Sashe 121
Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Malan ya tabbatar masa sannan ya yi shiru yana sauraronsa
Malan na Magarya ya yi tsam, kafin ya ce" Allah mai iko, to ai gani nan kawai, ba nisa tafiyar ai, bari in dauko shatar mauta, ba zan jira ba gani nan tafe, idan kuwa a matukar matse ake a daura, na bada yawuna a daura, shi Elhajin ai an san usulinsa, Allah sarki auta ashe matar Elhajin ce ita?"
Yanzu kam Aban yara mikewa yayi yana mika hannu cike da jin kunya ya amshi wayar da Malan baba ya miko masa yana ta fara'a ya dubi su Anna a tausashe ya ce" Anna, ki yi hakuri, maganar sasantawa zasu yi a gidansu, Ama a yadda mamansa ta fada min abinda yake faruwa, ba zan so a ci gaba da barin magidanci a wannan halin ba"
Aban yara kam waje yayi yana fadin" Kai yanzu kawai ba zaka kimtsa bakinka ba? Sai a yi tunanin mu ne ma ke so, ko a yi tunanin saboda dukiyarsa muke murna, Bama zaka yi tambayar in ita yar taka na so ba? Kuma a ina ka dan usulin nasa ne?"
Malan na Magarya dake irga kudaden aljihunsa saboda daukan shata ya dakata , a tausashe ya ce" In sha Allah idan na zo zan zo maka da magungunan karya tambaya, abubuwan da kake yi na wanda aka shiga gabansa ne ba komai ba, to da kake maganar tana son sa ka fada min nakasunsa, Allah na tuba ko bashi da ko sisi yaron nan dan buzaye ai mata sa so shi, bayan wannan Ni da kai muka gama maganar addininsa, taimakonsa da sauransu dazu da safe, ko yana da wani hali irin su zina, sata , yankan kai ne ban sani ba?"
Da sauri Aban yara ya ce" A'a, ban taba ji ba"
Malan ya ce" AHMADU , ko dai ba kai bane ke batun nan?, to ai in sha Allah harda da a'in idan na zo za'a daura dan ban ga amfanin jiran ba......., haba Ahmadu ina tunanin abin farin cikinka ne wannan ko? Ba dan dukiyarsa ba na rantse maka sai dan ganin Allah ya fito mata da wani a lokacin da mahaifiyar Wancen ke ganin an kakaba mata yarinyar ne dan dole, na zata zaka karba da farin ciki sosai ne Ahmadu?To ka ga a RINGA yiwa Allah godiya, sulaimana ne nake ta jira, ka san sosai yake da mutane a kasuwar nan, baka gani ba, dama yana cewa zai zo , ga tafiyar ta samu, gamu nan zuwa harda yayunsa zamu taho a daura auren, zan zo maka da malun malun ka saka, ka ga ka wanke ranka ka ji? Allhairin kenan in sha Allah, soyayya kuma idan auta na so dan girman Allah kar ta so shi, ba sai in yi mata bita zai zai da sunansa ba? Dan in na yarda auta ta karya mana kara a ido ta ki bawan Allahn nan Allah ya tsinen, gani nan zuwa Ahmadu "
Kitttt ya kashe kiran, ya bar Aban yara tsaye da waya a hannu cike da mamakinsa
Nur kam sai da ta gama wanke komai ta kilace sannan ta fito ta zo ta kara bin su da kallo kamar yadda yanzu ma ta ga sun sake binta da kallo , hakan ya sa da sauri ta wuce ta shige elevator cike da tsoron kallon nan , da sauri ta nufi dakin Farhana ta shige da yanayin tashin hankali ta ce" A'isha, wai kin ga abinda yake faruwa a falon kasa kuwa?"
FARHANA da ta farka , tashi ne bata yi ba zaune ne ta bude ido tana kallon Nur dake sanye da hijab ruwan hanta mai hannaye ta ce" Me ake yi a kasan ne na tashin hankali?"
Nur ta watsa hannayenta ta ce" Ni ina zan sani, taro ne makil, babu wanda babu, harda wani dattijo Balarabe banma san shi ba, kuma kamar an turke Anna, kamar jayayya suke yi, harda Abanmu da auntynmu, da maman yayanki da Aban yayanki, harda su Mutalab da yayunsa fa.........., kuma abin tsoron gaba daya suka bi Ni da kallo da zan taho, da na sauka ma, Farhana me yake faruwa ne?"
FARHANA ta zabura tana zaunawa bakin gadon hadi da zarro ido ta ce" Kar dai aje maganar auren namu ake yi?"
A'isha dake karatu ce ta ajiye da sauri tana dubanta ta ce" maganar aure kuma? Kar dai aje a yi maganar tawa auren nima Abanmu ya ki yarda da maganar yayanmu?, NUR ba'a ce mu zo a tambayemu in muna so ba? Kar aje Abanmu ya bani wani da ba yayanmu ba in shiga uku"
Nur ta zauna jiki a mace ta ce" to kuwa ina mai tabbatar muku ko meye ake tattaunawa a kasan nan ba abin kirki bane, saboda da mutun ya matso suke yin shiru, kuma sai su bi mutun da kallo, ta yiwu an fasa auren naku ne ku ma"
A'isha ta zabga mata harara tana duban FARHANA da ta sauko ta ce" Bari in yi bruch mu sauka kasan nan, an fasa fa? Ai tunda aka ce an min mijin nan gwara a daura kowa ma ya huta, Ni da kaina na gaji da fitinar Inna yanzu!"
Zuru du suka yi, kowa na tunanin abinda yake tunani a ransa
Abdul bassit da ya shigo dakin da IMAD yake bayan ya leka daki biyu bai same shi ba, direct inda yake ya karasa yana murmushi hadi da sake dubansa kafin ya ce" Wai ba zaka sauko ba? Ka ci wani abu ma kuwa?"
IMAD dake kallon sa ya kankance idannuwa a nutse yace" da zaka zo, da wa ka hadu a hanya?"
Abdul bassit ya wani dan girgiza kafadu kafin ya ce" Da bab na hadu, man yarinyar nan ta dace da Ni nake fada maka, auren nan da za'a daura ka taimaka ka haɗa da Ni mana plz"
Gaban IMAD sai da ya fadi, haka kuma nan take ransa ya bace.....sai dai bai samu yi masa magana ba kiraye kirayen sallar azahar ya saka shi duban time da mamakin gudun lokaci
Mikewa yayi ya nufi bayi
Bai jima sosai ba ya fito ya nemi nufar darduma
Abdul bassit ya zarro ido ya karasa ya janye dardumar kafin ya kama hannunsa ya ce" Allah dai ka je masallaci, kuma uncle na falo yana jiran ka, na san yanzu sun fita Masallaci, aby ke son magana da kai, Ni har kunya ta kama Ni, a daki zaka yi sallar kenan?"
A dole ya bi bayansa, yana tunanin cenza rigar dake jikinsa, sai dai ba zai taba shiga bangarensu ba, zai yiwa Aliyu texte kan ya je ya kawo masa sutura
Da suka sauko, matan nan uku kawai suka tarar a kasan, su ma suna haramar tashin sallar, hakan ya sa kawai suka wuce bayan ya gaishe su sama sama da musu alamun sun tafi masallaci
AUNTYN yara kam sai sune kai take yi cike da kunya da jin nauyin kowa, saboda abin ya zo mata a ba zata,
Anna ta Dube su a tausashe ta ce" Mama, aunty idan aka fito daga masallaci ina so mu je mu samu NUR, dan Allah ina so ku kama min mu rarasheta mu ji abinda yake ranta, suna nufin da yama zasu daura mata aure fa, ina so in ji idan ta aminta da auren nan, in bata so kuma barinsa za'a yi!"
Mama a tausashe ta ce" Anna, ki daina cewa in ta ki dan Allah, Ni da kin bari na je din, da kin bari na zauna da ita din, da kin bari na nuna mata tsantsan kaunar da nake yi mata, da kin bari na nemo mana soyayyar koda bata yi mana......, bana so ki ringa nuna ba zata so ba kin ji?"
AUNTYN yara kam murmushi kawai take yi, bata ce komai ba, sai dai har cikin zuciyarta ta ji ta yarda da maganar nan, har cikin ranta ta ji tana son maganar...........kuma zata so sosai ta tabbata.
Masallaci suka haɗe, bayan an gama sallah du suka zauna har aka yi addu'a aka shafa
A nutse mutane ke raguwa a masallacin, haka kuma WA'INDA basu ganshi a salolin da suka gabata ba suka ringa yi masa sanu da zuwa du a tunanin ko tafiya ya yi? Wanda hakan ya sa ya ji kunya sosai ta lulube shi, har ya yiwa kansa alkawarin in sha Allah ciwo kashirban ne zai hana shi samun sallah a masallaci
ANAS dake dan boyewa ne ya rabo da girmamawa sannan kasa kasa ya ce" Barka da warhaka sir, ............"
Dubansa IMAD ya yi , kafin ya karbi hannun da ya miko masa suka gaisa , sannan ya mike ya fito saboda su Mutalab na waje dama, uncle da su Malan ne kawai ke ciki tare da liman da ladan
Yana fitowa Anas na biye da shi, Aliyu ya gala masa harara, sai dai bai fasa bin bayansa ba har suka karaso kusan su Abdul bassit
Da kula IMAD ya dubi Aliyu ya ce" ka kai Anas kampanin kayan gwonjo........, a bashi mukashin shugaban direbobin cen..........a kara masa albashinsa"
Kwarai aikin da za'a mayar da shi, ya fi wanda yake ciki yanzu kauri, saboda a cen Bama a daukan wanda bashi da shedar takardar karatun boko ba, wuri ne da ake cinikayya na dilolin lesuka da atampopi, waje ne da manyan mutane ke zuwa mata da maza daga wasu garuruwan ma dan sarin kaya.....kwarai albashi ne mai tsoka , kuma samun waje a cen ba karamar Sa'a bace, sai dai aiki a kusa da ogansa ya fi wannan domin shi ya san ogansa mutun ne mai kyauta , a cen kuwa da wahala ya ringa samun kyautukan da ba na albashinsa ba