Sashe 49
Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Subahanalah, me ya faru ne? Na ji ana maganar waya barauniya ta shigo gidan ta dauki waya ne? Wannan shin ba mama bace? " Anas da ya mike tsaye yana duban Nur ya fada da tashin hankali sakamakon yadda ya ga ranta yayi mugun ɓaci
Kamar an tsoratar da ita haka ta juyo ta Dube shi, sai kuma ta juya da sauri ta sake bin hanyar da mama ta bi
Murya cen ciki ta ce" Dama ka san ta ne???"
Anas ya gyada kai ya ce" Eh, na santa saboda ta je gida ai tana fada min in fa zo in samu aba dan ya yarda da gaske nake da na zo inda kike, ba wasa a lamurana aurenki nake so"
Zuciyar Nur ta sake wata bugawar, tana dubansa bayan ta zaro idannuwanta waje ta ce" Kana nufin, ita ta je tace da kai haka????"
Yayi dan tsam, saboda a gaskiya shi yarinyar nan kamar wace ta fi karfin sa fa, to sam baya son abinda zai hada masa gwarama tsakaninsu, a tausashe ya ce" Eh mana, ba kukan da kike yi bane bama da Aba yace ba zai bani dama in zo inda kike ba ya daga mata hankali har ta je gidan namu? Dan Allah me ya bata mata rai haka? Waye yayi muku sata?, me aka dauka ne????"
Jiri ne ya nemi kama Imtee, bayan a duniya ita dai ta san bata da hawan jini ko kadan, kai ko iyayenta basu da shi bale ita bayan baya.....................
Da sauri ta duka ta jinginu da garun nan, wanda hakan ya mugun daga masa hankali harma ya duka din shima daf da ita yana dubanta a tausashe ya ce" NUR, wai lafiya?????"
Kallonsa take yi da tarin tunani a cikin zuciyarta......
Ita fa, har ga Allah a duniya abinda zata kiyaye shine namiji ya raina ta tun kafin ta shige gidan sa, to ai shinfidar ce wato zance kafin a yi aure, ta fuskar da ya samu tun a zancen ta nan za'a dore har a cikin gidan, idan har ya ga cewar baki da wata daraja haka zaki je ki kare a shashasha a gidan nasa...... Innalilahi wa Inna ilaihi raj'une, wai mama ce ta je gidan su ta roki ya zo inda take??????
Haka kawai ta samu kanta da dunansa cikin ido ta ce" Ta yaya za'a yi dan kawai mahaifina yace bai yarda da mu'amalata da wani namijin da banma fara sanin so a kansa ba har zan ringa kuka? To ko wanda aka saka min rana ne ai dole zan yi hakuri saboda mahaifina ake magana a kai fa ba wani bare ba!"
Duban idannuwanta yake yi zuciyarsa na bugawa,
Kalamanta idan har ita ta yi su sama sama ne dan ta tabbatar masa darajar mahaifinta a rayuwarta, shi ya dauka da mugun nauyin da har suka sa ya ji tamkar zai fashe da kuka saboda irin yadda ya amshi maganar ba irin yadda ita ta amsa bane, kwarai zuciyarsa ta fada masa kenan baka da wani mahimmancin da zata iya daga hankali idan an rabata da kai take nufi? Ama ai mamanta ce ta fada ko?????
Yanayin fuskarsa ya cenza ainun , hankalinsa kuwa ya nuna tashi kwarai da gaske, yana dubanta shima ya ce" Kina nufin mahaifiyarki zata fadi abinda ba shi ba?, yaya za'a yi ki fada min haka ne??"
Nur da dan sauri ta ce" Ba mahaifiyata ba.........."
Sai kuma ta yi wani irin shiru mai dauke duk wani yinkuri.................
A hankali ta sada dubanta saboda cikowa da idannuwanta suka yi da hawaye, kasa kasa sosai ta ce" Ka yi hakuri yaya Anas, dan Allah ka yi hakuri da zuwa gidan nan, ka yi hakuri da maganar mu...., wallahi yaya Anas ka min ba baka min ba, hasalima ka wuce matsayin yi min , kwarai na karbe ka a zuciyata, Ama jin mamana ta je gidan ku da maganata ya matukar sace min gwuiwa....., shin yaya mama zata dauki lamarina?, yarinyar da komai na kirki bai fara shiga ba har mamanta ta fara bin saurayin da ya nuna yana son ta gidansu? Yaya Fisabililahi kai da kanka yaya ka dauki lamarin da ka ganta? Na tabbata ka yi mamaki ka kuma yi tunanin bamu da wani tsari nagartace a gidan mu ko??????????......, yaya abanmu mutun ne mai taka tsantsan sosai a lamarin mu, wallahi ka ga idan ya ji maganar na amshi wayarka harda kudi ban san yaya zan kwashe da shi ba......., har a kai ga ya ji an tarda kai an roke ka a kan lamarina da kai?????, Subahanalah to mema zai kai mu aikata laifin nan mai girma?????, dan Allah ka yi hakuri!!!!!!"
Ta karashe tana mikewa da nufin shigewa ciki
Tabbas zafin da kirjinsa ke masa ya wuce misali
Yana sunanta idannuwa waje ya ce" Ke NUR, kina auna abu a abin aunawa kuwa? , wani irin in yi hakuri in daina zuwa? Ni kuwa laifin me na maki da zaki hukuntani ta wannan sigar????? Kwarai tabbacin Bakya so na NUR, a bayane komai ya fito cewar so na ne Bakya yi, da ace kina so na da wannan abin bai sa har kin nemi yanke alakarki da Ni ba, wannan wani irin hukunci ne mai tsauri haka????????, haba NUR???"
Nur ta dakata, bata shige ba, bata juyo ba
Yanzu muryarsa da yanayin harzuga ya ce" Ai ba rokona kika yi waya da cenjin da ko a titi ina iya ba wanda ban sani ba, sanadiyar su ba zaki yanke alakata da ke ba!, haka kuma zan fada maki yanzu na fara zuwa, ba ruwana da me mamana zata dauke ki, nine damuwarki kuma a haka kika min, sai na zo gobe!"
Daga haka ya wuce ransa bace ya nufi mota ya shige ya tayar ya dauki hanya ransa a mugun bace
NUR ta jima tsaye a nan har sai da A'isha ta kasa jira ta lekota ta ganta a tsaye a nan
Jiki ba karfi ta ce" Ki shigo gida mana"
Nur ta juyo da sauri ta dauke dubanta a kan fuskar A'isha.....
Yannayin A'isha yayi nuni da wace ta ji abinda ya faru ko?, yannayinta ya nuna cewar A'isha ta ji komai ko???, ya Allah shin A'isha ta ji lokacin da tace mama ba mahaifiyarta bace? Idan A'isha ta ji cewar a yau mahaifiyarta da ta zabeta fiye da ita ne ta budi baki tace ba ita ta haifeta ba ta yiwa yar uwarta adalci kuwa???????..........
Wani nauyi zuciyarta ta dake dauka a lokacin da ta tuna abinda ta sake ambata, wato mama ba itace ta haifeta ba! ........
Da sauri ta ratse A'isha ta shige ciki da gudu ta nufi dakin maman yara ta shige ta hade kai da gwuiwa ta fashe da kuka
Auntyn yara ta sauke ajiyar zuciya ta ajiye marfin tukunyarta a saman tukunyar ta dubi A'isha ta ce" Zo idasa tukawa in samu kanwar nan taki, gaba daya ta mayar mana gida na makoki???"
A'isha ta karaso ta zauna inda auntynsu ta tashi, a hankali ta dubi auntyn murya na mata rawa ta ce" Aunty, in kame bakina shi ya fi alkhairi ko? Saboda uwa ce bani da hurumin fadin wata magana a cikin lamarin ta ko????,....... Innalilahi wa Inna ilaihi raj'une wai wace irin rayuwa muke yi ne a gidan nan aunty? Shekaruna na karuwa......hankalina na sauka kan abubuwan da kwakwaluwata take kin fasara min dai-dai......., me yake damun MAMANMU ne????"
Tausayin A'isha ta kama Auntyn yara ........
A hankali ta duka kusa da ita tana dubanta ta ce" Kwarai, mahaifiyarki ce, ki kiyayi harshen ki a kan du abinda zaki fada da ya shafe ta, saboda tabbas Allah zai kama ki da shi, girman uwa ya fi gaban komai kin ji yarinyata???"
A'isha ta gyada kai kirjinta na zafi sosai
Auntyn yara ta ce" Du abinda zaki gani, ki dauka ba da ke take ba, ba zata taba cuta maki ba, Ni ce na yi mata laifi, a kaina take yi, ba zata taba cutar da ku ba, kin ji ko? Dan na yarda da son da take yi muku, na yarda cewar da da gasken cutar da ku zata iya yi da tuni ta yi, saboda ta fi kowa samun dama a kanku a duniyar nan kin ji????"
A'isha ta dubi aunty da mamaki..... cutarwa? Ta nawa kuma? In ba kwanakin nan ba, wato baya bayan nan harya sallah IMTEE bata tsayar ba, har a kai ga wasu abubuwan da kwakwaluwar mutun mai hankali zata yi tunani a kan hanya mai kyau.......
Imtee fa bata san komai da ya dace da wanda bai dace ba , a yanzu ne ma take ganin kamar kwarai ta fara shiga hankalinta
Mama sai da ta shige jikin Imtee ta yadda a duniya idan kana so ka ga Imtee na kuka to ka taba mama ne , ta gama ganar da ita duniya ita kadai ce mai son ta, ta hanata mu'amala da kowa bale har ta gane rayuwa, ta hanata shiga dangin mahaifinsu bale na mahaifiyarta, ko jiki ake yi a dangi sai dai ita kadai ta je, mama kan cewa Imtee ai bata son zuwa nan da nan......, gwara wanda ke jeji da Imtee domin kuwa gaba daya kwakwaluwarta kayyade mata ita ta yi ta tsayar mata da ita waje daya....., bokon bata barta ta yi na kirki ba, hakama islamiyar........, Imtee tafe kawai take idan ta fito ta kada hankalinta a kan mama..........., Imtee fa hatta pant din ta bata san ta wanke ba dai daga baya bayan nan ta matsa mata take wankewa harma ta gane amfanin wankewar da tsaftace jikin nata......, IMTEE fa horon fitsara da fada mama ta yi mata wanda ya sa bata iya jin nauyin mayar da magana ko cakumar du Wanda ya shiga sabgarta....., to wai aunty mema take nufi ne?????
Murmushi kawai aunty ta mata saboda kallon da take yi mata ta san manufarsa....., ta nufi dakin maman nasu ta shige kanta tsaye ta karasa inda nur take ta zuba mata ido kafin ta duka tana dubanta ta ce" to kukan me kike yi kuma? Fada kika yi da bakon naki ko meye????"
Nur ta dago tana duban mamanta.......