← Book details Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 95 OF 141

Sashe 95

Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

FARHANA dake dubansa cikin ido a lokacin da ya furta " Bab" ne ta sada kanta wasu irin hawaye suka bale mata ta sake bin yan matan nan da kallo , ta gane yarinyar da yake ce mata kanwarsa ce, wace idan suka zo daukan sako take fitowa ta yi ta hararanta ta dake dubansa lokacin da ya miko hannu zai kama mata hannu ta daga hannun ta cire shi da mari rai bace ta ce" Idan ka yarda ka taba min hannu sai na batar da kai a kasar nan Jafar!"

Budurwar nan da du ta fi dayar rawar kai ta zaburo zata mari FARHANA, Nur ta rike hannunta da karfi ta watsar da shi ta duka ta cire takalmin nata mai tsini ta juya inda ango da abokansa suke rike shi suna tausarsa ta ce" Dan iska mayaudari, bari ka gani sai dai a maka auren da ido daya yau"

Da sauri Aliyu ya juya da nufin neman izinin zuwa ya taho da su, sai dai yana juyawar ya ga ya bude ya fita daga motar, a lokacin da daya daga cikin abokan angon nan yayi raf da takalmin daya na Nur yake kokarin yi mata zobe dan ya kwace takalmin ya tatakata a wajen domin ya gane yar geto ce a daku ba zai ce mata komai ba, ya karaso da saurin da shi da kansa bai san yana da shi ba!

Yana zuwa dayan takalmin da ta wawuro na A'isha bayan tace mata" Indo ba zaki bani takalmin naki ba,? Dan iska ya fasa Ni da kai, sake min takalmina....."

Tana dagowa ta ji an kama hannun nata daya, mai dayan takalmin an masa matsar da ya sa ta sake shi, dayan da ta duka ta dauka kuwa an yiwa hannun irin dokewar nan dake sakawa a saki abu ba'a shirya ba, sannan aka hade hannayen nata biyu a waje daya aka yi musu curewar da ta sa bayan tsoratan da ta yi itama na ganin wanda ke yi mata wannan aikin, har azabar hakan ya sa ta duke tana fasa ihu bayan ihun da Farhanan ta saka , A'isha kuwa ta zangaya a guje ta nufi motar da suka zo da ita ta shige baya ta boye kanta jikin ta na rawa........

Tisa keyar Farhana Aliyu yayi, wajen kuwa tunda suka ga iko suka shiga watsewa, ciki harda angon da ya gudu a lokacin da ya ga Sir IMAD a filin nan, jikinsa na rawa kamar zai suma.........

A duke take, jikinta na rawa, gaba daya tana neman fita a hayacinta saboda bata taɓa ganin fuskarsa na huci irin haka ba sai yau..........

Aliyu da ya kai Farhana mota ne ya juyo dan tisa keyar wannan jarabawar ta ogansa, a lokaci daya ya ja ya tsaya yana zarro ido sakamon abinda idnanuwansa suka gani, a lokacin da kamilin, ustazun ogansa ya daga yarinyar nan ya loda a kafada sannan ya juyo ya nufo motar da ita a lokacin da take ihu tana haharba kaffafuwa , a lokacin da ya karaso inda Aliyu ya bude masa a tsorace, ya dana ta cikin motar , sannan ya duko inda take ihun nan da kakkausar Muryar da bata taba sanin tasa bace ya ce"

Innalilahi, ku zo mu je mu taya amshe ya'yan Anna, wayo yau mun higa taraKissan mumuke page 57

A mugun kausashen da bata taba sanin amon muryarsa na iya fita a haka ba ya dan rage tsayinsa ya dauke abin dan kwalinta da ta rufe fuskarta da shi ruf ya furta " Ki kama min bakin ki, ki zauna, shi ne abinda zai hana ni jan motar nan in nutsa ku a kogin da ruwa zai dauke muku numfashi..........!" Ya ajiye maganar da dan karfin da ya sa Nur bayan zarro idon da saka idannuwanta cikin nasa , ta kai hananyenta ta kankame bakinta hadi da mikewa da sauri ta ɗora kanta a kirjin FARHANA ta rukunkumeta hadi da sake rintse ido

Motar ya kama ya buga da karfin da ya sa FARHANA sake rufe ido ruf jikinta na rawa.....
Yau kam ta san ta mutu ta lalace, a yanzu Bama ta bikin zuciyarta take ba, ko daya, a yanzu ta gagarumin tashin hankalin dake gabanta take........

Zagayawa yayi ya bude motar ya shiga gefen direba.

Aliyu kuwa, da sauri ya je inda A'isha take ya bude a hade ya ce" fita ki koma cen"

Da sauri ta fita ta koma jikinta na rawa ita ma

Juyowa yayi inda Anas ke tsaye hannayensa saman kai ya je daf da shi ta yadda ya kure masa waje sosai,

A kausashe ya ce" A yau da baka da kusanci da Sir, da sai na gigita maka rayuwa na koya maka sanin darajar aikin ka!, ama a haka ma ka bata rawarka da tsalle saboda ba zaka kuma yin aiki a mention IMAD ba, ka kai min ky garage !"

Daga haka ya juya da sauri ya shiga motar nan ya tayar

Jikin Anas harta kwakwaluwarsa rawa suke yi,

Idan akace ya saki fitsari a wandonsa ma ba za'a yi gardama ba

Jiki na rawa ya shiga motar nan ya take ta ya bi bayansu , yana tukin yana hawaye tamkar zuciyarsa zata fita ta bakinsa ne

Innalilahi wa Inna ilaihi raj'une ina zai saka kansa idan ya rasa aikinsa?

'Wayo Allahna' kawai bakinsa ke fada har ya shige get din da sauri yana tsayar da motar ya fita da dan gudu ya zagaya bangaren da IMAD yake ya bude motar ya zube kasa hannayensa bibiyu cikin murya mai dauke da abin kuka da tashin hankali ya ce " Sir dan Allah kar ka bari ya kore Ni, dan girman Allah ka yafe min, ban kai FARHANA wajen nan dan wani abu ba sai dan su fadi sakon Anna, ba halina bane kai ta wajen da ba'a ce ba, dan Allah ka yi hakuri Sir"

Rai bace Aliyu ya bude ya fito a rana yana tunanin Yauwa an zo wajen da yake so, wato wajen da zai tataka yaron nan la'ada waje

Sai dai yana zagayowar IMAD ya masa kallo daya , sannan ya sauko daga motar ya zagaye shi ya nemi nufar bangaren Anna

Kuka ya saka da ƙatuwar murya irin ta gardi, hakan ya sa Anna da kofofin window din ɗakinta suke bude gaba daya zabura daga saman gadon ta da take zaune tana duba takardun dalibai ta leka ta window da sauri

Idannuwanta suka sauka a kan ANAS da ya rarafa da sauri ya sake bude baki yana kukan nan ya furta" OGA, dan Allah dan annabi ka yafe min, oga da aikin nan nake ciyar da mahaifiyata da marayun kanaina, da aikin nan nake kula da dangina, dan Allah ka rufa min asiri kar kace zaka kore ni saboda laifin nan, OGA na rantse maka gabanan idan me zasu ce ba zan kai su inda suka ce ba in ba na amshi umarnin daga hannunka bane!"

Kasa hakura ta yi, irin yadda Anas ke kukan nan hankalinta ya gama tashi da tunanin idan har korarshi zasu yi saboda wannan kenan ita ta janyo masa wannan masifar? Ai gwara ita su hana ta shiga gidan su da su kori Anas.....

Da sauri ta tsallake A'isha ta fita daga motar da dan sauri ta karasa inda ya tsaya yana kallon Anas........., kawai bakinsa ne ya kasa budawa ya masa magana....................

Wuce Anas din ta yi kadan kafin ta nemi karasawa daf da shi kadan

Sai dai tana dan matsawar ya daga rinanun idnanuwansa ya sauke a kan fuskarta, wanda hakan ya sa lokaci daya ta daka birki , sai dai idannuwanta a yanzu suka ciko da kwallah, da kuma dana sani ƙarara a kan fuskarta

Hananyenta ta hade, ta bude baki da farko, sai dai irin abin nan na jarirai da baki ke musu bari idan zasu fashe da matsanancin kukan nan bakinta yayi wanda ya sa ya sauke dubansa a irin yadda bakin nata ke rawa...........

Ta sake budewa wannan karon harda rintse ido da karfi kafin ta furta" dan Allah, dan Allah kar ka kore shi.........., ba laifinsa bane, ba laifin kowa bane, laifina ne........., Ni ce nace mu je mu ganshi....., ni ce duka na aikata haka, dan Allah kar ka ga laifin kowa, kar ka kori k............"

Da sauri ta hadiye maganarta sakamakon sauko da ƙafarsa daya da ya fara haudawa matakalar da zata kai shi falon Anna da yayi........

Sai ya zamo yana sauko da ƙafarsa tana mayar da Tata baya........., ya zamo sai da ya sauko gaba daya kuma ya yi takun da ya matse mata waje har ya zamo ta rintse ido tana jiran jin saukar mari, domin zuwa yanzu ta san cewa ya gama tsanarta , komai zai iya yi mata ne ......sai ta ji shirunsa yayi yawa, shirun nasa yayi mugun yawan da ya sa ta ɗan bude idannuwanta......, sai dai tana budewar sai da ta yi dana sanin budewar nan domin sai da gabanta ya tsinke ya fadi sakamakon ganin fuskarsa dan daf da Tata, idnanuwansa cikin nata.........sai dai a yanzu bata san wani irin duba bane wannan.........

A hankali ta bude bakinta, muryarta cen ciki sosai ta ce" Ni ce ya dace ka hukunta, Ni ce ya dace ka kora ba shi ba......m"

Bakinta ya zubawa ido............, kafin ya sake duban fuskar ta............

A hankali ya bude bakinsa ya ce" Na ce zan kore shi ne?......."

Ya yi shiru yana lumshe idannuwansa da sauri saboda du alamun wanda ke Daf da yin hannu daya kafa daya sun gama bayana a tare da shi, yana ji a ransa idan bai yi gaggawar ganin likita ba komai na iya faruwa da shi......., dan haka ya dan ja baya ya sake zuba mata ido bai sake ce mata komai ba ya sake juyawa ya kuma haurawa yana kokarin budewa ya shiga Anna ta bude ta fito
Chapter 95 · 0% Book details