Sashe 2
Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da farko dai mijinta, ya zamo irin mutanen nan da suke saka d'a a gaba da kowa, tunda ƴaƴansu suka fara wayo ta gane cewar a zamantakewarta da mijinta a yanzu idan har zaman lafiya take so dole ta bi ya'yan nan na cikinta kafin a wanye kalau, wanda yau da gobe da irin yadda yake tsireta a gabansu ya sa a yanzu ita da Sulaimana sai su yi sa in sa, dan tsaf yake tsayawa ya yi mata gardamar abu ido cikin ido, yanzu ne ma da sauki sauki idan tace ba zai yi abu ba yake buya ya fadawa uban, kuma uban sai ya nuna ai laifinta ne, ta cika takura, kamar ba ita ta haifi yara ba, ta matsa musu, gayanan ita mai bin sulaiman din ta gujeta ta koma dakin abokiyar zamanta saboda zafin zama irin nata......
Sam babu wanda ke ganin abinda ita take gani, har ya zamo a yanzu da NUR wato imtee ta kai shekarun da a duniyar mu ta hausawa ta gama girma sai fatan shiga dakin miji kuma a cancana rayuwa har mai yiwuwa ta yiwu ....ama uwar rikonta, wace ta janyota jiki, ta nuna ta fi sonta fiye da mahaifiyar da ta kawota duniya, har ake yaba mata ana ganin lalle a yanzu da wahala a samu mata irinsu dake yiwa yarinya kishiya irin wannan a n, bayan ita ta san rikon aikata goshi ne tsantsa ke wakana a nan Ama bata da bakin magana!
Dole ta kirayi wannan riko da haka, domin wani irin riko ne take yiwa yarinyar ba kwaba, ba kyara, ba gyara saima saka wasu irin tunani a kai wa'inda ke Tsoratar da ita, dan kuwa a shekarun imtee fa sai ta biyo layi ba hijabi ta zo gida, wai karama ce yaushe ma aka haifeta. Ga Imtee da jiki irin na ginanun mata, babu inda bai kai tsole ido ba....... Iri irin haka ke saka mata wani shaku da tsoro, sai dai karfin yawun jama'ar da suka zagayeta ya saka mata dari dari da gudun yiwa abin tufka mai kyau ta hanyar fuskantar lamarin, harma da tsoron fito da shi ko yin fito da fito da shi ɗan kar a zageta cewar lalle butulu ce ita ta kasa godewa mace mai son ta.
A yanzu haka abinda ya hadata rigima da mai gidan nata, irin yadda saurayi mai shekara ashirin da daya a duniya kamar Sulaiman ya zamo du idan zai fita sai dai ya ringa zagaye zagaye dan ya samu abin sakawa na mahaifinsa ya saka ya fice abinsa, dan tsabar kiwya baya wanki, harta na kayan zuwa masallacin juma'a a rana irin ta yau mai albarka, duda ba wasu tarin kaya ne da shi ba wa'inda zai rinka tarawa a jaka yana cenzawa ba, Ama yana da daidai gwargwado domin kuwa mahaifinsu fa yana iya hanawa kansa ya musu, domin matarsa ta farko ma y'arta daya rayaya , wato A'isha , sai Sulaiman din nan da kuma imtee hakan ya sa du dan samun da yake yi na shagon saida kayan miyarsa da yan kayan masarufi suke tafiya a bukatun yaran nan,
Dan ma Allah ya taimake su, ba a gidan haya suke ba, gida ne da ya gada cikin gadon da aka raba na mahaifinsa aka bashi, wato gidan mai dauke da daki biyu ne kacal, sai dakin dake zaure wanda a ciki Sulaiman yake da kuma mahaifin nasa domin dakunan cikin gidan biyu ne, na auntun yara ciki daya ne, na maman yara ne mai ciki biyu....ga yan mata sun girma, sai kawai ya zamo zamansa ya fi yawa a dakin zaure...... ai da sai sun shiga tare tare na rayuwa sosai da sosai ko dan kudin haya.
A yanzun ma abinda ya bata haushi katon saurayi kamar Sulaiman ya zo wai wani zai dauki jalabiyar babansa , bayan jalabiyun nan kwaya uku ne da shi du duniya , dayar yakan zauna da ita ne a zaman gida, wace ya dauka din kuwa da ita yake wankan juma'a du juma'a ta Allah, sai wace yake zama a shago ita ta fi mutuwa ma....shine yaron nan ya daga hankalin ita zai saka, dan tace ba zai yiwu ba ba zai dauka na, shine ya yi mata rashin kunya ta hanyar fadin shi fa sai ya dauka, Shikenan daga cewa ya fita idannuwanta ta rufe ita fa ba sa'arsa bace, ya kiyaye harshensa idan yana yi mata magana, ya kiyayi fushinta , shine mahaifin nasa ya tareta da fadin wala haula wala kuwata Ila bilah, zata daga masa hankalin ko? Shikenan ba damar ya zo dakinta sai ta ringa daga masa hankali a kan ya'yansa? To ta ci kanta ta kiyaye shi ɗan a kan ya'yansa wallahi yana iya cira mata cikitin zawarci a yanzu da dukan wani alkhairinta ya kare furfurar tsufa ta gama bayana a gaban gashinta da bushewar hannaye ya sake ta ta je ina?sani ne malam bai yi ba, ko sarkin ta ya yi shi ne mai rikon ta, Kai innalilahi wa Inna ilaihi raj'une, ita kam tana cikin jarabawar dake sakata fashewa da kuka a duk lokacin da ta samu kanta a kaka naka yi ta lamarin cikin gidan nan!
Ta dauki lokaci sosai a dakinta, ga zafin rana irin ta ranar juma'a, gashi ita bata dakin ciki daya ne kuma bashi da wani girma, na maman yara ne kurya da falo
Cikin gaggawa ta fito ta hasa wuta ta ɗora silalan shinkafa sannan ta daura alwallah ta shige sallah dan an fito daga sallar tuni, ba zata so ya dawo gidan nan bata gama abinci ba, duda ta san da wahala ya kuma shigowa gidan sai dare .
Wuni ta yi tana ta aiki, dan kuwa du rashin yawansu gidan nasu wuni ake ana dauke cen ajiye cen, bale ita mace ce da sam bata son dati, hakan ya sa idan girkinta ya zagayo takan hade tun daga ɓangaren uwar gidan nata da nata bangaren da kuma dakin Sulaiman ta share ta gyara ko'ina, dan ta riga ta saba da aikace aikacenta tun da jan sawayenta a lokacin da aka yi mata auren farko ma shekararta goma sha daya ne, dan auren wuri ne aka yi mata, a hannun mijinta na farko ta girma ta yi wayo sai da suka shekara goma tare sannan Allah ya amshi abinsa, a yanzu shekarunta arba'in da uku, karamin jikinta ya sa sam bata wahala wajen motsawa.
Tana aikin tana ta ambaton Allah ne a cen kasan zuciyarta, saboda abinda ke ci mata tuwo a kwarya irin yadda kiri kiri aka rabata da Y'arta kwaya daya mace kuma aka koyawa y'ar rashin jin kai da tausayinta, domin idan aiki zai kasheta a gidan nan imtee ba zata fito ta kama mata ba, hakama Yar uwarta A'isha.
Sai da dare ya tsala sannan babansu ya shigo ya shige wanka, bayan ya gama ya shige cikin sange yayi kwonciyarsa dan har yanzu fushi yake yi da ita,
Tana hankalce da shi har sai da sawaye suka dauke sosai sannan ta tarda shi, ta yi anfani da damar da gareta a kansa har ya zamo garin Allah ya waye yana amsa gaisuwarta da sakewar fuska harma da sakawa aka dibo mata fulawa da kayan miya ta jajaga wainar fulawa aka karya da ita kafin ya fice wajen neman abincinsa, domin har yanzu bai gajiya da fita nema, dan hatta kasuwa yake zuwa a kekensa yayi sarin abinda ba zai fi karfin hawa keken ba , sai idan ya san siyayarsa da yawa ne yake zuwa a motar haya ko kuwa sulaimana ya je ya saro.
Tunda karfe takwas ta yi, auntyn yara ke duba kofar dakin abokiyar zamanta tana jimirin jiran ganin fitowar su imtee dan zuwa islamiyya, Ama shiru kake ji, tunda suka amshi yaji suka ci wainar fulawar nan ita bata kuma ganinsu bama, gashi har karfe tara na neman yi basu fito ba, makarantar da ake shiga karfe takwas da rabi a fito sha biyu, ya zamo dai yaran nan sun gama sabawa da Latin zuwa islamiyya, kai imtee fa hatta bokon ba wani cika zuwa ta yi bama, dan kuwa tsaf safiya ke yi yar uwar ta yi tafiyarta ita ace ta tashi da ciwon jiki ba zata iya tafiya ba, kuma Shikenan ta yi wuninta a daki bama ta fitowa bale har ta kara wani da dauke kara a cikin gidan'''''''''
Cen dai da ta ga karfe taran ta kusa sai ta nufi dakin da sakewar fuska ta yi Salama sannan ta shiga tana sake sakin fuskarta ta ce" Bari mu kara gaisawa maman yara, fatan an tashi lafiya.....? Ni yaran nan nace lokaci fa sai shigewa yake yi , ban ga sun fito sun shirya bama bale su wuce islamiyyar a kan lokaci"
Maman yara ta dubeta, kafin cikin yannayin basarwa ta ce" Au, islamiyya ko? Haka ne ashe yau asabat, to ai inaga sai dai ita A'isha ta tafi, imtee yau tace da kasala ta tashi ba zata iya hayaniyar islamiyya ba"
Da mamaki Mama karama ke kalon maman yara,
Du yadda ta so juyawa ta yi tafiyarta sai ta ji ta gaza
Da farko ta so ta tsaya su fahimci juna da maman yara yada zata tsawatarwa imtee dan ta fito ta je islamiyya, sai ta tuna cewar tabas ihu bayan bugu ne zata yi da batawa kanta lokaci, Sai kawai ta nufi kuryar dakin maman bayan ta saki murmushi ta dage dan yololon labulen dakin, ta ga A'isha na ta shirin tafiya islamiyya, ita kuwa tana kwance saman katifa ta lumshe ido kamar wace take barci hancin nan nata zuwat yana shaƙar nukusashiyar iskar dakin, dan komai a watse yake ba tattara bale shara .......
Bata tsaya bata lokaci ba ta karasa shiga ta daga hannunta ta Dada mata duka a cinyarta fili............💅💅💅💅💅💅💅💅💅💅
*KISAN MUMMUƘE*
💅💅💅💅💅💅💅💅💅💅
_PAID BOOK_
*BY*
_SAJIDA NIJAR_
*Yan Naija Mutanen mu 1k ne a kan wannan account number 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank* sai a bani shedar biya ta layi na kamar haka +22793811618
*Yan Nijar mutanen mu zaku turo da hoton kati ta airtel ta dala dari , wato 500francs cefa a kan Numbarna kamar haka +22793811618*
*Na gode, sai kun zo.....taku ce SAJIDA NIJAR*