← Book details Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 109 OF 141

Sashe 109

Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abdul bassit yayi gaggawar cewa" Subahanalah, ina ita ina taba lafiyar jikin ta? Ai ina ga tana da ilimin da ba zai bari ta aikata haka ba, kawai dai gyaran ne, a barshi a gyaran, plz kar ka yi bincike a kanta kar ka tabo abinda zai daga maka hankali, Ni fa harkar mata tsoro take bani shi yasa Ni da su mu huta dai-dai Yadda Allah ya hukunta mana, daga wannan Bana musu shishigi"

Imad ya Dube shi, a hade ya ce" Ta yaya zaka iya sakin jiki da tunanin dake damunka irin wannan mai karfi? Idan surgery ta yi, a kan wani dalili? Ta yi ne dan ta burge duniya ko kuwa Ni da nake zaune da ita ne na nuna mata ina so?, ta yi ne dan bata tsoron Allah ko kuwa tana tunanin ba zata mutu ba?, wa yayi mata? Mace ce ta bude ta ba budewar haihuwa ba , ba ta wani ciwon da Allah ya dora mata ba?........., iya wannan ya hana Ni sakar mata jikina...........iya wannan na saka Ni jin kamar zan fita hayacina....bale idan na yi tunanin........nami......nami......"

Ya dakatar da maganar, a hankali ya furta" Ya rab, idan fa namiji ne yayi mata aikin nan?, ta yaya zuciyata zata dauka???"

Da sauri Abdul Fatah ya rike hannunsa yana girgiza kai ya ce" Ka daina wannan tunanin, ka cire wannan tunanin a ranka kar ya hana maka zaman lafiya da matarka......, MAZNA ba zata taba aikata haka ba, ta fi kowa sanin waye kai, ta fi kowa sanin irin yadda kake kafa kafa da ita a komai, ba zata taba zuwa gaban wani namijin ta cire tufafin ta ba, bale har a kai ga aiki irin wannan da ake musu Tik a musu du abinda suka zo nema na neman kyan su........., plz ka cire maganar nan a ranka, Bama zai yiwu ba"

Zai yi magana wayarsa ta dau tsuwa, yar karamar wayarsa, hakan ya sa ya duba ya daga a tausashe yayi Salama

Dan jim yayi kafin ya furta" Alhamdulilah Anna, gani nan zuwa"

Daga haka ya kashe kiran, ya dubi su Abdul bassit da Abdul Fatah ya ce" Allah ya sa....., gys wai yaushe kuka zo????"

Ganin ya nufi wajen turarensa yana fesawa yana magana saka takalminsa plate hadi da dan dubansu ya sa Abdul bassit yin murmushi ya ce" Bamu jima da sauka ba, so muka yi mu maka surprise, ashe kai kana nan ciwon jaraba zai kashe ka, gaskiya ba zan kuma barin ka ba sai na tabbata cewar ana baka abinci yadda ya dace kana ci, ina anfanin wannan rikon amana na matarka tana bari yinwa na neman kashe mana kai"

Murmushi kawai yayi, ya dauke jalabiyar ya dauki karamar riga ya saka a ciki sannan ya dora jalabiyar a sama, dama jalabiyar baka ce sidik mai kauri sai kawai ta yi mugun hawa jikinsa da fatar jikinsa ta masa kyau

Shi ya fara yin gaba ya bude kofar dakin ya fito

MAZNA da JAUHARA dake zaune kusan a tare suka mike,

Da sauri MAZNA ta nufo shi, fuskarta ta gama yin hulu hulu na abin kukan da ta sha,

Tana zuwa ta nemi rungume shi, a hankali ya kama hannayenta ya rike yana tare ta kadan hadi da sakar mata murmushi kadan , wanda ya ba aminansa damar ficewa ba tare da sun tsaya sun kalli komai ba

Sai bayan sun fita a tausashe ya ce" Kuka ne kika yi ?"

MAZNA ta karasa jikinsa saboda a yanzu bai tare ta ba, a hankali tana shashekar kuka ta rike shi a jikinta kam cikin abin kukan ta ce" Na Tsorata, har yanzu jikinka da zafi Akul, dama baka da lafiya jiya Ama ban sani ba?"

Murmushi yayi, a hankali sosai ta yadda Jauhara ba zata iya jinsa ba ya ce" Bani da lafiya, kuma ke kike son kashe ni"

Gabanta ya fadi, ya fadi sosai , ta zuba wa fuskarsa ido dake kara kawatuwa a idannuwanta, da sajensa mai matukar daukan hankalinta......, a hankali ta ce" Me yake damun ka"

Duban da ya mata na cikin ido ya sa tsigar jikinta motsawa, domin duba ne mai aikawa da tsananta j bukatuwa, mai fassara cewar idan ita ta zama abin nan zai iya cinyeta tassss tsabar yadda ta barshi da ƙishirwar dake neman lafiyarsa

Kanta ta sada, tana rike da hannunsa ............., jikinta ya mugun mutuwa, komai nata ke neman dakatar da aiki

Murmushi kawai yayi ya janye ta daga jikinsa ya karasa falon yana duban JAUHARA da ta sake mikewa tana gaishe shi hadi da tambayarsa jikinsa

Kasancewar bai taba tunanin zata iya yiwa JAUHARA fira irin wace suke tattaunawa da ita ba, ya sa a sake ya amsata har ma ya Dube ta da kula ya ce" JAUHARA, a manema aurenki, kina da wanda yake shirye da fitowa aurenki ne?"

Jauhara ta yi shiru na dan lokaci kafin ta girgiza kai ta ce" Big broth a'a"

Ya Dubeta da mamaki , sannan ya dubi MAZNA ya ce" Ba kin ce min tana da saurayi ba?"

MAZNA ta sauke ajiyar zuciya a tausashe ta ce" ka dan lamarin JAUHARA Akul, ta yiwu sun rabu Ni ban ma sani ba"

Kai ya gyada, kafin ya ce" Idan kina da wanda kuke tare, ki turo min shi, saboda mu zauna da shi, kuma in yi bincike kansa, ke ma zan mika ki dakin ki ne ba da jimawa ba"

Daga haka ya juya ya fice a dakin, ya bar su tsaye su duka biyun

JAUHARA ta silale tana sauke boyayiyar ajiyar zuciya ta ce" inama mijinki mutun ne da za'a hau da wasa da dariya ko bai so ba? Da cikin wasa nace masa cikin samarin nan uku ya bani daya, Ni dama Allah ya min son fararan maza, kin ga du wanda ya nuna yana so na kuma baki ne........., dan Allah kwatanta masa mana "

MAZNA ta Dube ta kafin ta girgiza kai ta nufi sama saboda ta je ta ɗan huta , zuwa an jima sai ta sauko........ Ta bar Jauhara nan zaune tana tunane tunanen mafita, dan ita idan har zata damu daya cikinsu lafiya lau ne ta gama samun miji.

Bata jima da zama ba wannan saurayin nata dake daya daga cikin masu kula da shige da ficen wayoyin familly din ya ajiye mata message din da ya gigitata, wanda ya sa ta mike a tsorace jikinta na daukan rawa ta nufi sama da gudu ta nufi dakin IMAD dan ta san MAZNA ta fi son zama a dakinsa fiye da ko'ina a sauran dakunan gidan ta shiga bugawa ba kakautawa tana dake duban message din hankalinta na idasa tashi.

A bangaren su IMAD kuwa da ya fito , sai da suka zagaya bangaren baki ya gaisa da uncle Muhammad ya masa ya hanya, ya sake duba masu kula da shi sosai sannan suka fice da nufin zuwa bangaren Anna suka barshi dan ya huta sodai

A lokacin da suka karaso bangaren na Anna haka kawai ya ringa wani tunani a cen kasan zuciyarsa............

A gaskiya da a da ne, bashi da wata damuwa da tunanin ta yiwu ya samu abinda ba haka ba, saboda ya san du rashin jin FARHANA bata zama a falon kasa da shigar da hankali ba zai dauka ba, Ama a yau sai ya samu kansa da duban zaratan samarin dake tare da shi su uku, garza garza da su da hutu ya sa suke nishi su kadai na jin dadi, ga Mutalab sai mita yake cewar a kan me zasu kore shi daga dakin IMAD su su zauna, me suka tattauna wanda ya fi karfinsa shi?, Abdul bassit sai sake hasala shi yake yi yana masa dariyar shakiyanci yana faman fadin yaro ne kai, AKOY firarakin da baka riga ka ajiye budurcinka ba, ba zaka ji ba, shi kuwa takaici na rike masa wuya yana duban IMAD ya ce" Yanzu broth baki zaka bari su hada ni da kai ? Yaushe ma suka zo?"

Abdul bassit ya yi murmushi yana juyi ya dan daki gefen kafadarsa ya ce" ka dan fa yanzu wannan sirikinka ne, so kake a maka zancen lamarin da ya shafi nan na sirikinka?"

Ya fada yana rike arzuzumin wandon Mutalab, domin shi kaya ne irin namu na Hausa ya saka, wa'inda tunda ya fara sakawa FARHANA ta yi murmushi ta boye fuskarta da yace yayi kyau? shiKenan ya mayar da su tufafinsa, in dai zai fito to fa wahala ya saka jalabiya, sai dai ya saka su ya fito hankali kwonce

Ido Abdul Fatah ya zarro, haka ma IMAD

IMAD ya doke hannun na Abdul bassit kasa kasa sosai ya ce" Kai, ka ga ciki zamu shiga, ka kama kanka, saura idan mun shiga ka mana wani abin da yara zasu iya raina mu!"

Abdul bassit ya kalli Abdul Fatah, shi ma ya kalle shi

Abdul bassit ya gyara tsayuwa yana sarawa ya ce" Sorry Sir, ba zan yi abinda yara zasu raina mu ba gaskiya!"

Ido ya zuba masa kafin ya dauke kai yana girgizawa ya fara dana sonore, har sau biyu sannan ya dan dakata yana dubansu

Da mamaki Abdul Fatah ya ce" Yaushe ka fara neman dogon izini haka kafin ka shiga falon Anna?"

Idannuwansa ya saka a cikin na Abdul Fatah ba tare da niyar bashi amsa ba, haka kuma yana niyar juyawa ya bude din FARHANA ta bude , domin sun zata bako ne ko bakuwa aka yi ya sa ake neman izinin shigar

Baya ta ja da sauri tana fadin" Barka da safiya yaya, Barka da safiya yaya, Barka da safiya yaya, Barka da safiya yaya"

Wato su duka hudun sai da ta marabace su yadda ta saba jera musu sannan ta koma gefe tana sada kanta dan girmamawa da kuma basu hanya su shige

Gira daya Abdul bassit ya dagewa Mutalab da ya zama na karshe wajen shiga, kasa kasa yace" Sai ka min wata rashin kunyar wallahi in saka ka a damuwa , dan rainin wayo mai son sanin abinda ke damun sirikinsa "
Chapter 109 · 0% Book details