Sashe 82
Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
A lokacin da ya karasa ya samu yan makarantar na cikin aji, sai malaman dake sanarwar cewar karfe goma kowa ya je gida ya sanar da iyayensa nan da sati za'a fara tankade da rauraya dan a ware wa'inda zasu ci gaba da zuwa makarantar da wa'inda za'a salama saboda shiririta da rashin bada hankali a karatun......wanda a zuwansa bai fi saura minti goma a fido sun ba, dan haka ya karasa ofice din Anna ya gaisheta ya same ta kwonce saman doguwar kujerar ta, sai da Farhana suka gaisa sannan ya fita ya samu irin dogon bencin nan dake nesa kadan da office din ya zauna yana tunanin irin firar da suka yi shi da mahaifiyarsa hankalinsa na kara tashi , nutsuwarsa na son barin gangar jikinsa.......
Bai jima sosai da zaman ba, aka fito da yan aji, ya kasance wajen ya dauki surutu kafin su fara watsewa suna daukan hanyar tafiya daga makarantar a hankali a hankali har wajen ya dan rage sosai
Hango su ya yi sun nufi bangaren da yake, wato wajen office din Anna, harda kanwarsa Fa'iza, suna fira cikin shigar abayoyin da ya siyawa Nur, wanda suka dauki jikin su Masha Allah, Bama kamar NUR sun matukar amshi jikinta sun haskata sosai sun ci kuɗinsu a jikin nata..............
Murmushi ya fara yi kafin ya mike tsaye ta yadda suka ganshi
Fa'iza ce ta fara yin murmushi ta ce" Lah, yaya, ku zo mu gaishe shi"
A'isha ta fara bin bayanta kafin NUR ta raka musu baya tana jin a ranta eh bari ta je dan ta gwada masa kayan nan ma ta masa godiya, duda yanzu kanwarsa ta gama cewa wai a ina suka samu kayan nan masu masifar kyau, suka ce da ita a gida abansu ya basu, haka kawai suka ki sanar mata daga ƴaƴanta ne, kuma ba wani hada baki suka yi, ko daya kawai haka amsar ta zo musu ba tare da wani ya koya musu ba
Gaisuwarsu yake amsawa yana murmushi, suna gama gaishe shi Fa'iza ta ce" Kun ga, Ni fa tafiya zan yi, yaya dan bani na alewa mana"
Harararta yayi yana laluba aljihunsa ya ce" Zaki yi bayani ne, amshi ki sayi mai kanti ma, je ki bamu waje in gaisa da kyau da matata mana"
Dariya ta yi ta cafke dubu biyunta ta yi gaba da gudu tana cewa" Allah ya da a jera wata kana bani na alewar nan, ai da sai kasuwanci yaya"
Nur na yi mata yar siririyar dariya, A'isha ma ta yi dariya ta nufi cen gefe tana fadin" bari in baku waje ku gaisa sai mu tafi, yan soyayya"
Jinjina mata Anas yayi yana yar dariya, NUR kuwa ta sune kai kawai tana murmushi
Zaunawa yayi yana nuna mata saman bencin ya ce" Zauna mana amaryata?"
Nur ta noke kafada tana dubansa ta ce" ka gani ko yaya idan kana saka Ni jin kunya guduwa zan yi"
Dariya yayi yana tafa hannu kadan ya ce" shiKenan kanwata zauna magana nake so mu yi da ke mai mahimmanci, Nur ina cikin damuwa, mai girman gaske, dan Allah ki zauna mu yi shawara in fada maki halin da nake ciki dan mu samu mafita tare, domin na san kina so na, kuma zaki iya dubana ki yarda da abinda zan fada maki, zauna plz"
Wajen ta duba, kafin ta yi murmushi tana noke kafada a hankali ta ce" Ka ga fa cikin makaranta ne nan, Malaman mu sun hana irin haka ko da dalibai bale da manya, idan har maganar ba zata jira ba har ka zo gida ka fada min a nan , Ama idan na zauna komai na iya faruwa a cikin makaranta yaya Anas"
Ajiyar zuciya ya sauke yana dubanta ya ce" Haka ne, Nur ina cikin damuwa mai girman gaske......., wai Mamana ke maganar aurena da ke....cewar...cewar..........., Nur ban san ta inda zan fara ba , gaba daya abin wani iri nake kallonsa, abin ne kamar wata almara "
Nur ta sake zuba masa ido, yannayinsa na iya son sakata a wani tunani daban, to ko dai ce masa aka yi maza maza su yi aure yanzu ne ko me? Tabdijan to ita anya zata iya yin aure yanzu yanzu kuwa.?????????
Isowar motar da ko kuka bata yi sai wani silent kuka tamkar tana ajiye numfashi , fara kal kal kal ya sa A'isha dake kallon wajen zubawa motar ido dan tana gani ta san baban yaya ne ke cikin motar nan, sai Anas da ya waiga saboda irin tsayuwar motar ko ba'a fada masa ba ya san ta ogansa ce
Ganin motar ya saka shi sakar mata murmushi yana duban ta ya ce" Ina ga OGA ne ya iso, karfe goma ta gota kenan, bari ya fito in gaishe shi, idan ya shige sai mu idasa maganar"
Murmushi ta yi tana dan waigowa ta dubi motar sau daya kafin ta dubi ANAS a tausashe ta ce" To ka zauna mana, wannan ai ko gwamna ne zai wuce ba zaka mike kikam haka ba ko"
Ido ya dan fitar yana duban ta kafin ya ce" wa Ni? In zauna? Haba dai, ke ma juyo ki sada kai alamun girmamawa a gaban ogan mijinki, OGA na ai ogan ki ne ko matata?"
Ido ta dan fitar ita din ma kafin ta girgiza kai tana murmushi ta shiga bashi amsa a lokacin da IMAD ya zuba musu ido har na sakwanin da suka wuce ka'idar kallon da yake iya yiwa mutun kafin ya juyo da dan sauri dan ya dubi fuskar Aliyu, ya zamo yana juyowa Aliyu ya shiga goge madubin motar daga gaba da hannunsa yana kara murzawa irin sam shi bai ma kalle shi ba
Hannunsa ya murza da dan karfi saboda jin da yayi kamar zai masa mijirya, sannan ya dubi gaban rigarsa saboda nan take yayi tunanin ko ya manta wayarsa a gida? Sai kuma ya kai dubansa kan agogon hannunsa ya duba ta da kyau kafin ya bude motar bai tsaya ya bi ta kan kowa ba ya haye matakalar nan ya shige office ɗin
Fitowa Aliyu yayi ya karasa inda Anas ke fadin" To, sir bai kula da mu ba, da ya tsaya mun gaisa, Nur ban taba ganin mutun mai adalcib ogana ba"
Baki ta tabe ta ce" Baka fada min damuwar da kace kana ciki ba, ko mama cewa ta yi a mana aure yanzu yanzu????"
Aliyu na isowa ya dubi Anas ya ce" me ya hana ka zuwa daukan su Anna a kan lokaci yau???"
Irin yadda Aliyun ya hade fuska yana wurgo masa tambaya sai da hankalinsa ya so tashi, saboda nan take ya shiga tunanin ko dai an yiwa Aliyu shugaban direbobin gidan Anna baki daya bai sani ba??
Da sauri ya dubi Nur ya ce" Je ina zuwa, zamu yi magana idan kika fito"
Nur ta tabe baki tana yiwa Aliyu kallon uku biyar saboda ta ji haushin ya zo waje ko Salama bai musu ba bale su gaisa ko kallonta bai yi ba ya shiga yiwa ɗan aikensu tuhumar raunin wayau.....hum shi yasa fa sam ita bata wani ra'ayin zama karkashin wani sama da mijin aure, shi yasa take hango kanta a matsayin mai siye da siyarwa nan da shekaru barkatai idan ta samu yan kudade
Da haushi ta zagaye shi ta haura matakalar ita ma ta karasa ta bude kofar bayan ta yi dan bugawa sau daya ta shiga da yar Salama a bakinta bata ko tsaya ta gane cewar A'isha na waje fa, A'isha fa bata shiga ba, A'isha fa ganin oga ya shiga ya sa ta kara tsayawa ma har sai ya fito su shiga din dan su ji shin zasu tafin ne tun warhaka ko kuwa su wuce gida kawai?????
Sai dai Nur na shiga ta samu IMAD zaune yana rike da gaban goshin Anna yana tofa mata addu'a, a hankali ya ce" Dama baki da lafiya kika zo makaranta, why ba'a yi kirana ba?....., ku tashi mu je asibiti ke Farhana dauko min Jakarta "
Da sauri NUR ta karasa tana dukawa gaban Anna ta saka hannunta wajen fuskar ta Anna tana tabawa a raunane ta ce" Anna, annata baki da lafiya? Menene, menene yake damun ki????"
Hannunsa ya janye da ta shafa yana sauke mata duba da kakausan idannuwansa ya ce" Ke tashi daga nan"
Da sauri ta Dube shi, haka ma FARHANA dake dauko jaka ta daka birki tana lekawa da kyau saboda yadda ya daka tsawar da irin kallon da ta masa sai ta ji ina ma tana da baiwar daukan hoto da ido? Yau da ta kashe kilisai masu karfin gaske
NUR dake kallon sa bayan ta ɗan nemi ja baya , Anna ta rike hannunta a hankali ta ce"
Barka da juma'a yan uwaKISAN MUMMUKE PAGE 52 and 53
Nur dake kallon sa, bayan ta ɗan ja baya, ANNA ta riko hannunta a hankali ya dube shi ta ce" Andadinine ka yi mata a hankali mana....."