Sashe 118
Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Anna ta sauke ajiyar zuciya ta dubi abincin da ta gyara ta nuna da hannunta ita ma da Yaren Larabci, sai dai nata ba irin mai nauyin nan sosai bane, domin nata ba zai gagari fahimtar su Aban yara ba ta ce" Shi ne na yiwa girkin nan, kuma ban kai din ba, dan na san halinsa, ina iya kai masan ya amsa ya ki ci, bai iya fushi ko bacin rai mai girma ba, ban san yaya zan masa ba................, ama zan je in turo muku shi da karfi idan ya zo sai ku masa fada, ai ba za'a yi rayuwa a haka ba ko?"
Uncle ya gyada kai ya ce" Eh, turo min shi, ya taho mu hada mu tafi ma, mu je ya huta a cen Saudiya, idan ya samu nutsuwa sai ya dawo kawai......"
Anna ta sauke ajiyar zuciya ta mike tana gyara ƙatuwar abayarta ne Abdul bassit dake ta tunani a tausashe ya ce" Anna"
Anna ta juyo tana dubansa hadi da amsawa
Abdul BASSIT ya mike yana dan shafa bayan keya a tausashe ya ce" Anna ina NUR?"
Anna ta yi dan tsai tana dubansa, cike da tunanin Nur kuma?
Abdul Fatah ya dube shi da kakausan kallon kai ba fa lokacin tsokana bane yanzu, domin kaf nan a cikin zulumi ake
Abdul Bassit ya tabe baki yana dauke dubansa daga kan ABDUL Fatah a tausashe ya ce" Eh Anna"
Anna ta dubi hanyar sama ta ce" HALLAH ai tana dakin Inna, saboda jiya da na je zan rage sanyin AC a cen tace zata kwana, Inna ma tace a bara mata jikarta "
Murmushi yayi ya dubi kayan abincin nan a tausashe ya ce" Anna, ki bata ta kai masa abincin ......kuma, kuma ki ce idan ta kai din ta tsaya har ya ci ya gama sannan ta maido maki kwanonin"
Mutalab da ya zarro ido yana duban Abdul bassit ne ya maido dubanda kan mutanen dake falon, kusan kowa su yake kallo, harta su AUNTYN yara da suka ji sunan HALLAH ƙarara ya fito a firar sai suka bada hankalinsu kansu, dama Malan tun jiya yake cigiyarta yana faman fadin bai ga auta ba
Malan ya dubi Malan baba da alamun son karin bayani, sai dai shi din ma su din yake kallo, haka ma Mama da tarin son karin bayani kan wannan HALLAH din take kallon su
Abdul Fatah a hankali ya ce" Kai me yasa kake da neman fitina ne?, yaya zaka ce a tura ta a yanzu da yake cikin halin bacin rai? Ko sai ka yi abinda zaka sa ita ma ya ji ya tsane ta? Ka san fa ransa a bace da matarsa ko?"
Abdul bassit ya girgiza kai ya ce" Tsana?, ya tsane tan mana in gani, lalle kai baka yarda da son da yake mata ba ko????"
Mutalab da sauri ya ce" Abdul, a wajen nan babu wanda baya jin yarenka, yaya zaka tona masa asirin abinda bai fada da bakinsa ba???"
Mama ido waje take dubansu, Anna kam sai kawai ta girgiza kai ta nufi elevator da dan sauri tana fadin" Ina zuwa"
Mama kuwa sai ta mike tana duban Mutalab ta ce" Mutalab, zo ka gani"
Daga haka ta nufi wajen kicin da dan sauri, shi kuwa ya rasa guduwa zai yi ko bin nata zai yi? Ya tabbata yadda Malam ke jin Larabci haka Mama ke ji, saboda sosai Mama ke fira da Larabci da su baki daya, .......ya san cewa idan ya bi Mama maganar da aka yi zata nemi karin bayani, shi kam a gaskiya Abdul bassit baya kyautawa sam, mutun sai neman fitina?
A dole ya nufi kicin din, yana zuwa ya ce" Mama kar ki sa in fada maki abinda in ya ji Ni na fada zai ga laifina "
Mama ta kama hannunsa ta nuna masa wajen zama ta ce" Fada min zaka ya, ba zan taba cewa kai ka fada ba,........fada min wace HALLAH?, kamar HALLAH daya na sani KANWAR A'isha?, me me yake faruwa tsakaninta da yarona da har za'a ce a irin halin da mu muke tsoron zuwa inda yake dan mun san zamu hadu da rikicewar zuciya ne ita a tura ta? Wani irin alaka ce tsakanin su?"
Ajiyar zuciya ya sauke a tausashe ya ce" Mama, kawai fa harda abin Abdul, abinda bai ma taba nuna mata yana son nata ba?, da bari yayi Anna din ta je, Ni bana so a tura ta ita ma ya ji haushinta kin san fa halinsa ko?"
Mama ta zarro ido ta ce" Wai so?, kana nufin son yarinyar yake yi har ya gaza fada mata?, ama yaya aka yi kuka sani ku?, yaya aka yi kuka sani?, ya aka yi kun sani din Ama kuka kyale min shi a halin da yake ciki har yarinyar nan ta iya wulakanta min zuciyarsa take bata masa rai tana wulakanta masa daraja?"
Mutalab ya sauke ajiyar zuciya a tausashe ya ce" Mama tsaya ki ji abinda yake faruwa fa.............." Nan ya shiga labarta mata dalilin da yasa har su din suka yanke hukuncin halin da yake ciki Kenan.......................
Yanzu kam mama da tarin mamaki ta yi waje ta karasa falo kusa da malam kasa kasa ta shiga yin magana.................., Mutalab na biyo bayanta ya samu Uncle din su ya saka su Abdul gabansa shi ma yana tambayar karin bayani fuska hade dan ma kar su masa zagaye zagaye, jiki ba karfi ya karasa kusan Aban yara ya zauna a takure cike da fargabar ai kamar shi ne ya fasa kwan nan ko? Idan Imad ya ƙaryata fa????? Innalilahi, sai dai bai san yayi gudun gara ya fada gidan zago bane, domin yana zaunawa Aban yara a hankali ya ce" d'ana......, wanene ke son Nur din?, me yake faruwa da Elhajin ne?"
A hankali ya dafe kirjinsa yana Ayana ' Na mutu na lalace.........' dan kuwa ya sani, Aban yara ma ba mutumen da zai ki fadawa abinda ya tambaye shi bane, ya Allah.
A lokacin da Anna ta haye sama kuwa, dakin Inna ta je a hankali ta bude ta shiga tana sauke dubanta kan Inna dake kwance tana barci, .....dama idan ta yi sallar asubahi ta hantse sosai ta sha madarar da take sha sai ta komawarta barcinta........., a hankali ta juya inda take kyautata zaton ganin nur zuciyarta cike da tunanin eh, kwarai ta gwada haka din a gani......
Samun Nur ta yi zaune saman gadon Inna ta bude litattafai tana dubawa, yadda ka san manyan yan karatun jami'ar nan, ta dage dubawa take yi kamar ba gobe
Murmushi ta yi a nutse ta karasa inda take , bayan Nur din ta rufe tana murmushi ta ce" Anna, Barka da safiya, so nake yi in gama in zo in gaishe ki sai in karanta maki ko kya ji dadi Anna"
Anna ta zauna gefen gadon tana duba bayan litafin a tausashe ta ce" Masha Allah, kwarai da na ji dadin kuwa yarinyata, ashe kin farka, kin karya ne?"
Nur ta ce" Na karya Anna, ai yau Inna tace madarar nan da take sha zan sha, cewa ta yi wai madarar nada anfani a jikin mace, ko wani anfani oho......., galan din cen ta sa na shanye , yanzu haka jina nake kamar in fashe dan koshi"
Anna ta yi dariya tana furta" alhamdulilah, "hadi da yin dan shiru dan tunanin inda zata fara
Nur ta rarafo tana duba kwandon da Anna ta shigo da shi ta ce" Anna wannan fa? Mu fa mun karya"
Anna ta yi murmushi a tausashe ta ce" Eh, wai da yayanku ne zan kai ma Wancen dakin, kuma sai hannuna ya gaji sosai........., ina ga nemowa zan yi a kama min dan ba zan iya ba"
Nur ta daga kwondon, dan ta ga ko zata iya..... tsakani da Allah ba wani nauyi fa, dan haka sai ta idasa saukowa ta ce" Anna bari in kama maki , mu je, wani daki yake ne?"
Anna ta mike tana fadin" Yauwa yar albarka zaki iya kuwa? Da nauyi fa, yana Wancen dakin a nan ya kwana, Ni bari in fitar da kayan datin Inna kafin ki kai ki dawo, Yauwa idan kin je ki tabatar da ya ci kafin ki dauko kwanonin kin ji yar albarka, ko yace baya ci ki matsa masa, "
Nur ta dakata ta juyo tana kallon Anna, ......ta ga Anna ta nufi wajen wardrob din Inna, ta kalli Inna, ta kuma kalli basket din dake hannunta
Kasa kasa ta ce" Anna, Hala yaji ya mata?"
Anna ta dube ta, tana dan zarro ido a hankali ta ce" Namiji na yaji dama?"
Nur ta ɗan watsa hananyenta a hankali ta ce" Anna kin ce a nan ya kwana, kuma kin ce a matsa masa ya ci abinci......, ko fushi yake yi ko?"
Anna ta yi murmushi ta nuna mata hanya ta ce" Oya go"
Juyawa Nur ta yi ba tare da ta kara wata tambayar ba a hankali ta fice
Ajiyar zuciya Anna ta sauke tana zaunawa hadi da duba time...........
Karfe takwas har ta gota,
A dole ta mike dan ta koma kasa, da tunanin da an dauki mintina goma zata dawo ne ta gani.................., zuciyarta cike da tunanin kar ya koro Nur.
A hankali Nur ke kara bugawa, ............sai dai kamar ba kowa, ba'a bata damar shiga ba
Kamawa ta yi ta murda a hankali ta tura kofar da ta ji ba dai nauyi ba, ta shiga sannan ta ja ta tsaya sakamakon ganin duhu ya mamaye dakin tamkar safiya bata yi ba
A hankali ta shiga lalubar wajen kuna fitilu tana anfani da irin yadda ta ga na dakin FARHANA da dakin Anna da dakin Inna suke, kusan du a bari daya suke cen wajen tsakiyar dakin.............jikin bango..........., har ta ji yatsarta ta taɓa wajen, hakan ya sa a hankali ta yi Bismillah ta kunna fitulun gaba dayansu hadi da sauke ajiyar zuciya ta juyo dakin kasa kasa tana furta" Ko ba kowa a dakin nan?"
Idannuwanta ne suka sauka a kansa........
A zaune yake tsakiyar gadon, da dogon wando jikinsa ama ba riga ko daya........
tunda aka fara bugawa ya zauna ba tare da ya amsa ba.........................