Sashe 115
Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Aban yara ya bashi hankalinsa gaba daya yana furta" To to to, ina sauraro Allah gafarta Malan "
Malan ya gyada kai, a tausashe ya gyara zamansa ya ce" Malan, da farko dai Elhaji yace a sake yi maka godiyar rikon kanwarsa da kayi, sannan a sake sanar maka yarinya taka ce, idan ma a yanzu ka ki zumuncinta da mu ba zai ja ba, za'a yi maka biyayya ne , har zuwa lokacin da ka ji zuciyarka ta aminta da haka, domin ya fada da kansa cewar kwarai ya jima bai ga mutun mai datako da halin girma irin naka ba, kuma yana kara baka hakurin irin hargitsin da ya kutso maka ya daga maka hankali a kan iyalinka....., yace kwarai yana baka hakurin shigar iko cikin gidan ka......yana mai kyautata maka zaton ka fahimci girman dalilin"
Aban yara cike da mamaki ya dubi AUNTYN yara dake murmushi kanta a ƙasa cike da ji a ranta kwarai alhamdulilah da Allah ya sa da kunnen Malan ya ji abinda take masa hasashe cewar bayin Allahn nan kwarai mutanen kirki ne, ba suna rabarsu dan su kwace masa A'isha ba, sun san mutuncin mutun ne kawai, in har kwace aishan suka so yi ai ba sai sun wani rabi jikinsu ba, ko basu hada da hukuma ba in suka kwace A'isha suna da tsayin hauro garun gidan nan dan karbar ta ne?, kwarai na kirkin ne kawai, jita jitan da ake yadawa a kansu, jita jitan ne .
A tausashe Aban yara ya ce" Malan, hakuri kuma?, ai ko laifi aka min Ni kam na yafe bale ba abinda aka min?, an saurare Ni, an min uzuri , ba'a wahalar da Ni da ahalina ba ta hanyar hadani da maman yara aka rufe har sai an gane gaskiya ta bincike mai zurfi ba, ai Malan a sanar da Elhajin cewar Ni Ahmadu kam ba komai a zuciyata sai godiya da addu'a "
Malan na gyada kai yana faman furta Alhamdulilah Masha Allah, sannan ya dora da fadin" Sai sakonsa na gaba, magana a kan gida"
Nan fa zuciyar Aba sai da ta buga, sai dai bai ce komai ba yana duban Malan cike da kula
Malan ya ce" Idan kana tune, kwanaki an yi ta kai kawo kan maganar don ka siyar da naka gidan kai ma, Ama ka bayar da uzurinka cewar gurbi ne na mahaifanka ba zaka so a tayar da kai ba sai idan kabari za'a kai ka daga nan ko?"
A tausashe Aban yara ya sake sada kai ya ce" kwarai an yi haka, kuma a yanzu ma ina kara bada hakuri dan Allah a Bara min gurbin nan, idan har ba lalle lalle ana son wajen bane? In har da hali a min hakuri a Bara min wajen nan dan Allah"
Malan na murmushi ya ce" Malan Ahmad, a zamanin nan mai daraja ai mutun nada yanci......, ai Elhaji da kansa da ya ji komawar masu siye da siyarwar dukiyarsa wajen ka har sau uku sai da yayi kira ya saba musu fiye da tunanin ka....., kwarai yayi fada kuma ya ce a tabbatar da an nemo du WA'INDA aka sayi gidajensu zai zauna da su, idan har ya gane cewar matsa musu aka yi dan a nuna musu iko da dukiya da fin karfi aka tashe su daga muhalansu sai an mayar wa kowa gidansa, kowa mai iko da dukiyarsa ne, idan mutun yace ba zai siyar ba babu mai takura masa kan sai ya siyar "
Aban yara ya dauke ajiyar zuciya yana jin kunya na son kama shi
Anna a tausashe ta ce" Ka yi hakuri Aban yara, ka fito daga asibiti an tare ka da maganganun nan, Malan ko zaka yi hakuri har ya huta ne?"
Aban yara da sauri ya ce" A'a Hajiya, ai kin ga rike nin nan da a'i ke yi, sai da nace mata ta fa bari, Ni wani karfi ma nake ji a jikin nawa, kiyawa ne ta yi, dama ita AKOY sarkafa, ita fa auta kadan jikina ya tabu suna like da inda nake ne"
Anna ta yi murmushi tana furta " Allah sarki"
Malan ma da mutuntawa ya ce" kwarai Ni ma na so bari sai ya huta, sai dai sanin Mutanen mu da irin karantar Malan Ahmad da na yi na gane cewar mutun ne mai matukar girmama kansa da kiyaye dukiyar wani komai kankantarta.....wato Malan Ahmad abinda Elhaji yace a tattauna da kai shi ne, yana so ka bada amanarka, a rushe ginin nan a sabunta maka shi, yace ace maka idan har ka ga ba takurawa, ba wata matsala ko wace iri ce da zata shafi zuciyarka ko nutsuwar ka, idan har ka yarda har zuciyarka kuma ka ga ba damuwa a taba, ka bada damar da ba zata gaza wata daya ba, a sabunta gidan idan ya so sai ka koma fa iyalinka ka yi zaman ka.............., yace ne idan ka kiya kar a takura maka saboda ba'a san dalilin da zai sa ka kiya din ba, Ama yace idan a cikin dalilan dake iya sakawa ka kiya AKOY gudun maganar mutane ka ajiye wannan a gefe, domin mutun na yau ko gawarka yana iya cewa bata masa ba bale kai a raye.........., "
Ya dan ajiye maganar ya dubi Aban yara da ya zarro ido na mamaki ya ce" Idan har zaka amince, in har zaka yarda, kwarai zan baka shawarar amincewar ta hanyar sake tabbatar maka cewar ba kyauta ce mai dauke da dafi ba, ba kyauta ce da za'a goranta maka ba, ba kyauta ce da zata sa a nemi wani abinka ta karfi ba, ba kyauta ce da zata sa a mayar da kai yaron gida ba....., ka ga nan da ka gani, ina da gida nawa , haka ma Mama tana da nata tantsamemen gidan, kawai shakuwa ta hana mu yin nesa da bayin Allahn nan, domin ba irin yadda bai ba cewar za'a ringa kawo Ni wuni a mayar da Ni na kiya, dan kuwa Ni nan ne dangina, su ne dangina............., kyautatawa ce kawai ya ga ta dace , kuma ya baka dama ka amince da kanka"
Aban yara sai ya rasa me zai ce, ya dubi AUNTYN yara ya fi a irga , ama ta ki dagowa ma bale har ta saka baki a lamarin........
Gaba daya sai ya rasa bakin magana
A kullum jajensa fa, Allah ya bashi dama, Ubangiji ya hore masa abinda zai ringa tara biraguna a hankali a hankali , idan ya tara na daki daya sai su hadu shi da SULaimana su tada daki, sai daya ta koma, kuma in ya tara wani sai ya yiwa dayar, a da fa har ya fara kwatantawa, wani lokaci maman yara ta daga nasa hankali tace idan har yana tunanin fara tadawa AUNTYn yara daki ne maza ya farka, domin babu ta yadda za'a yi tana zaune ya yiwa AUNTYn yara gini ya saka ta ita kuma ace sai daga baya dan karyar dakin AUNTYn yara ya tsufa , rufinta du ya bude......, idan damina ta zo fa dakin AUNTYn yara baya zaunuwa, bale idan ana ruwa da dare sai dai ta je dakin zaure ta rakube, sulaimana kuwa ya kwana a nata dakin yana ta fitar da ruwa....., haka idan lokacin zafi ya zo AKOY inda rana ke bajewa dalll abinta, ya zamo kullum karuwa abin yake yi du irin yadda ake kawo tabarmar kaba a rufa sai a hankali, ga wata uwar tsaga da bangon yayi, a haka ake rayuwar , da yake AUNTYn yaran ta nuna masa kar ya damu idan Allah ya hore a fara yiwa maman yaran idan ta koma ita sai ta shige na maman yaran, a nan ma maman yara ta nuna ai in dai ba daki biyu da falo za'a mata ba babu ubanda zai fitar da ita daga ciki da falo ta koma wani ciki da falon ko kuma ciki daya......, abubuwa dai kala kala da suka sa ya gwammace kawo ido ya zuba mata yake iya yinsa, in damina ta zo AUNTYn yara ta kaura dakin zaure kenan sai damina ta wuce, idan ta wuce aka kwaba laka aka yi mata dabaru kawai sai ta saka labulenta ta rufe bangon, saman kuwa sai sulaimana ya kawo rabarmar kaba ya hau ya yi dabara ya rufe shiKenan sai ta ci gaba da zamanta.......sai ga waga magana rana tsaka???????????
A hankali ya furta " ya Allah......."
Ya sake duban A'isha da farin cikinta ya kasa boyuwa tana rike da hannayensa.................tana jira ta ji yace kwarai ya amince
Ya dubi antyn yara , ya sake duban Malan a hankali ya ce" Malan, wai kana nufin gaba daya gidan za'a rushe a tayar da wani ginin?"
Malan yayi murmushi a tausashe ya ce" haka yace Malan Ahmad"
Aban yara ya dubi AUNTYN yara a hankali ya ce" Rahama, kina jin wani batu dake son tsayar min da numfashi ko?"
AUNTYn yara ta dago idnanuwanta da suka cika da hawaye, a tausashe ta ce" Dama na san, addu'ar da kake yi, Sarkin dake amsawa ya wanzar da AKOY a inda babu, zai wanzar da ikonsa a kanmu muma Aban yara......., kuma har a zuciyata nake jin alkhairi ne idan har ka ji kai ma haka, ka aminta, tabas allhairin ne, idan kuma baka ji hankalinka a kai ba, ka kiya, kwarai abinda ka yanke da shi zan yi aiki "
Malan ya lumshe idannuwansa, kafin ya sake budewa a kan Anna wace ta zubawa AUNTYn yara ido, zuciyarta cike da kara yarda da zabin nata zuciyar itama, kwarai zuciyarta ta kara yarda, kuma ya san koda an yi kutsen lalata a tarbiyar yarinyar, AKOY halaya da gadon allhairin dake fito da kansa koda ba'a shiryawa hakan ba, a yau ta gani da idnanuwanta a kan kalaman bakin yarinyar, kuma tana ji a ranta sangartar ma nada nata alkhairin....dama haka ne, idan ka rike Allah, abinda ake ganin cutuwa ce ake yi maka Allah zai juyar da shi ya zamo cutuwar mai tafe da alkhairi a gare ka