Sashe 98
Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
IMAD da ya sauka, ya samu Mutalab yanzub a zaune, FARHANA a nesa kadan da shi, A'isha ma a zaunen saboda ta so fita, Mutalab ya kiya yace ta zauna , magana zasu yi....., kuma ya ki yin maganar yana ta kallon hanyar elevator har sai da ya fito suka yi ido hudun da ya sa ya zuba masa ido kamar yadda ya Dube shi kafin ya daure fuska ya ficewarsa ba tare da yace musu ufan ba
Yana fita Mutalab yayi dariya a tausashe ya ce" He is in love.........."
A zabure suka juyo su duka suna kallonsa
Mutalab ya dan dage kafadu yana doka murmushin da ya sa FARHANA dan matsawa kusa da shi kadan tana zarro ido ta ce" Ya Mutalab, me kace?, kamar yaya? Na wa?????"
Yana murmushin nan ya kai yan yatsun sa biyu ya dinke alamun ya rufe bakinsa ba ruwansan nan, kafin ya tausasa muryarsa ya ce" Me yasa bakya so na?"
FARHANA ta zuba masa ido, zakuwar da take yi ta koma cikin cikin ta, a hankali ta sada kanta,. A'isha kuwa sai kawai ta mike ta yi gaba kadan tana lumshe idannuwanta cike da jin wani dadi a cen cikin zuciyarta...........
To ai magana ta kare
Ita gani take yi komai ya zo musu da sauki ma, tunda hukuncin ya sauka a kan maganar yi musu aure??????????, kuma ya zama kowace cikinsu da tsayaye? Ai shiKenan baban yaya Allah ya saka maka da alkhairi......, Ama me maganar Mutalab take nufi ne????, Duda ita da kanta tana da manyan tambayoyin da suke mata yawo a kwakwaluwarta a kan lamarin nan, sai dai ba zata yarda ta yiwa kowa ba saboda magana ce mai girma a kan mutun mai girma......., Duda ita sam bata ga daukowar da aka yiwa Nur ba, tana dai ganin wasu abubuwan ne da idannuwanta suka gani hankalinta ya kai wajen.
A tausashe ya ce" Kina tsoron kar in yaudareki ne? Ko Bakya son aurena in kai ki nesa da Anna bane.....?........ Farhana kina tunanin yayanki zai bata lokaci wajen turo maki saurayi ne? Kin kuwa san waye yayanki?, kina tunanin ba zai iya daukar maki matakin hadaki da wanda yayi niya a lokacin da yayi niya bane har sai ya maki zagaye zagaye?????, FARHANA ki Dube Ni, ko kina tunanin bani da wani abin da zan iya baki a gidan auren mu ne????? Ki Dube Ni plz"
FARHANA sai ta ringa jin jikinta zai dauki rawa.............
A dan tsorace ta saci kallon sa, wani irin nauyin daga ido ta dubi nasa ta ringa jin yana damunta, abinda bata taba ji da kowani namiji ba, aboki ko masoyi
A tausashe ya ce" Ban miki alkawarin a rayuwa ba zamu saba ba FARHANA , ban miki alkawarin yi Miki biyayya a rayuwa a kan komai na, Ama na maki alkawarin idan mun samu sabanin zan zamo mai sauraron bayanan ki zan zama mai yi Miki uzuri, mai yafiya a gare ki, sannan zan nemi afuwarki idan na bata maki, FARHANA zan nuna maki kauna irin wace addininmu ya tanadar mana ......, zaki zauna inda kike so a lokacin da kike so......., ki yarda da Ni, Ni mai son ki ne........ki aminta a yi mana aure.........."
Wani irin murmushi ne ya kwace mata, ta dago ta dube shi har sau biyu kafin ta mike da dan gudu ta nufi hanyar elevator.........
Dariya yayi kamar yadda A'isha ta yi har hawaye na son bale mata kafin ta nemi bin bayanta .....sai dai Mutalab ya dakatar da ita ta hanyar fadin" A'isha zo"
Zuwan ta yi, ta duka daga dan nesa tana fadin" Na'am????"
Shiru yayi na dan lokaci, kafin a tausashe ya ce" A'isha, ya dace ku yi iya yin ku, ku nesanta Anas da NUR........................, saboda wanda ke son Nur ba tsaran Anas bane......zan iya cewa ban taba ganinsa a soyayya irin wannan ba, Ama a yau zan sanarwa WA'INDA suka isa su tunkare shi da abin tun kafin ya fi karfinsa su saka shi ya dubi lamarin tun kafin ya saka shi fara aikata abinda ya fi wanda ya aikata a yau......plz ku nisanta NUR da ANAS dan samun kwanciyar hankalin kowa kin ji?"
A'isha ta rasa amsar da zata bashi, kuma tana so ta yi tambayar waye wannan? Ama ta gaza saboda gani take yi kamar Mutalab ya fi karfin ta tsaya yi masa tambayoyi irin wadinan........., karshe ma mikewa yayi ya mata Salama ya barta cike da tarin tunani har sai da su Anna suka sauko suka sameta zaune suka dunguma bangaren Mama gaba dayansu , Anna na niyar idan suka ga mama suka yi fira sosai sai ta sa a kai su gidan su Nur din kafin ita ta zo, dan ba zata iya fitan ba , bata ji yaya jikin nasa ba......, hakan ya sa ta yiwa direba magana dan ta ce da ANAS yaje gida ya huta, sai sun zauna da IMAD kan maganar ANAS ta kara tausarsa ta nuna masa ba halin yaron bane haka, an yi kuskure yanzu, kawai a yi hakuri a tarbi gaba, ba zai kuma ba.
A bangaren IMAD kuwa clinik Magori Aliyu ya kai shi
Suna zuwa suka shige da motar su har wajen ajiye motoci, sannan ya fice ya nufi inda doctern ya fada masa, a nan ya hadu da wata nurse ta yi masa jagora suka haye har ofishin likitan dake jiransa, domin ya tashi tun Dazu, msg din IMAD ya saka shi zaunawa yana jiran zuwansa
Bayan sun gaisa IMAD ya zauna yana duban kayan aikin Docter kafin ya maida dubansa kansa a lokacin da ya ce" Me yake damun uban gidana ne?"
IMAD yayi murmushi ya ce" Abokina kai ne oga........."
Shi ma yayi yar dariya yana girgiza kai hadi da sake fuskantarsa da kyau ya ce" Me yasa kace kana son ganin likitan zuciya? Me yake faruwa ne?"
IMAD ya dan sauke ajiyar zuciya yana dubansa a nutse ya ce" kai zaka fada min, domin Ni ma ban sani ba......., ina fama da yawan bugawar zuciya kwanakin nan, zaka ga har zufa na keto min........, kar aje shigar ciwon zuciya ne ban sani ba"
Mikewa docter yayi yana daukan kayan aikinsa ya ce" Ok, gwara da ka zo da wuri, Bismillah bari mu yi gwaje gwajen da ya dace"
Dukan wani gwajin da ya dace ace an yi masa sai da likita yayi, gaba daya result din da aka samu masu kyau ne wa'inda sam basu nuna wani damuwar da zai sa a ga wani ciwon da ya shafi zuciya da ma abin numfashi...........
Da kula likitan nan ya ce" Sir, dukan gwaje gwajen ka fa lafiya lau ne, zan iya cewa a shekarun ka kana da lafiya sosai fiye da wasu masu shekarun ka, saboda irin yadda jini ma ke gudu a jikinka na maji karfi ne , kana sport ga dukan alamu kuma kana kiyaye abincin da kake ci..........., ama ko zan iya gane wasu lokuta ne kake jin irin haka?, misali cikin barci kake zabura da shi? Da sasafe kake farkawa da shi?, idan dare yayi kake jin sa?, idan kana cikin tafiya ta gagawa kake jin sa?, ko kuma idan ka zurfafa tunani , misali idan kana cikin damuwa sosai kake jin sa?"
IMAD yayi shiru yana ta tunanin amsar da zai ba likita
Wacece amsar da zai ba likita ne???
Me zai cewa likita?????
To shi da kansa a yanzu ne ya gane idan ya ga yarinyar nan ne kawai yake tsintar kansa a irin wannan yanayin........
Ama me ya sa haka????
A tausashe ya ce" Docter, du ba a irin lokutan nan bane, ...........ama mutun na iya samun kansa a haka in ya ga wani abin da............wani abin da zai iya hadasa masa hakan?!?"
Docter ya sake fuskantarsa, tambayar bata fito yadda yake so ba, Ama sai ya gyara zamansa ya ce"Sir, idan mutun ya ga abinda ya mugun tsoratar da shi, ko ya hadu da wata situation dake sakawa ya ji faduwar gaba, misali ko wani launin abin dake tuna masa wani abin da ya shaku da zuciya, ko wani abin da ya faru da shi mai girman da ya zauna masa a zuciya.......ko wani abin da yake gudun ya faru da shi misali kuma ya san lalle lalle zai faru da shi.........."
Ya dan dakata saboda du bayanan da yake iya badawa yake harhadawa wa'inda suke iya hadasawa mutun faduwar gaba ne, ko bugun zuciya ne, da sauransu
Ya dora da fadin" ko kuma mutun ya rasa wani baban dukiya haka , ko rashin mutun haka.........harta soyayya, misali idan zuciya ta kamu da abinda take so zaka ga zuciya na bugu da abinda ya fi karfin misali.......du abubuwan nan na iya hadasa haka, a cikin su babu wanda ka fuskanci shi ne damuwarka?"
Ido ya zuba masa........, gaba daya sai ya ga kame kame abin ke neman komawa
Da kula ya ce" Docter yanzu a gwaje gwajen da ka yi baka ga komai ba???"
Likita ya tabbatar masa cewar shi kam bai ga komai ba
Kai ya gyada hadi da sauke ajiyar zuciya kafin ya mike su yi Salama har ma likitan ya taka masa har wajen mota ya shige suka yi Salama ya jinginar da bayansa a jikin motar wani irin sake sake na shigarsa, cike da tarin tunani mai nauyin da zuciyarsa ke neman girgiza wato to in kuwa duka kaf ba daya cikin abinda likita ke nufi ko dai Mayu ke son kama shi???????, lokaci yayi da zai sanar da Anna ko ta fara yi masa addu'a saboda gujewa harkar Mayu kwarai da gaske....., a lokacin ne yayi kiran Numbar Anna dan ya sanar mata cewar zai biyo ya dauke ta, domin tuni yaran suna cen gidan su yarinyar nan, su je su ga iyayen nasu sai su wuce gida......., a yau ko bi ta kan komai bai yi ba da ya shafi kampani da sauran su...................hm!.
_______________________________