Sashe 126
Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da mamaki Inna da hannayanta ke dan rawa irin na abin tsufa ta kame haba tana duban Anna kafin ta waigo wajen Malan baba ta ce" Ka ji tsiyar zamani ko? Ka ji yarinta irin na yarinyar nan ko?, ita dai ba zata girma ba? Wai su shirya ya'yan, ko uban me zasu shirya su da shi? Ko kuma zuwa za'a yi a yi ta dirka musu maganin mata na zamanin nan na masifa yan mata da su a cushe musu mahaifa a zo ana fama da ganin likita kafin ya bude mahaifar? Wani shiri ne zaku yi musu? Dinkuna kuwa kafin su fara fitowa daga gidajensu ai sa saba da mazan sosai ko?, ko so kike yi ki ce min yawon dangi zasu yi tun gobe? Aure an daura shi, ga maza a kusa a je a yi abinda ya dace mana , ko me kike son ce min kike jira da maganar raya sunna?????"
Da sauri Anna da ta mayar da kai kasa take girgiza kai tana hade hannayanta da son bada hakuri,
Ama Inna ta ringa masifa tana karawa ta sake duban su Aban yara da suke ji ina ma da hanya da kowa ya ba ƙafarsa iska ya gudu daga gaban baiwar Allahn nan mai tsage bayani ba raba koda gyauto ne
Inna ta dubi zaratan mazan da hasken wajen da ya hade da nasu hasken suke sheki da kanshi ta ce" Imadi, AKOY matsala da wajen da zaku saka matanku ne?, idan ba gidajen da zaku saka su ne Shikenan sai su kwana daya jal yau a wajena garin Allah na wayewa a fashe min asusuna a je a siya musu wajen zama , dan babu wanda zai yi wannan rashin da'ar da ni a daurawa ya'yan aure kuma ace wai tarewa sai nan da sati, zawarawa na baku hala???"
Har ga Allah sai da ya karewa bakinta kallo, kafin ya mayar da kai ya kima a kar ya ki cewa komai, ...........sai Abdallah ne ya dubi Abdul bassit kasa kasa ya ce" Ka ce wani abu mana"
Abdul bassit ya tabe baki ya ce" Ni fitsarare ko?............"
Abdul Fatah ya dubi Sulaimana ya ga ya ki dagowa , bayan da shi aka hadu bayan sun so dakuwa shi da IMAD a lokacin da suka ce masa ya zo a je a duba gidaje saboda a yau suke so matan nan su tare, yace ai shi dai yayi gini, kuma sai ya yiwa Nur kayan daki da A'isha koda zasu tare ne Imad yace masa kayan daki kuma? Shi ne yace eh ai babu yadda za'a yi ya bashi kanwarsa bai mata kayan daki da Gara ba, hakuri za'a yi har yayi sannan a tare, shi ne Imad yace ba damuwa, an hakura, Ama shi ma babu inda A'isha zata je sai lokacin da ya gama tunani da yarda cewar eh ya dace da auren tasa kanwar shima, a nan ne fa SULaimana yace yaushe A'ishan ta zama kanwarsa?, bashi da hurumin hana masa matarsa, IMAD yace ok, su zuba su gani idan yana da hurumin ko bashi da shi, karma ya rainawa mutane waye ya kama bakinsa dan yana iya sakawa sai ya sakar masa kanwa, A'isha ba kanwarsa bace, matarsa ce, kuma ko an kai masa ita sai ya kwato abinsa bale ba'a kai ba......., ganin dai zasu ciwa juna mutunci ya sa suka zaunar da su suka nuna musu hakan bata gyara su, gwara su sasanta junna su gane halin da suke ciki sannan a kai ga haka....., a nan ne ya amince da maganar gidan bayan sun saka manya ciki, sannan suka je suka duba gidajen suka sa aka shiga saka kaya da duk abinda ya dace, gidaje uku ne jere.........sannan suka dawo gidan Anna, Duda shi IMAD a ransa ya kudurta bayan an kwana biyu idan ta gama sabawa zai maidota inda Anna take ne, haka yake ji a ransa Anna na raye bashi da wajen zama nesa da mahaifiyarsa da ko wacece.
A hankali Abdul Fatah ya ce" Sulaiman, me zaka ce? Kawai a barsu din sai nan da satin ko?"
Ido ya zarro a kallon kasan da yake , ya dago ya dubi Abdul Fatah, ya dubi IMAD, kafin kasa kasa ya dan mintsini hannun IMAD cen kasa yace" A bani matata ni dai, to ko a gidan Aban yara ai ma zauna bale da gatanmu?"
Malan na Magarya me zai yi banda dariya yana duban Sulaimana ya dubi Inna ya ce" Shakiyi bai iya rada ba, muma a kauye ai ba'a daura aure ba'a tare ba, sun je sun gama lalurar gidan, a basu matansu kawai, Allah ya basu zaman lafiya, a yi hakuri Hajiya ko wani irin shiri ne sai a bi su da shi daga baya....., ko kuwa? Mamansu? Auntyn yara ko baku amince ba? Idan sun kiya hakura za'a yi ai iyayen nan mata su ne da komai"
Auntyn yara kara boye fuska ta yi, ita fa sai da ta ki zuwa zaman nan, Anna ce tace wallahi sai ta sauko, tun dazu da suka haura sama suka samu yan matan nan suka yi musu nasihar da ta sa su duka kuka daga yaran har su iyayen, da kyar Mama ta rarashe su, hadi da ɗora nata nasihar kan zaman aure, da girman hakuri, da biyayya wanda shi ne kawai abinda zai sa auren dadi da kuma dorewarsa, kwarai ta nuna musu kowace mace sai ta yi hakuri a dakin mijinta, kowace mace sai ta yiwa mijinta biyayya in dai ibadar auren za'a yi, in dai aljanar za'a nema, in dai zaman lafiyan za'a nema, kwarai ta nuna musu girman darajar mazansu a yanzu, kwarai ta nuna musu girman tsafta da iya girki da kiyaye duk wani abinda yake na masu gidajensu, kwarai ta nuna musu darajar sirrin aurensu, sannan ta rufe da sake yi musu nasiha da juriya da hakuri na zamantakewar aure......, to tunda suka fito ta so guduwa bangarensu Anna tace atafau su zo su tayata yaki da maganar tarewar yan matan yau, dan ita fa bata shirya yaran ba, so take yi ta shirya su sosai, bale Nur mai kishiya, ta nuna ita tana so ta musu shiri irin na gararin nan, wanda hakan ya sa Auntyn yara jin kunya sosai, tace ita dai babu ruwanta, Ama Anna tace Allah sai ta tsaya, Gayanan Malan na Magarya na son sakata a maganar shi ma, bayan irin yadda wannan yaron marar kunya ya budi baki yayi magana shi da bai iya maganar sirri ba!
Inna ta ce" Ai ka barsu wadinan, bakinsu daya, bari in je cikin a sauko da su, ba fa wace zata kwanan min a gidan nan kuma, Allah ya bamu alkhairi"
Tarin gajiyar wunin yau ya sa ta mike da kyar, hakan ya sa Anna kamata ta talaba ta, sannan su Mama suka mara musu baya suka shige elevator suka haura sama
Dan shiru wajen ya kara dauka kafin uncle yayi murmushi ya dake duban samarin a tausashe ya ce" Dama, ba zan so ace sai daga baya a kai yan matan nan dakinsu ba ko ni, sai dai na so ace an kai gobe saboda isowar iyayenku a yi musu gatan da ya dace..........., Ama a yanzu ma ba zata gagara ba, babu abinda na dauke muku......, ba zan yarda iya aljihunmu ya shiga harkar aurenku ba, kowane zai yi bajinta da karfinsa ya saka abinda Allah Ya hore masa .....in sha Allah a gobe idan aka dauko su aka kawo su saboda taron da za'a musu na tarbar cikin ahalinmu, zan amshi kyautukan da zaku musu......, babu na wanda zamu raina, Ama kuma babu wanda zan yarda waninsa ya ba matarsa, ina fata kun fahimta?"
Malan na Magarya ya gyada kai da Larabcinsa ya furta" Lah shaka...........lah shaka"
Aban yara ya Dube shi yayi murmushi yana girgiza kai, shi ai bashi da ta cewa a gaban bawan Allahn nan, sumul ya masa da suka iso kafin a shige masallaci harda cewa ko dai yana cikin WA'INDA Allah ke nufa da arziki suna gocewa? Ce masa yayi to da yake nokewa ai kowa a duniya bauta yake dan aljanna, haka ma samun alkhairi shi ne abinda kowa ke so a duniya, idan ya san ya shirufce ya kauce a yi a gama..............
Malan baba ya furta" Haka ne kam, Allah ya bada iko, sannan kar a yi wasa da nasihar da aka yi muku, ya'yan nan amana ne a hannayenku, kar ku yi wasa da ita, idan kuka yi wasa da amanar nan, Allah sai ya kama ku da shi!"
Sun ci gaba da yi musu nasiha, har elevator din ya sake budewa
Tsakani da Allah sai da IMAD ya ji gabansa ya fadi, a hankali ya dan dago idannuwansa yana son satar kallon ta........sai kuma ya mayar da kan nasa kasa ya sada cike da jin wani abu a ransa, saboda kukanta yana ji har cikin zuciyarsa, Duda ba ita kadai ke kukan ba, nata ya fi ratsa masa zuciya
Gurfanar da su aka yi gaban iyayensu maza, a tausashe suka sake yi musu nasiha hadi da saka musu albarka sannan Anna a tausashe ta ce" Na da Aliyu fitar da motar da zata daukesu su duka, da kuma WA'INDA zasu raka su....., sannan da motocin da zasu daukar musu yan kayan bukatu......., ina fata an saka masu gadi da masu tsaro????"
Abdul bassit ne ya ce" Eh Anna, wannan duka mun gama............, masu aiki kuwa dama mun ce ne sai daga baya saboda a barsu su ..........."
"An gama komai!" IMAD ya fada yana katse masa hanzari hadi da sakar masa duban da ya saka shi yin tsitttttttttttt.........
Kai Anna ta gyada sannan suka mikar da su, suka nufi fita da su, wanda Nur ta rarafa da sauri ta kama kafar mahaifinta ta ɗora kanta tana girgiza kai a hankali ta ce" Abana, ina za'a kai mu kuma? Abana a'a"