a kansu daga ita har yayarta.....?

Tunda abansu ya zaunar da su ya nusar da su saka aiki, sakawa a koyi du wata hidima ta cikin gida da aunty ke dagewa da fadan a tashi a yi, da ya zamo bata so ta ga an zauna ana firar duniya idan har ba an gama komai ba, ba kiyaya bace soyayya ce mafi kololuwar soyayyar da zata iya musu a yanzu da suke gabanta, wace zata hana a zage su, a musu dariya, ko a wulakanta su idan suka kasance a gidajen da zai zamo su ne ke rike da ragamar gidan.....wato a dakunan aurensu......, ya dage ya nuna musu ba komai yasa aunty ke jajircewa da dagewa sai an yi abin kirki ba sai dan ya zamo burinta ace nata sun fi na kowa abin kirki....., ya fada musu a lamarin gyara kayanka da aunty ke dagewa babu batun sauke mu raba....., shin me yake faruwa ne?????,

Mikewar ta yi ta fito ta shiga aikin bayan ta dinkime kan nan nata, saboda ko aunty bata san me kan nan nata yake ciki ba.........................

Suna tsakiya da aikin mama ta dawo, bata bi ta kan kowa ba ta shige dakin ta ta yi kwonciyarta , dama bata yi nisa da gidan ba tana hange har ya fito a harzuken nan ya tafi, ta je ya samu mai kanti ta loda kati ya mata kiran aminiyarta, shine ta shiga kora mata zance, harma suka yi alkawarin haduwa a gidan nata idan Malan ya fita gobe, saboda su zanta sosai da sosai, Malan kuwa ya hanata hulda da ita dama, saboda tun lokacin da aka yi Shari'a da ita ta fito ta fada itace ta yiwa mijinta asiri ya soke mu'amalarsu, bai san mu'amalar ta fi ta da karko ba, dan ita aminiyar Tata kullum fadan da take mata ta ba kanta lafiya ta yiwa aunty asiri ta kadata duniya, idan ya so ta malake uban kowa a gidan ta juya su son ranta, ita maman yaran ce ke ce mata a'a, ita da ta yi asiri ina ya je?, ta ci maganin zama da su, da kisa zata watsa gidan malan, da kisa zata fi cusawa aunty bakin cikin da zai sakata ta yi hauka tana ji tana gani, da irin Tata kisar zata yi nata yakin.........., a yanzu haka ita ta san ta cin musu fiye da tunani saboda ta tabbata sulaimana ya shige duniya ne, shi yasa Malan ke rikice kwanakin nan , ga uban tunani da yake fama da shi, dan haka kawai zaka ga yana ta kallon A'isha, kamar wani zautace, ita ta tabbata tunanin dansa yake yi.........., har ta gama ta dawo kuwa Malan bai shigo ba

Sai bayan isha'i Malan ya shigo, sosai aunty ke jira maman yara ta daga maganar waya, Ama shiru kake ji bata yi maganar ba, har Malan ya kwonta bata ce komai ba, itama kuma ta yi shirun bata ce koman ba, ama ta shirya mata tsaf, da wahala a gabanan kuma ta kara dauke kai a hayagagar Mama, kai ba zata kuma hakura ba sai wani ikon Allahn!

_______yaya ANAS_________

Gidansu yayi direct, saboda irin yadda hankalinsa ke tashe ba zai iya nufar wajen ogansa a haka ba.

Yana zuwa ya samu mahaifiyarsa a filin gida tana feraye doya

Har ga Allah a birkice yake, hakan ya sa ya karasa ya zube gabanta ya yi shiru zuciyarsa na ta bugawa

A rikice mamansa ta ringa taba shi tana kiran sunansa da tambayarsa ko lafiya?????

A birkicen shi ma ya bude baki ya ce" Wai daga na fada mata mamanta ce ta zo take fada mana halin da take ciki dan abansu ya hana in zo wajenta sai ta nuna a kan mema zata daga hankali bayan umarnin mahaifinta ne? To ko rana aka saka min Ni da ita in ya hana ai ita ba abinda zata yi bale wani soyayyar da bata wani fara ganewa Bama, mama Ni zata rinka wulakantawa zuciya ko???"

"Innalilahi wa Inna ilaihi raj'une yau Ni na ga jaraba ganin idannuwana, yau Ni na hadu da tashin hankali a gabana, na shiga uku, Anas wai yarinyar nan ce ko? Yarinyar nan ce Nur ko? Wai uban me ka gani a jikin yarinyar nan da har zata rinka daga maka hankali haka? Anas me aka yi aka yi yarinyar nan da har zata daga maka hankali haka?, Ni kam Ni na ga masifa ganin idona, wannan yarinya in sha Allah ba zaka aureta ba matsiyaciya yar iska.............."

Da sauri Anas ya rike hannayen mamansa hankalinsa tashe ya ce" Dan Allah kar ki min haka, Ni na san wulakanta wasu matan da na yi ne Allah ya kamani a kan Nur har yake jarabani a kanta....., Ama kin ga idan kika hana aurena da ita ko? Mutuwa zan yi shiKenan kowa sai ya huta......, mama kar ki sa tsoron da take maki ya tabbata mana, idan ta san Bakya son ta ba da zata so Ni ba, kuma in ta ki Ni Ko in zame maki tantiri ko kuma zuciyar ma ta buga....dan gaskiya ina cikin tashin hankali, ki yarda mama ina cikin jarabawa..............., ke kike ganin bata da komai da ya dara na wata, Ni kuwa a idannuwana a yanzu dai ban ga macen da ta kai min ita kawatuwa ba...., mama dan Allah ki tayani son ta kin ji? Ki daina zagin uwar jikokin ki!"

Ya karashe yana mikewa ya nufi ciki dan kuwa so yake yi ya zauna waje daya yama idasa fahimtar abinda ya yi mata da zafi haka da har take irin abin nan........, mene laifin sa ne shi? Me yayi da zafi haka? Ya Allah.

Mamansa tamkar mutun mutuni ta bi dakin da kallo har ya bacewa ganinta

Shigowar Fa'iza dauke da man jan da ta je siya dan su rabarbatsa dafa dukan mankanin ya fargar da mama cewa ta dawo

Da tarin haushi ta dungure mata doyar ta mike tana nunota da yatsa ta ce" Du laifinki ne , dan ubanki da baki kawo min yar jaraba dangin Mayu ba da bata kama min d'ana ba, to kuwa sai dai ta haɗa mu ta cinye, dan wallahi ba zan yarda ba, ba zan taba yarda ya auri yarinyar nan ba, alamu sun nuna min idan na yarda Anas ya auri y'ar nan an gama da Ni, tabbas zai iya mantawa da Ni a duniya, idan mun hade a kiyama ya nuna uwarta ce ta haife shi ɗan kauna, karya suke daga ita har iyayen nata Allah ya kai mu gobe!"

Tana gama fadan ta yi ciki ta lalubo wayarta ta danawa lami aminiyarta ta kora mata zance, suka yi alkawarin hadewa su isar da sakon da ya dace a inda ya dace!
Chapter 50 · 0% Book details