Sashe 54
Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Filin gidan ANNA ya dauki ma'aikatan gidan bisa umarnin da uban gidansu ya basu a jiya cewar yau karfe goma kowa ya halarta a filin gidan, du wani ma'aikaci ya tabbatar da ya halarta a filin gidan a lokacin nan, sai ya zamo tun karfe tara kowa ya zo din, ciki kuwa harda ALIYU HAIDAR dake dauke da shiga irin sojan Nijar, wato kaki na sojan Nijar, shiga irin ta sosai din nan domin a kugunsa harda karamar bindiga a daure , haka kuma idannuwansa dauke da bakin gilassss, sannan motar da yake tsaye a jikinta sabuwar mota ce, ba a cikin jerin motocin gidan take ba dan basu santa ba, haka kuma tunda ya yi tsaye a wajen bai zauna ba, kuma bai nuna alamun zai ɗan zagaya wani wajen Bama, hakan ya sa du Wanda ya zo wajen sai ya samu nutsuwa ta shige shi kai tsaye, sannan tsarguwa da gudun ya zauna su darsu a zuciyarsa.....hakan ya zama kowa a tsaye yake, kuma ba mai surutu, sai yaya Anas dake yawan kallonsa sai ya ji dari dari na kama zuciyarsa da tsoron kar dai aje korarshi za'a yi????.........
Da wannan tsoron ya zagaya baya yayi kiran mahaifiyarsa, wace ita din ma a dari dari take da shi tana gudun ya ji abinda ya faru jiya, wato abinda ta aikata ita da aminiyarta, dan sai yanzu take ta tsoron kar aje ya ji din, bale a jiya da dare da ya dawo sun sha tsaraba da kudi na kyautatawa kawai..........., hatta Fa'iza bata san abinda ta aikata ba, haka kuma cikin son bugun zuciyarsa sai da ta tambaye shi labarin IMTEE?, sai kawai ta ga yayi murmushi yace yau kuma da ta fito sam basu yi fada ba, .....ita har ga Allah ta fara tsoron yarinyar, take taken yarinyar na firgita ta, yaya za'a yi su je gidansu su musu tijarar nan Ama ta kula shi? Kwarai tunanin ta ya sake tabbatar mata yarinyar nan ta shirya tsaf dan ta kwace mata danta ne...., ita kuwa itama a shirye take tsaf dan ta kwatowa kanta yanci da d'anta!...........
Bayan wayar ta yi ringin ta daga, muryarsa a dan birkice ya ce" Mama, kin san abinda yake faruwa a nan kuwa?, wannan mutumen da nace maki na dauko daga aéroport kin san da na bincika dama yana daya daga cikin manyan masu kaki dake bada tsaro a Babar famillyn SAWIRIS, kuma a cen shine ke kula da oga, mama abinda ke bani mamaki kin ganshi nan da kakin soja na kasar nan, kin san ba zai yiwu a nan yayi amfani da kakinsa na cen ba, haka kuma idan ba kakin bashi da damar amfani da wasu abubuwan masu girma dan bada tsaro....., Mama Gayanan dai harda su bindiga a jikinsa, Ni yanzu tsoron da nake kar aje korata za'a yi, saboda an hada baban taro na ma'aikatan gidan nan yau, kuma maganar da nake maki ba wanda baya nan, kar aje a dakatar da Ni, ko kuma a sakani cikin kananun ma'aikatan gidan nan, bayan saboda Ni ne na hannun daman oga har kirana suke karamin oga....., shin yaya zan yi????"
Mamansa kanta hankalinta sai yayi mugun tashi, ta rasa mema zata ce masa......., yannayinta da tarin tashin hankali ta ce" Subahanalah, wai yanzu haka abinda ke faruwa kenan?"
Anas ya tabbatar mata
Mamansa ta ce" Kana ji, ka kwantar da hankalinka in sha Allah ba zai kore ka ba, a shekarun da ka dauka karkashin sa Ni da kaina na san uban gida ne mai mutunta na kasa da shi, na yarda cewar ba zai taba wulakanta ba ko ya kore ka, ba ruwanka da bakon nan, in me aka bashi ba ruwanka, kawai kai dai kar su kore ka ka fahimta? Ko me aka baka ka amsa ka yi godiya kar ka yarda ka kawo musu rashin kunya ko ka nuna ba'a kyauta maka ba ka gane?, ina sauraron ka, abinda ya faru ka fada min, in sha Allah a hankali ma damu Anna ta mana maganin bakon nan!"
Ajiyar zuciya ya sauke ya juyo da dan sauri sakamakon hango kamar du sun sake NUTSUWA
Kashe kiran yayi yana fadin" Sun fito, ina zuwa mama"
Daga haka ya barta cikin zulumi da tunanin idan aikinsa ya tabu ai sun shiga uku.
Fitowarsa da ta su Anna a kusan tare ne, domin dama Anna tunda safe ta shirya, ta zata tun da safen zasu wuce, sai kawai yace da ita sai karfe goma, yanzu haka yana gamawa ne ya sanar mata su fito, hakama ya ajiye wa Mutalab msg cewar ya fito su wuce ...........
A nutse ya karaso kusan shukoki inda du suke tare, wajen dauke yake da gazon , a share tas tas ga sanyi, .........wajen dai yana da dadin zama sosai da sosai
Shigar dake jikinsa a yau shiga ce ta yadi, wace ya jima rabonsa da irinta
Lalausan yadi ne baki sidik mai dauke da sasaukan dinki wai hannu daidai dantsan hannayensa ya zamo rigar ta sauda daga gwuiwarsa kadan ........ɗinkin dai daidai da jikinsa ne ya hau yanayin kirar jikinsa, ya fito da murdadun damatsunansa da hasken fatarsa sosai da sosai......., sai dan hiramin da ya mugun zame masa jiki ya yafa a saman lalausan gashin kansa mai yawa da santsi.................
Ƙafarsa sanye da takalmi budade ne baki sidik wanda hasken kafaffuwansa suka mugun haska takalmin , sai agogon dake hannunsa na hagu ...... Daga haka baya rike da komai, domin jakar dake dauke da waya da du wani abin bukatarsa a hannun MAZNA ne, wace ke sanye da ƙatuwar abaya baka sidik budadiya sosai da sosai , haka kuma fuskarta dauke da nikaf, da Safar kafa......, hannayanta kawai ke bayane suma hannun abayar na rufe su, idan ba ciro su ta yi dan ta yi wani abun ba su din ma ba'a ganin su......., kuma shigar nan haka ya fi so ya ganta da ita ko a lokacin da bata da duwawu ma bale yanzu
Gaban Anas bai kara faduwa ba sai da ya ga sunna karasowa wannan sojan, wato ALIYU HAIDAR ya karasa dan nesa kadan da MAZNA ya mika hannayensa dake dauke da wata Safar hannu wace wajen yatsotsin ke bayyane ya amshi wannan jaka ta computer mai dauke da komai na SIR ya nufi wannan motar ya bude gidan gaba ya ajiye ya rufe sannan ya ja ya tsaya idannuwansa a kan su, sai ya ji kamar ya zube ya tafka burgima da ihu a wajen, bale da du jama'ar wajen ma'aikatan ke yin ido ido da shi alamun yana gani kuwa? Ya shiga uku kam shi.
Hannayen Anna ya rike a hankali ya sumbaci bayan hannayen bayan ya yi mata runguma irin ta larabawa a tausashe ya furta" Barka da safiya UMMI"
Anna ta yi murmushi itama ta furta" Barka da safiya ukty"
Sannan ya dubi FARHANA dake kara dukawa tana ta karra miko tata gaisuwar hadi da kara dukar da kai alamun girmamawa
Murmushi yayi kawai bai ce da ita komai ba, ya maido dubansa kan Murtalab da yake masa murmushin shima
Alamu ya masa na dagawar hannun kafin ya mayar da dubansa kansu gaba daya
Da kula sosai, sannan a tausashe sosai ya ce" Barkar ku da warhaka "
Gaba daya wajen ya dauki amshi cikin girmamawa
Murmushi yayi a tausashe ya ce" Alhamdulilah, na damu sakon ku daga wajen Abah....."
Ya nuna Malan dake tsaye, ya dora da fadin" In sha Allah za'a daidaita....., a cikin ku akoy masu korafin albashi a banki na wahalar da su, wasu kuwa sun nuna su gaskiya ya fi gyara su ko?......, mun yi magana da comptable , na fada masa ya zauna da kowa, ina da damar da zan yiwa masu bukatar albashi a nan gida a musu, masu so a zuba musu a banki a zuba musu......, ina fatan hakan yayi, sannan idan da wata maganar da ake so a yi da ji kai tsaye Bismillah, "
Gaba daya wajen godiya suka ringa yi da fatan alkhairi, Aba a tausashe ya ce" Masha Allah, alhamdulilah, Allah ya kara lafiya da girma da nisan kwana......, Ubangiji ya kara budi......, ai idan ma akoy wata maganar in sha Allah zasu bi ta hanyar da ya dace, bale a yanzu sai da na jinjini kowa ya zamo ba mai wani korafi sai san Barka"
IMAD ya yi murmushi ya sake riƙe hannun Anna ya furta" Masha Allah, kowa ya koma bakin aikinsa "
Daga nan du kowa ya wuce ya zamo an bar ANAS kadai, da su Anna
Sai yanzu yayi hannu da su Anas din, su Murtalab
Da kula ya dubi ANAS ya ce" Anas, daga yanzu kula da mahaifiyata da Farhana ya dawo hannunka....., kwarai na yarda da kai ya sa na dauki aiki mai mahimmanci irin kula da kai kawon mahaifiyata na saka a hannun ka, sannan albashin ka na kara maka shi da kuma kyauta da aka ware ta ma'aikatan gidan nan da suka jima ta gida da mota wace kai ma ka samu, .......ina fatan zaka jajirce ka kiyaye, kar na same ka da laifin komai a lamarin da ya shafi Anna"
Innalilahi, sai kawai Anas yake neman zubewa kasa , domin nan da nan hawaye ya kece nasa ya ringa hade hannaye yana ta godiya da alkawarin in sha Allah ba za'a same shi da wani laifi a lamarin kula da Anna da FARHANA ba.
Nan take ya karbi jakar Farhana da ta Anna ya nufi tasu motar shima ya bude gaba ya ajiye ya juyo zai budewa FARHANA motar domin yana bada baya ta bi bayansa saboda ai an gama sai tafiya ko????
Harara ta sakar masa ta ce" Dila Ni matsa, kai kam ba Ni ba kai, kuka ne kake yi? Wallahi Anas ka bani kunya, maimakun kace baka son wata mota daya jal da kudi a kan aikin nan mai girma sai ka fara kuka? Ni kam ina sanin ciwon kanka ya tafi ne? Kai ka san sai na mayar maka da rayuwa kaka naka yi, domin du inda zan je kai zaka kai Ni fa, ama sai ka wani bige da murna a kan motar daya da gidan daya jal???? Mtsssss Ni matsa min, Allah wadaran naka ya lalace"