← Book details Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 141

Sashe 41

Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*JAMA'A NAZOMUKU DAWANI TSARI NASAMUN KUDI TA HANYAR AMFANI DA WAYAN HANNUNKU
WANNAN TSARIN SHINE METAFORCE

MENENE KASUWANCIN METAFORCE* ????

*Metaforce kasuwancine ingantacce halattacce Wanda yake biya 100 💯 Wanda ake Gudanar dashi da wayar hannu,METAFORCE is also a part of network marketing,is a 100 percent decentralized project da aka daurasa Akan Blockchain technology Wanda babu wani mahalukin daya Isa YAYI editing,hacking ko deleting wani abu acikin sa,Kuma yanada matakai yanada rassa Wanda kowane reshi ka rike a METAFORCE to ka samu GUDUMAR DUKAN TALAUCI*🌎

METAFORCE ANASAMUN KUDI ACIKINSHI SOSAI MATUKAR ZAKAYI ABUNDA AKEBUKATA

zaku iyahada miliyoyin kudi aranadaya acikin wannan kasuwanci me albarka in sha Allah

Duk wacce tashirya zata iya tuntubanmu akan wannan number
09136899615
Hajja DataINDAI KUNSAN KUDIN KUKESON SAMU A ONLINE BUSINESS TO KAWAI KUYI JOINING GROUP DIN NAN 👌🏻😅KUNSAN bani kawo abun banza
💃🏻https://chat.whatsapp.com/L64v3OVQ52pJqtMT51yL2x

24

A dole ta mike jiki ba karfi ta nufi wajen Masallaci dan ta yi sallah ta koma aji, domin ta gane cewar Anna ta yi nisan kiwo ne

Bayan an tashe su daga makaranta yau ma ita fa Na'ima kallo irin na jin haushin juna suka jefi juna da shi

IMTEE ta girgiza kai a lokacin da aka ɗauki Na'ima a mota, a ranta tana ayyana ' Allah ya nuna min ranar da zaki yi batan basirar fitowa a kafar ki, sai kin sha mamakin dukan da zan maki !'

Bayan sun fara tafiya ne IMTEE a tausashe ta ce" Fa'iza fushin kike yi da ni har yanzu?"

Fa'iza ta yi mata banza, saboda har ga Allah zuwa yanzu haushi take ji sosai a ranta na yadda IMTEE ke yiwa ƴaƴanta

A tausashe ta ce" Ki yi hakuri, ai ba zan kuma yi masa fushi ba, abinda an ce abanmu ya aminta da alakar mu?, Ni yau du ban ganshi Bama"

Fa'iza ta dube ta da dan mamaki ta ce" Kina nufin kin ajiye fushin naki na jin dadi a gefe????"

IMTEE ta yi murmushi tana gyada kanta

Fa'iza ta yi murmushin itama ta ce" Allah ya sa, yau ai ba zaki ganshi ba, tunda safe mai gadin gidan da yake aiki yayi kiransa cewar uban gidansa ya zo, yau ko a leke ai da wahala a ganshi yana cen wajen aiki"

IMTEE ta gyada kai ba tare da tace komai ba a ranta kuwa tana tunanin ko shine dalilin da yasa bata ga Anna ba yau? To shi idan ya zo du sai ya Hanna mutane zuwa inda ya dace ne????????

Bayan Fa'iza ta yi kwanar layinsu A'isha ta ce" Yaushe Aban ya amince da maganar nan?"

IMTEE ta dubeta tana murmushi ta ce " Dazu mama ke fada min, tace ma shiKenan gabanan ba wani abu dan an gani da shi, tace ko me na kyautatawa in masa, "

A'isha ta ɗan dubeta, a hankali ta ce" A'a, hakan ba yana nufin za'a ganki da shi a cikin gari ba, saboda ba mijin ki bane, idan ya zo gida ku zauna ba laifi bane, Ama ba zan yarda da batun a ko'ina ba gaskiya"

IMTEE ta dubeta kafin ta tabe baki a ranta tana ayyana'ka ji uwata, harda wani ba zata yarda ba, A'isha idan tana wani abin sai kace wace ta haife ni, to sai ki hana in gani!'

Ta yi gaba tana turo baki, Aisha kuwa ta ɗan dafe gaban goshi sakamakon irin yadda take ci gaba da ganin abubuwan tashin hankali a kan mahaifiyarta wanda bata isa ta fada ba, dan dai a yi mata kallon wace ba yar halal ba, ko yayane halin mama yake ita ta haifeta, sai dai ta bi ta da addu'a a cikin zuciyarta.

Da suka karasa gidan Mama bata nan, abinda ya zame musu wajibi suka shiga yi.....

Bayan sun gama haka kawai Imtee ta je inda ta boye wayar nan da ya bata tana ta tunanin ya dace ta kuna yanzu, tunda an yarda ya fara zuwa inda take, idan ta kuna sai su yi magana da shi, ta yiwu ma ta samu sakon shi a wayar

Sai dai du irin neman da ta yi ba waya ba labarin ta

Sosai abin ya daure mata kai, har ta fito tana duban A'isha ta ce" aish, baki ga wayar nan da yaya Anas ya bani ba wai?"

A'isha dake ferar doya ta dubeta tana girgiza kai ta ce" Ba a jakar ki na ga kin saka ba? Ko mama kika ba ajiya?"

Nur ta yi dan tsam sai kuma ta koma ciki tana fadin" Ta yiwu dai maman ta cenza mata waje

Auntynsu dake yiwa A'isha jajage ce ta shiga tunanin waya kuma? Wace irin waya?, kar dai aje Nur abin hannun yaron nan take amsa?, Subahanalah Ama kuwa da an fara tarayyar nan ta gurguwar hanya idan har ya zamo tun yanzu tana karbar abin hannunsa......, Ama kuma sai bata tambaya ba, dan ta tabbata yarinyar zata tambayi mamansu wayar, idan maman nasu ta bata wayar kuwa zata fi jin dadin tarbarta da maganar idan wayar ta bayyana.

_______________________________

Tunda safe MAZNA ta saka kannanta yan mata a gaba kowace ta haɗa tarkacen ta ta koma ɓangaren Anna ba tare da Annar Bama ta san sun shigo bangaren nata, saboda a lokacin da Anna ta gama sallah ta yi adu'o'inta kwonciya ta yi dan ta san bakin nata ma ba zasu fito da sasafe ba, koda zata gansu sai kusan goma na safe, harkar girki kuwa tunda asubahi chef ta zo ta rubuta komai ta tafi, ta tabbata za'a kula da su ta wannan fagen, haka kuma bata cika matsewa abinda ya shafi MAZNA waje ba, domin ta sani ne yanzu da mijinta ya zo komai zai shiga hannunta ne

Bayan sun koma ta koma ɓangaren ta ta budewa masu aiki suka shiga kyalkyale mata du inda ya dace, sannan ta sa aka shige kicin aka shiga girka masa abin kari

Kusan karfe tara da wani abu ta salami kowa sannan ta haye nata dakin ta sake yin wanka ta sauko kasa ta zauna tana kada kafa tana jiran fitowarsa........

Cen kusan sha daya na safe ya bude dakin nasa ya fito a nutse cikin shigar kamala, domin kuwa jalabiyar ce yanzu ma a jikinsa, dan ya fi saka jalabiya fiye da kowani tufafi a rayuwa, haka kuma ire Iren wanda yake anfani da su masu kyau da tsada ne, suna matukar karbar jikinsa

Kansa ba hula, hakama ba hirami, hannunsa dai ke rike da wani karamin carbi fari kal mai santsi da kyau a ido

Mikewa ta yi ta zuba masa ido a lokacin da shima ya dakata ya zuba mata nasa idannuwan masu ɗauke da wani sinadari mai matukar kashe gaban bawa........

A sanyaye ta furta" Barka da safiya Akul"

Idannuwansa ya lumshe mata kafin ya juya a nutse da niyar fita

Da sauri ta furta" Dan Allah ka tsaya mu yi magana"

Dakatawa yayi, sannan ya juyo a nutse ya dawo ya zauna saman kujera yana dan mikar da sambalelen hannunsa kafin ya zuba mata ido yana dubanta

Dan daburcewa ta yi, a hankali ta zo ta zauna kusa da shi a rainane ainun ta ce" Na yi laifi, ina neman afuwarka"

Idannuwansa ya dago ya zuba a kan fuskar ta

A hankali ya bude lebensa ya ce" Dalilin ki kaɗai nake son ji"

Da sauri ta riko hannunsa ta kai wajen kirjinta ta jimke ta ce" Bani da wani gamsashen dalili, sabawar time muka riga samu , bana samun ta shi yasa har na tafi bata sani ba....."

"No, kar ki kawo min maganar da zata iya bata min rai!" Ya fada a hankali, sai dai daga yanayin da ya dakatar da ita ta gane a hasale yake tabasssss

Kara tausasa kalamanta ta yi ta ce" Ban kyauta ba, ka yi hakuri, ka san cewa ba kyau yin dogon fushi.....? Bana hayacina, fushin ka na daga min hankali .....plz Akul"

Idannuwansa ya lumshe, a hankali ya fitar da boyayiyar ajiyar zuciya kafin ya janyota jikinsa ya sakata a jikinsa , kanta a saman kirjinsa, a hankali ya dan yi tpng din bayanta kafin ya furta" Zan je wajen Anna....., kin kawo min abincina cen???"

Da sauri ta gyada kanta, cike da farin ciki ta sauka daga saman jikinsa sannan ta nufi dakin ta

Murmushi ya yi, ya mike yana dan shafa gefen fuskarsa ya fice ya nufi bangaren Mama

A lokacin da ya je tana ta shara, saboda Malan kin fada mata yayi da zuwan IMAD din, dan kuwa ta aika ta kwana a kofar bangarensu, shi yasa bata wani damu ba dan bata san cewa ya sauka ba

Yana yin Salama ta dago da karfi tana zaroo ido

Da farko ihu ta saka na farin ciki, sai kuma ta juya wajen Malam tana nuna masa, wanda yake saman buzu yana ta karatu, shigowar Imad din ya sa ya dakata yana murmushi dan kuwa ya san a rina idan ma bata kwashi rawa ba da sauki sauki

Da sauri ta je ta ce" Malan, Elhaji ya zo, La'ila ha ilalahu, yaushe ya zo???"

Sai kuma ta juyo inda yake da mugun sauri tana dafe haba ta ce" Na rantse ya zo, innalilahi yaushe ka zo????, bari in dauko maka tabarma, a'a kujera zan baka, ko kuwa bari in shinfida maka katifa ....."

Malan na dubanta ya ce" Ki nutsu mana "

IMAD na murmushi ya karasa ya duka inda Malan ke zaune suka kara gaisawa, Malan din na masa ya gajiya, ya amsa a tausashe kafin ya dubi mama wace ta duka tana fadin" Ina kwana? Ya gajiya, eh ya aiki? Ya jirgi? Kulun kulun Malan sai yace jirgi zai kawo ka, tun ina irga jiragen har na gane karyar banza ce kawai......."

" a'a mama, kar mu yi haka da ke, ba nace ki daina gaggawar rikicewa ba?, ina addu'ar da na koya maki du idan kika ji kamar ki yi ta magana? Ba nace ki ringa yi ba??" IMAD ya fada a tausashe yana katse mata zancen da ta kwasa ba tsari ba daidaitawar harshe

Mama ta yi shiru cen kasa kasa tana ta karatu Ama kuma farin cikinta a bayane yake na jin dadin ganinsa
Chapter 41 · 0% Book details