← Book details Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 131 OF 141

Sashe 131

Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

'Ya Allah, tabbas Allah ya yi musu baiwa mai girman gaske, wato mata' abinda yake aiyanawa a zuciyarsa kenan, ya kara shafa gefen cikinta, a hankali ya furta " Nur......."

Nur da ba barci take ji ba, kawai yannayin da ta samu kanta a ciki ke so lalle lalle sai ya sumar da ita tsabar shiga hali na shauki da bugawar zuciya.....a hankali ta ɗan motsa alamun tana jinsa hakan ya sa ya ce" Zaki so Ni kuwa wata rana.....?......"

Mamaki ya kama mata zuciya......

Cabdijan, so? Wane kalar yake so wanda ya hana ta kasa kiya masa du irin azabar da ta san cewar zata sha?
So ? Wane ne yake son gani wanda ya da a duk lokacin da ta samu kanta a Daf da shi take zaunawa ta yi ta masa surutu?

So? Wane yake so sama da biyayar da take yi masa koda kuwa bata so a rayuwa??????????????

"Nur..........., ki so Ni, koda kadan ne kin ji?, idan har kika saka koda kadan ne a ranki , zamu fi jin dadin zama da juna......., domin idan baki so Ni ba, zaman zai iya yi miki tsayi.....U seee ina tunanin har in mutu ba zan barki ba"

Ya fada cen kasan makoshi

Dago kanta ta yi da sauri saboda abinda ya fada din

A hankali ta ɗan matsa damtsen hannunsa......, kafin ta rage girman idannuwanta cen ciki ta furta" Mu mutu dai ya dace ka ce yayan FARHANA.............., ka daina tuna min abinda yake dole.........domin ni.........ni...............ina............"

Gaba daya ya juyo da ita yana kallon ta, a hankali ya ce" Kina me?????"

NUR ta yi dan murmushi tana boye fuskarta a wajen habarsa cen ciki ta ce" Ina kyautata zaton ko na mutun......zan mutu ne da son...............Yayan FARHANA "

Jikinsa ya sakata da karfi ya rungumeta yana lumshe idannuwansa hadi da sauke ajiyar zuciya mai dumi mai kara saka bawa a shauki.................

Sun kara daukan wani dan lokacin, cen ciki ya furta" Ina son ki"...........

Idannuwanta dake daukan nauyi na barci ta sake lumshewa tana sake kwonciya da kyau......har barcin yayi awon gaba da ita, barci mai nauyin gaske , wanda sai da ta yi barcin ne ya daga a hankali yana dake duban fuskar ta kafin ya sake yin dan murmushi ya mike a hankali ya dauki Babar wayarsa ya koma falo ya zauna yana mike kafafuwansa hadi da shafa gefen cikinsa a hankali ya saki murmushi sannan ya dana NUMBAR Anna ya kara a kunnensa ...........

A nutse yayi Salama bayan ta daga kiran, hakan ya sa ta amsa a tausashe ita din ma kafin ya gaisheta, sai kuma suka yi dan shiru na dan lokaci

A hankali Anna ta ce" Bamu yi haka da kai ba, yaya maganar uncle din ka?"

Sai yanzu ya ji nauyi da kunya sun kama shi, Ama kuma dai ya dane a tausashe ya ce" Ni ma, ban so haka ba....., ki yi hakuri , tana cikin aminci, idan kuma in kawota mu taho yanzu?"

Anna ta girgiza kai tana duban Mama dake yar dariya ta sake girgiza kanta a hankali ta ce" A'a, ka kula, ka kiyaye , ka bi a hankali"

Mama ta zarro ido tana duban ta ,

Shi ma sai ya sake sada kai kamar a gabansu yake, a hankali ya ce" In sha Allah......, sakon kuma, Abdul Fatah zai kawo, daga aljihuna ne"

Murmushi Anna ta yi, ta ce" Masha Allah, dama ina jiran kiran naka.......Mazna na asibiti IMAD "

Tsai yayi , kafin ya bude idannuwansa

Anna ta ci gaba da fadin" Cikin dare muka kai ta, likitar da muka samu ta nuna mana abinda aka yi mata na aiki na tafe da tempérament dinta, ya zama lalle lalle ta kwontar da hankalinta, ko kuma a cire mata ........, shi ne na nuna mata zamu je a cire ne, sai ta ce a halin da take ciki, kar a yi tafiya ta jirgi da ita, idan har muna da halin dauko mata likitan a dauko a zo a yi mata a nan........."

Ta dan dakata, kafin ta ci gaba da fadin" Shi ne na tambayeta ko AKOY wanda zata hada mu? Tace kwarai AKOY, likita ce mace ce, kuma ta san aikinta......., .......na amshi numbarta, dan ku gama magana ta taso, likitar tace a gaggauta yi, kar hawan jinin ya kai girman yi mata ila..........."

Ajiyar zuciya ya sauke cike da jin bacin ran dalilin wani dalili nata ta saka kanta a halin tashin hankalin n rayuwa

A hankali ya ce" ku yi maganar Anna, du abinda za'a saka a fadawa Aliyu........, Allah ya bata lafiya"

Dan tsai Anna ta yi, kwarai bata so yana haka har cikin ranta, ba dan bata ji zafin abinda Mazna ke yi ba, sai dan tana so a samu masalaha a lamarin sosai

A tausashe ta ce" Ka samu ka leka ta , zan tura maka adrsss din inda take"

Yanzu kam bata tsaya ta ji amsarsa ba ta kashe kiran tana ajiyewa hadi da duban Mama wace ta hade rai, ta ce" Ya dace ki taya Ni, ya kamata ace kin masa fada zuwa yanzu"

Mama ta sauke ajiyar zuciya a tausashe ta ce" Zan masa fada Ni ma, ama zan bashi dama ya gama hucewa, Anna ba kowa yake da zuciyarki mai hakuri da saurin saukowa ba, ba kowa bane zai iya yadda kike yi a rayuwa......, Allah ya baki ladan, Ama ki bashi dama ya gama hucewa da kansa, na tabbata zai yi abinda ya dace"

Anna ta yi murmushi kawai, a tausashe ta ce" Shikenan, yaya jikin na yaran nan?"

Mama ta yi yar dariya ta ce" Mutuniyar ce dai dole sai da aka jona mata karin ruwa, Ama A'isha da sauki sosai, su da kansu ai suka hakura da maganar kunshin amaren yau, maman MUTALAB kuwa ta nin'ninka masa sadaki har tausayi ya bani da ta fara dungure masa kai"

Murmushi Anna ta sake yi kafin su ci gaba da abinda yake gabansu, har yama ta yi Abdul Fatah ya shigo ya kawo kayuta ta cheik da ky din plaza ya ajiyewa Anna hadi da katin baban butik din suturu wanda aka bada damar a je a hada mata duk wani abinda ake so ko na nawa ne, da kuma sakon godiya a farar takarda mai dauke da kalamai na godiya da saka albarka.....wanda hakan ya saka Anna farin ciki matuka suka hade suka kai bangaren Aban yara, wanda shi tsoro lamarin ya bashi, har ya kasa tabawa, haka ma auntyn yara, karshe suka roki anna ta ajiye komai a wajen ta, su idan suka amshi abubuwan nan ma su kai su ina?, su kam sun yi addu'a Allah ya bada zaman lafiya, daga nan iyayen mata baki suka hade suka mayar da sauran amaren dakunansu hadi da kayan kowace, wace ita ma sai a lokacin suka je nata gidan, wato Nur suka kai nata sakon..............sannan suka ganta suka yi musu addu'a suka wuce tare da sheda masa a gobe gobe zasu juya, sai sun kai musu ziyara, daga nan suka rabu da juna suka bar shi ya ci gaba da kula da lafiyarta cikin tsantsan kauna da girmamawar junna.

Sai da yayi kwana uku cir bai je cikin gari ba, daga masallaci sai gidansu, inda ake kawo musu abincin rana da na dare a kan lokaci, na kari kuwa shi ne yace shi dai a bar gidansa kar a kawo na kari, domin ana hana musu barcin safe, harma da yan tsotse tsotsen da yake tabawa na dafen, dan kuwa tunda ya samu haja sau daya ba'a kuma baje masa harkar ba, shi da kansa ya daga kasa ne ya bada dama domin kuwa farkon shiga dole sai da lalabawa, Ama kuma sauran jikinta babu inda bai saba da shi ba zuwa yanzu, kawai cen din ne baya zuwa yake barinta , hakan ya sa ta kara sakin jikinta da shi sosai...........

A yau da suka cika kwana bakwai ne ya shirya ya fita bayan ya sanar mata inda zai je, wanda tunda ya fitan sai kawai ta zauna da waya suna call bayan ya gwada mata yadda zata yi, ya haɗa mata call da A'isha da Farhana, zuciyarta cike da tunani da tarin tsoro a yau da ta tuna ba fa nata ita kadai bane, ba fa malakinta ita kadai bane, sai kawai du wata walwala Tata ta rasa har ma ta wuni da zazabi da tarin kasala da tunanin inda yake, domin wasa wasa dai da dare yayi, har a lokacin da aka zo aka buga mata sashen nata ta dauko hijabin da ta wuni tana sallah da shi ta je ta bude, sai ta ga matar Aliyu ce ta kawo mata abincinta, hadi da gaisheta sosai har ma ta kara yi mata Barka da shigowa ahalinsu, sannan ta sanar mata zasu koma domin Aliyun zai koma wajen gine ginen da ita bata ma san ko na meye ba, ta juya ta tafi ta barta a nan

Wanka ta je ta yi, cike da jin matsananciyar kewa, ta cenza sutura ta sake feshe jikinta da dakunnan da turaruka masu dadin kanshi, sannan ta zauna a falon hadi da hade kanta da gwuiwarta ta fara kuka, domin zuwa yanzu karfinta ya kare da tunani da bugawar zuciya, haka kuma sai take tunanin ta yiwu ya koma wajen matarsa ne saboda ai ya gama yi mata satin amarcin da ake yiwa amarya....Shikenan wayo ya mata yayi tafiyarsa??????????

Bata taba tunanin kishin ta ya kai haka ba sai yanzu

Sai take ganin bata yiwa kanta adalci ba

Sai take ganin kamar ta matukar cutar kanta da har ta saka wannan damuwar mai girma a zuciyarta

'Ya Allah, da matarsa fa na same shi, matar da ta ringa fada saboda kishinsa, ashe haka take ji ya saka ta fada? Ashe tana da gaskiya da take jin haushina? Ita fa ta dauki shekaru da shi tun bani da isashen wayo kenan fa, ya Allah ka sassauta min abinda nake ji da zazafan kishin mijina , ka bani ikon kawar da kaina a komai fa ya shafi iyalinsa, ya Allah ka sassauta min zafin kishi' abinda take ta maimaitawa kenan, har ta ji ana murda ky alamun za'a shigo
Chapter 131 · 0% Book details