← Book details Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 141

Sashe 1

Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

💅💅💅💅💅💅💅💅💅💅
*KISAN MUMMUƘE*
💅💅💅💅💅💅💅💅💅💅

_PAID BOOK_

*BY*

_SAJIDA NIJAR_

*Yan Naija Mutanen mu 1k ne a kan wannan account number 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank* sai a bani shedar biya ta layi na kamar haka +22793811618

*Yan Nijar mutanen mu zaku turo da hoton kati ta airtel ta dala dari , wato 500francs cefa a kan Numbarna kamar haka +22793811618*

*Na gode, sai kun zo.....taku ce SAJIDA NIJAR*

Tallah, tallah tallah....rabi ka siyar mana

*JAMA'A NAZOMUKU DAWANI TSARI NASAMUN KUDI TA HANYAR AMFANI DA WAYAN HANNUNKU
WANNAN TSARIN SHINE METAFORCE

MENENE KASUWANCIN METAFORCE* ????

*Metaforce kasuwancine ingantacce halattacce Wanda yake biya 100 💯 Wanda ake Gudanar dashi da wayar hannu,METAFORCE is also a part of network marketing,is a 100 percent decentralized project da aka daurasa Akan Blockchain technology Wanda babu wani mahalukin daya Isa YAYI editing,hacking ko deleting wani abu acikin sa,Kuma yanada matakai yanada rassa Wanda kowane reshi ka rike a METAFORCE to ka samu GUDUMAR DUKAN TALAUCI*🌎

METAFORCE ANASAMUN KUDI ACIKINSHI SOSAI MATUKAR ZAKAYI ABUNDA AKEBUKATA

zaku iyahada miliyoyin kudi aranadaya acikin wannan kasuwanci me albarka in sha Allah

Duk wacce tashirya zata iya tuntubanmu akan wannan number
09136899615
Hajja Data

*1*

Kai kawo take ta yi a dakinta, idan ta yi tafiya ta kuma yi sai ta rike karfen gadonta irin gadon karfen nan ta yi shiru kanta a kasa, sai kuma ta sake daga kan nata, ta kuma bin bangon dakin da ido kamar wace ke son karantar wani abin a jikinsa......, sai ta sauke ajiyar zuciya, ta yi haka ya fi a irga.

Shigowarsa ya saka ta juyo da sauri ta sauke dubanta a kan fuskarsa kirjinta na dokawa

Yannayinsa a harzuke yake, fuskarsa ba fara'a ko kadan

Bai ce da ita ci kanki ba ya karasa ya dauki dardumarsa ya juya a fusace da nufin ficewa daga dakin nata.

Da sauri ta furta " Abansu"

Dakatawa yayi ya juyo a fusace ya ce " meye kuma?"

Kai ta fara sadawa kafin ta ce" Dan Allah ka zo mu yi magana"

Rai bace ya ce" Babu wata maganar da zan yi da ke, zan sake maimaita maki, ki daina takurawa y'ayana, ki basu lafiya su huta a gidan ubansu, na gaji da halinki, na gaji da halinki sosai, ki yarda ki kai ni bango, zan nuna maki babu wani abu da zai sa in yi shiru ina kallo ana cutawa yayana in ci gaba da zama da mutun ko waye shi, aikin banza aikin wofi!"

Daga nan ya wuce, kunnayenta na jiyo mata yadda ya ja kekensa ya fice a gidan, ga dukan alamu yau shi zai je kasuwa ba sulaimana ba

Zuciyarta ta gama cinkushewa
Gaba daya bata fahimtar komai a irin lokacin nan
Sai ma da Sulaiman ya shigo yana cika kirji ya bude wajen tufafin mahaifinsa ya dauki jalabiyar mahaifin nasa wace a kanta ne aka yi ba dadi yanzun ya fice yana fito ya zura tun a gabanta sai ta ji kirjinta yayi mata mugun nauyi......ya hayul kayum,

Silalewa ta yi kai a kasa ta saki kukan dake dane mata zuciya domin ji ta yi kamar kirjin nata zai fashe ne,

"Iya miko miko, samodara, iya kali idona....samodara...." Muryar wata matashiyar budurwa ta nufo dakin , lokaci daya wakar da take yi ta koma ihu a lokacin da ya saka hannu ya kwada mata mari da hargagi ya ce" Ke dan ubanki ina hijabinki?, fice a gabana yar kaniyar banza kina tafe kina wurga kafa kamar shanyayiya, ke kam kin ji kunya ƙatuwar banza ƙatuwar wofi......."

Ihu budurwar nan ta saka tana rike kunci, ta sake saka wani ihun tana neman zubewa, hakan ya sa mahaifiyarta mikewa da sauri ta dage labule zata yi magana, sai dai nan take ta ja bakinta ta yi shiru sakamakon abokiyar zamanta da ta fito daga nata dakin tana sakarwa Sulaiman harara ta kamo hannun budurwar nan ta ce" Ka ga sulaimana ka kiyayeni, babu abinda ta yi maka zaka ci zalinta? Ku Shikenan sai ku kawo karan tsana ku sakawa yarinya kamar wace ta muku mugun laifi? Idan ta shiga dakin mahaifiyarta kamar ba ita ta haifeta ba sai kyara sai hantara sai zagi, kai kuwa da ka ganta sai ka kama neman daga mata hankali da cin zali? Hijabin me Allah na tuba, ina y'ar yar nan ina a wani matsa mata da sai ta saka hijabi? Ta ki ta saka hijabin Ka barta abinta in ba haka ba wallahi in sasaba maka a gidan nan!"

Bai ce da ita komai ba ya kada ya fice domin alwala ya daura, hakan ya kular da ita, wato ya mayar da ita shashasha yau Bama zai kula ta din ba ko? sai ma da ta ga jalabiyar mahaifinsa ce a jikinsa sai ta ji ranta na kuna sosai, wato a gidan nan sulaimana ba zai daina saka jalabiyar Malan a gaban idannuwanta ba dan uwarsa ta daure masa ko?

Ta so ta yi fitina a kan hakan, Ama sai ta kade ta ture ta ja hannun yar budurwar nan suka nufi dakin ta tana fadin" Wuce mu je, ban san me zaki je ki yi a wajen makiyiyarki ba( wato mahaifiyarta), kulun fada maki nake yi matar nan da ba dan dole ba da ba zata kawo ki duniya bama, rabon ki rayu a duniya ne ya rantse ya sa kika zo ta tsatsonta, Ama ke sai ki sadadeni ki nufi dakin su dan su hadu su wulakanta ki? Je ki kwonta ki yi barci!"

Y'ar budurwar nan ta ringa sauke ajiyar zuciya na abin kukan da ta yi murya a raunane ta ce" To mama bari in yi sallah, jiya a islamiyya malan yace du Wanda baya sallah a kan lokaci sai ya hadu da azabar Allah bale idan ya balaga, an ce mace da ta fara haila wai ta girma, shine nace to ko dai na balagar nima? Tunda shekaruna sha tara yanzu ai ko?, yace kar mu yi tunanin sallar da muke yi Iyayenmu muke yiwa, alkawari ne da muka dauka wajen ubangijin mu, Allah ne muke bautawa, domin an halicce mu ne dama dan mu bauta masa, wai mutuwa bata kan yaro ko baba, ana yin bari ma wai, haka yace wai idan ka mutu bayan tambayar waye ubangijinka, menene adininka , sallar ka za'a fara dubawa cikin ayyukan ka, idan ta yi kyau to ana yi maka kyakkyawan zato wai, ni du ya dame ni"

Dagowa ta yi ta kalleta shekeke kafin ta dauke kai ta shiga kunna redio bayan ta tabe baki ta ce" ka ji wani sababi, bilahilazi tsaf nake iya cire ki a islamiyar in ga ta hanyar da uban wani zai maki fatan shiga wuta, kin ga malaman nan da neman fitina suke, ke wai dududu nawa kike ne? Shekara goma sha takwas a saka ki a gaba? Sha tarar ma baki cike ba fa, Aikin banza wuce ki kwonta nace ki huta kafin raina ya bace!"

Jiki ba karfi ta shige fale dayan dakinsu ta kwanta saman yar yololuwar katifar su sannan ta shiga neman barcin, duda ba wani jin barcin take yi ba, ama yin nasa ba zai bata wahala ba.....dan maman nasu ta saba sakata barci a ire Iren lokutan nan, takan ce ta kwanta ta huta dan itace yar autarta............. Ta fi riritata fiye da yada take ririta A'isha, dan kuwa A'isha tuni ta dau buta zata yi alwalarta abinta.

A bangaren mahaifiyar Sulaiman da wannan yar budurwa kuwa daki ta koma ta zauna ta sake yin shiru.....
A zuciyarta aiyanawa take yi maganganu kamar haka... ' Shin kowani namiji ne yake da wannan baudaden halin ko kuwa iya mijinta ne?, ......'
Sai kuma ta girgiza kai da sauri sakamakon tuna Marigayin mijinta da ta yi, wanda suka dauki shekara goma sha daya matsayin ma'aurata ba tare da wani abu na wulakanci da tauye haki ya taba shiga tsakaninsu ba.....
To a lokacin da take auren Muhammadu fa, idan ka ga hankalinsu ya tashi yan uwansa ne suka sake dauko maganar haihuwa, wace sam baya basu damar kaiwa ga daga mata hankali yake katse fitinar, duk wani abu idan ya shiga tsakaninsu na zamantakewar yau da gobe zama yake yi ya zaunar da ita su zanta har su samu matsaya guda......., rana tsaka mutuwa ta zo ta shiga tsakani ta yi mata yankar kauna, wanda hakan ya sa bayan shekaru biyu da rasuwarsa ta sake yin wani auren.

A gidan wannan miji nata, uban ƴaƴanta biyu da ta samu da shi, tana ganin rayuwar da take kyautata zaton idan aka ci gaba a haka ta shiga uku ta lalace, ko tace ta gama shiga ukun fa, sai dai gyaran Allah domin abinda take gani itace kadai ke gani, bayan ita babu wanda yake gani, ga shekaru sun riga sun tafi, a yanzu ko ta fita ina zata nufa? Da shekarun nan me zata iya yi????
Chapter 1 · 0% Book details