Sashe 7
Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kasancewar idan suka fita daga girki tunda safe malan ke fita daga dakin wace ta yi girkin ya koma na yar uwarta ya sa ta sakawa zuciyarta cewar da wahala ta samu abin kari yau, sai ma kawai ta sakawa ranta dangana da tunanin ganin na rana zuwa karfe hudu zuwa biyar din yama, dan wani lokacin na ranar ma baya samuwa domin tsaf maman yara ke yin kwado dan kadan din da hatta malan ba zai samu ba, dan ce masa take yi ya'yansa sun cinye, dole kowa zai san na yi , shi yasa yawancin lokuta idan ta dau girki auntyn yara ke daukar azumi, ko ba komai ta san zata samu lada da nutsuwar zuciya domin ita kanta yinwar na yin tasiri ne idan ba azumi a baki, yau din ma ta tashi da fashin sallah ne kasancewar har yanzu bata shiga monopause ba.
Fitowar yan matan cikin shigar da ta nuna alamun zasu fita ne ya saka ta daga idannuwanta ta sauke a kan fuskar Imtee.......
Ya Allah, gaba daya yarinyar nan a kamanin mahaifiyarta, wato kakar imtee din babu abinda ta baro, hatta izar da kwarjinin ta kwaso wanda ke sakawa ta ji wani sanyi na ratsa zuciyarta idan ta kalleta..........
Masha Allah tamkar ba cikinta ne ya fito da yarinyar nan ba,
Gaba daya imtee ta tsatso kyau da fuzga ne ga idannuwan dake kalonta, tabas halitta ta Allah ce, Allah ya tsara halittar Nur gaba da baya sai fatan Allah ya basu miji na gari daga ita har yar uwarta.
Sau biyu sunna hada ido da auntyn yara da imtee , imtee din na gaggawar sada kanta , sai kuma ta ɗan juyar da dubanta tana murzar hancinta har babansu ya shigo kamar yadda maman yara tace su jira shi ya basu kudin taxi, kamar yadda ta tsara masa cewar ta aike su ne gidan bikin aminiyarta da ba zata samu zuwa ba saboda bata jin jiki, bayan tsari ne kawai, tunda yaran suka yi mata maganar sunna son zuwa gidan kawarsu dan su mata kitso da kunshi sai ta amince bayan ta san mahaifinsu ya hana haka din, yace ne shi ba zai hana su yiwa yan mata kitso ko kunshi ba, ama ya zamo an tardo su gida sun yi, ita kuma ta fada musu kar su yarda su yi kitson bati komai tsakaninsu da kawa idan suka anfaneta sai ta biya su, shi yasa yanzu ma da zasu fita ta sake jaddada musu kuma suka yi jiran mahaifinsu ya basu dari biyu kudin abin hawa dan ta sanar masa haka ne kudin motar.
Da murmushi ya dubi auntyn yara ya ce" To wai yau ban ga an karya tare irin yadda jiya aka ci abincin rana tare ba auntyn yara da yaranta"
Auntyn yara ta yi murmushi ta ce" Ai zamu ci idan suka dawo in sha Allah "
Du irin yadda ta so jin inda zasu je su yi din gagara ji ta yi, domin maman yara ta fito ta kasa ta tsare fuskarta daure tana ta tunanin maganar malan da son gane inda ya dosa, Ama ta kasa samun amsar tambayarta ɗan kuwa gaba daya ficewa suka yi, ta san kuwa irin yadda yarinyar nan ke yin ido yanzu da wahala ta wani bata gamsashiyar amsa..........Ama ba komai zata samo amsarta ne da kanta, idan har abinda take hasashe ne kuma wallahi ran kowa sai ya bace a gidan nan.
Tana ji tana gani suka yi tafiyarsu, haka ta koma dakin ta domin yau ba itace da girki ba cike da sake sake da addu'ar tsari a cikin zuciyarta.
Kasancewar gidan su Kawar tasu du cikin anguwar ne ya sa basu nemi abin hawa ba, duda da yar tafiya haka suka taka suna zantawa har suka karasa gidan nasu
A lokacin da suka zo shiga suka samu wata wuleliyar mota a kofar gidan a parke, suka zagayeta suka karasa cikin gidan bayan sun bude get din gidan suka shige, domin gidan su kawar tasu get din mota ne da su, kusan sunna cikin masu maiko maikon anguwar saboda yaronsu dake aiki a gidan da kowa ke son ganin cikinsa na anguwar, wato gidan da kowa ke son sanin me ya kunsa su waye a ciki Ama ba wanda yake da takamaiman amsar da ta dace.
A hankali Imtee ke takawa a bayan A'isha kadan, saboda aishan ta yi ta yi su jera ta kiya ta buya a bayanta tamkar wace take jin tsoron kar wani abu ya kamata har suka karasa kofar dakin imtee ta ja ta tsaya, A'isha ta karasa tana yin Salama hadi da dakatawa.
Da wani irin farin ciki Fa'iza ta fito tana ihun murna na ganinsu
Gaba daya ta rasa wane zata rike saboda har ga Allah bata yi tunanin A'isha zata iya ciyo karfin imtee su zo gidan nan yau ba, sai gashi sun zo din, kai ita ta san cewa an fa gama zata dau ado da wanka yadda ya dace
Jansu ta yi madaidaicin falonsu ta zaunar da su sannan ta yi ciki tana fadin tana zuwa
Imtee dake kallon kasa ce ta dago a hankali sakamakon mintsininta a karo na uku da A'isha ta yi, saboda tunda suka shigo suka zauna ta sada kai bata daga ba kamar ta zo gaban sirikinta gaisuwar farko din nan
A lokacin da ta dago lumsasun idannuwanta da nufin yiwa A'isha hararan da zai sa ta bata lafiya dan ita gaba daya a takure take tunda ta zo , shi yasa bata cika son shiga harkar masu hannu da shuni din nan ba, dan du sai ta ji ta takura idan ta kusanta kanta da daular su, ta fi gane gidansu na laka abinsu da pankar mafici fiye da wannan, a lokacin ne idannuwanta suka sauka a kan wanda ke tsaye yana kallonta
Ga dukkan alamu fitowarsa kenan daga dakin dake falon ya ja yake binta da kallon da ya sa gaba daya ta ji ta tsargu....
"Yauwa yaya, dama kai nake dakon jira, yaya kawo kudin mana dan Allah in aiki baratu ta siyo min kayan kunshin , wallahi idan Imtee ta gaji ba zata min kunshin nan ba, ka ga Allah ya taimakeni ta yarda ta zo, plz my yaya........." Fa'iza ta fada tana alamar zata yi shagwabar nan, domin alamu sun nuna kwarai tana yiwa ƴaƴanta shagwaba a cikin gidan su
Idannuwansa ya kifta yana sauke dubansa a fuskar fa'iza, lokaci daya kirjinsa na bugawa da wani irin shaukin da ya saka ya damki hannun fa'izar yayi dakinsa da ita yana rage murya sosai ya ce" Fa'iza, wacece wannan? A ina kika san wannan? Menene hadin ki da ita?"
Da mamaki kwarai take kallon yayan nata, Cabdijan, to ai dole zata yi mamakinsa saboda gaskiya ƴaƴanta baban yaro ne, tabas ya samu wajen aiki na gani na fada wanda basu rage masa komai na a zo a gani a rayuwa ba, yana murza manyan motocin su, yana murza manyan suturun dake kara janyo masa yan mata ta kowace kofa......, yayansu baban yaro ne da ba kasafai zaka ga ya dubi mace sau biyu ba, kai ko budurwarsa da aka sani a gidan su ita ke fama da ranta, saboda irin yadda yake wahalar da ita har tausayi take basu, gata kyakkyawa da ita mace har mace ama idan ya kiya har kuka yake sakata yayi tafiyarsa sai dai su su rarasheta......,maganar da ake yi ana shirye shiryen kai kudi gidansu ma fa
Murmushi fa'iza ta yi tana dubansa ta ce" Yaya kawata ce fa, kawayena ne , yan uwan junna ne, itace nace maka idan Allah ya taimakeni zata zo ta min kunshi na bikin nan"
Idannuwansa ya rintse yana budewa lokaci daya ya sake zuwa ya dan dage labulen nan ya leka su imtee dake zaune sannan ya dawo ya zauna daf da gadonsa yana shafa kansa a bayane ya furta" Calm dawn , calm dawn, babu Macen da ta isa ta dubeka ta kasa yabawa a duniya....babu ita"
Da mamaki fa'iza ta ce" Yaya, me kake nufi? Kai da kake da fiancé?"
Hannunta ya kamo yana dubanta ya ce" Ki rage murya, dan ba zan yarda ki min gangamin maganar da zata shiga tsakanina da yarinyar nan ba, ke Ni fa namiji ne, ina da damar kawo mace hudu a rana guda matsayin matana...., bale idan yarinyar nan ta budi baki tace bata so in kuma fada maki magana ko ke kanwata an gama bale wancen uwar nacin!"
Baki fa'iza ta saki tana dubansa
Yayi yar dariya ya mike ya bude walt dinsa ya ciro kudin da suka sa fa'iza zarro ido yana kalonta ya ce" A siyo mata duk wani abinda zai sa ta ji dadin zama a gidan nan na ci da sha, kar ki wahalar da ita plz, bari in je in dawo ki tabatar da kin rike min ita har in dawo Fa'iz....."
Fa'iza kam ta kudaden nan take, hannaye biyu ta sa ta karɓe tana gyada kai hadi da fadin" Kar ka wani damu big yaya , Allah dai ya dawo da kai lafiya kawai"
Murmushi yayi ya sakawa kansa nutsuwa sosai hadi da janyo duk wani ajinsa, saboda ya san cewa idan akoy abinda ke saka shi jan hankalin yan mata bayan wanka da kanshin turare da hawa Babar mota da latsa Babar waya to kuwa ajin da yake ja musu ne....., ya sani ne idan ya ja mata ajin itama tabas ya gama tafiya da ita, ta yiwu zuwa gaba itama sai tana nemansa yana wulakantata tana masa kuka.
Ga tarin mamakinsa du irin uban turaran da ya kara a jikinsa a lokacin da ya zo fita ko idannuwanta bata daga ba bale har ta nuna ta san da wanzuwar wani bawa mai rai a wajen...., hakan ya sake daure masa kai da tunanin du inda ta fito wata Y'ar masu kuɗin ce da har ya zamo shi bai isheta kallo ba.........
Tabas du irin yadda yake da garatee da yarda da kansa sai da ya ji tsoro tsoro na son kama shi.......
Da gaske abinda bai yi zaton haduwa da shi bane ya sarke shi da farar safiyar nan har yake kokarin yi masa kisan mummuken da zai hana shi sukuni.