Sashe 67
Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A yadda ya rayu da abin nan a zuciyarsa ta tabbata a yanzu idan zai samu gaba daya ahalin matar nan rufe su zai yi ta yadda za'a batar da irin su a doron kasa......, kuma ba wai rasawar zai yi ba, dan ko yanzu da take zaune ita ce tace ya zauna ya saurari mijinta, kuka ita ce ta ce a je a dauko sauran a ji ta bakin kowa...., sannan ita ce ta sa ya taushi zuciyarsa ya fara yin hakuri ya sako ilimin sa saman fushin sa............
Kai ta gyada ta karasa kadan kusa da kujerar da yake zaune a tausashe ta ce" Andadinine"
Idannuwansa dake kallon su Aban yara da duban da ya sa a yanzu shima Aban yaran tsarguwa ya dauko ya sauke a kan fuskar mahaifiyarsa
Ido ta fara tsurawa nasa idannuwan....., a hankali ta dauke dubanta ta ɗan yi yannayin dake nuna masa hankalinta na iya tashi da yannayinsa kafin ta safe sunansa a tausashe sosai ta ce" Ka sa a shigo da su........., ba kowa ne mai laifi ba"
Fuskarta yake kallo, kafin ya kai dunansa kan yarinyar nan dake tsaye, duba daga kafarta har zuwa kanta da katon hijabin nan da ya yi mata yawa sosai ........
Idannuwansa ya lumshe saboda kwarai ya san Anna na tausayin yarinyar nan......... Anna nada shakuwa da yarinyar nan......, itace zata ce Anna ta sa a sanyo iyayenta......, dama ace zasu bashi waje yayi abinda yake ganin ta fi dacewa, dama ace Anna zata gane ba zai iya daga kafa a lamarin nan ba...., dama kar Anna ta yi anfani da damar da Allah ya bata a kansa ta saka shi yin abinda zai yi mata kuka yau da idannuwansa????, dama Anna ta gane girman abin nan a zuciyarsa ta bashi dama yayi yadda ya ga dama????.....dama ta gane shi babu wanda zai bashi tausayi a nan saboda a irgensa an dauki sama da shekara ashirin da daya yana kallon mahaifiyar yarinyar nan cikin halin da take ciki..........
Yar karamar wayar sa kawai ya dauka ya yiwa Aliyu msg kamar haka" Su shigo"
Kafin ya sake duban Anna da ta koma ta zauna abinta haka kuma ta zaunar da NUR Daf da kafaffuwanta , domin da so ta yi ma yarinyar ta zauna saman kujerar kusa da ita, ita ce ta nuna mata inda zata zauna harda dora kanta a kafar mahaifiyarsa............
Sanyin zuciyar mahaifiyarsa na iya cutar da shi a yau!
Ba'a dauki lokaci ba aka bude kofar polise biyu suka fara shigowa sannan su Auntyn yara suka shigo, da maman yara sai baban sojan da abin ke hannunsa, da kuma Aliyu , sauran an dakatar da su a waje, bisa umarnin babansu.........
Wajen da Aliyu ya nunawa kowa suka zauna, harda A'isha dake jikin auntynsu ta dora kanta ta boye a hijabin auntynsu, ya zamo auntynsu na fito da ita tana komawa tana boyewa, IMTEE ce da ta ji haushin lokacin da suka so zuwa daf da ita ama wannan sojan fari ya yi gaggawar nuna musu yin nesa da su kamar wa'inda zasu yiwa Anna wani abu ta dake duban A'isha da ta fi dan kusa da ita ta yi murmushi saboda yadda suka likewa juna ita da Auntynsu kamar za'a sace ta .....?.........
Tunda suka zauna din, shiru suka yi su dukansu babu wanda ya ce ufan, ya zamo falon ya dauki shiru sosai da sosai har sai da yayi niya ya gama hana kansa aikata duk wani abin da zai iya sumar da matar nan kafin ya dubi sojan nan a nutse ya furta" Sir, Bismillah ka gabatar da aikin ka"
Murmushi sojan yayi ya gyada kansa ya kai dubansa kan maman yara da a duniya idan akoy abinda ke firgitata to fa tsoron yan sanda ne ya ce" Ke matso nan ki mana bayanin yadda aka yi kika sace yar mutane da dalilin da ya da kika sace ta, da kuma wa'inda suka taya ki sace y'ar mutane.....matso nan ki mana bayani!"
Hankalin maman yara ya kara tashi, ga yinwar dake ciciyar hanjinta, ga ƙishirwa, ga gajiya, ga bugawar zuciya uwa uba tsoron ikon nan da suka dafe ta
Tsayuwar da Aliyu yayi a gabanta ya mata nunin inda zata matso din ya sa Nur rintse idannuwanta ta jimke hijabin Anna, zuciyarta na neman karyewa....................
Tashi mama ta yi da sauri ta zo nan din ta tsaya tana kallon Malan da kuma Nur zuciyarta na sake daukan zafi da radadin dake huruwa a cikinta......, kai tun da aka fara abin nan fa kallon kirki bata yiwa A'isha ba kamar wanda take yiwa Nur da Malan......
Haka kawai take ji a zuciyarta cen cen karkashin zuciyarta me zai faru da ita yanzu idan aka raba ta da Malan da kuma Nur???
Wannan sensation din da take ji ta fi komai firgitata da hargitse mata lisafi......
A kan me zuciyarta zata ringa hasko mata Nur a cikin wace zata fi shiga kaka naka yi idan aka raba ta da ita ba ma A'isha ba? A kan me zuciya zata yi mata haka bayan ita ta san baban burinta a duniyar nan ta ga Nur a cikin halin kaka naka yi na rayuwa?, to wai a kan me zata yarda zuciya ta saka mata samuwar halin da Nur zata shiga idan bata kusa da ita bayan ga ubanta ga uwarta a raye? A kan me take ji a zuciyarta kamar numfashi zai katse mata idan ta tuna malam na iya tsanarta tsana ta har abada har ma ya raba ta da NUR???????????
Tsawar da sojan nan ya mata a lokacin da ya ga ta tsaya din Ama ta kasa yin magana ya sa ta zabura har sai da ankwa din hananyenta suka dauki wata kara, lokaci daya su auntyn yara ma suka zabura , uwa uba Nur da zaburar da ta yi ta hade da kankame kaffafuwan Anna cen cikin wuyanta ta furta" Mama...., wayo mama kin kashe Ni, mama me yasa........"
Anna dake dubanta tana shafa kanta a hankali ta saka hannayanta ta dagata ta zaunar da ita saman kujerar da take kafin ta kwontar da ita a saman cinyarta ta ci gaba da shafa bayanta a hankali wanda ke alamun rarashi da métrise dan ma kar ta shiga maganar da za'a yi
Maman yara jiki na bari ta dubi sojan nan kafin ta sada kai ta ce" Eh, Ni ce na dauke ta, a wata ranar Laraba a asibitin dabe, a lokacin da likita ta leko tace ina wanda ya rako juwaira , ta kara maimaitawa ta ce a biyo ta da zani ta koma da sauri......a lokacin muna ringa kallon mutanen da dama du mun san wa'inda suka rako, muka ga ba wace ta tashi sai kawai mu muka tashin muka shige da zanin muka tsaya ana miko jaririyar aka bani aka ce maza in mika ta dakin da za'a goge ta a aunata, Ni kuma a lokacin ne na ba aminiyata ita ta yi waje da ita a cikin hijabinta sannan na cenza hijab na yar da wancen a nan na ringa fakar ido har ni ma na fice da gagawa kafin a ankara a fara nema tuni mun bar anguwar, kuma bamu dauki adaidaita sahun kofar asibiti ba, bamu dauki abin hawan kofar asibiti ba, sai da muka je inda zamu a kafafuwanmu sannan muka je gidan aminiyar tawa muka sake kimtsa wa muka nado ta a cikin hijabina muka yaryara jinin kaza a jikin hijabin muka fito muka dauki adaidaita sahun ya kai mu gidan malan, muka shigar masa da baby, aminiyata tana ta rungumo ni da yi min sannu , a ranar ne muka sanar masa a hanya na haihu!"
Anna ta lumshe idannuwanta tana ta kallon inda A'isha ke boye, sam ta ki ta fito ma, haka kuma kuka take yi daga ita har auntyn nasu da ta rungumeta, Sulaimana kuwa wani kallo ne kawai yake yiwa maman nasu kamar zai iya shake ta ya kashe ta a tsayen nan, domin bayan ta ajiye maganar ta sai yanzu IMAD ya dago ya dubeta ya datse lebensa na kasa .......
Malan mijin mama zuwai ne ya dube ta da mamaki yana sake duban fuskar ta ya ce" Ke ce na bige a lokacin da na shigo da robar haihuwa? Har kika yi wata irin tsorata na so in bi ki in baki hakuri kika ce ba komai kika yi waje da sauri?"
Maman yara ta zuba masa ido, duda abin tsufa da kuma rawanin dake fuskarsa kwarai tana tune da wannan abin, domin a lokacin da take sanda sanda zata fita wani mutun ya bige ta da kaya a hannunsa har kayan suka bare, yana gagawa yace da ita yi hakuri dan Allah Malama, sauri nake yi na amso kayan nan a shagunan waje matata ke kan gwuiwa, sam ban ganki ba, dan Allah ki yi hakuri....., ita kuma ta yi gaggawar ce masa ba komai sannan ta fita da sauri ta fice.....
Kai ta sada bata bada amsa ba
Sojan nan ya girgiza kai ya dubi Malan ya ce" Wato ma har ta hadu da kai, Ama tsabar ba imani ta yi tafiyarta da babynka......., zaki yabawa aya zakinta ne yau, ke su waye abokanan muguntar taki? Ke da wa kuka hada baki kuka yi wannan aikin? !"
Maman yara ta zuba wa su Malan ido, Bama kamar Malan na Magarya wanda hakan ya sa yayi tsuru tsuru yana ta kama sunnayen Allah, saboda shi zuwa yanzu kam kuma ta fara bashi tsoro....dama har haka ta kai da rashin jin tsoron Allah da mugunta? Dama matar nan har haka ta yi nisa? To shi yanzu ai ba zai so wani abin da zai sa su yi doguwar magana shi da ita Bama gaskiya, kuma kallon nan da take masa Allah ubangiji ya rufa masa asiri kar tace shi ne abokin shawarar nata ta ja masa jaraba, domin kuwa ya san kafin a gane gaskiyar magana ai an halaka shi a gidan maza.......................