Sashe 96
Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Dakatawa yayi, sai da ta fito sannan ya shige din shi, hakan ya sa ta bi bayansa da kallo ta juyo tana dan zarro ido da alamun lalle sun tabo mata rikici yau a gidan nan ta kai dubanta inda FARHANA ta fito da gudu , A'isha na bayanta, Nur kuwa, sam sai ta ki hayowar, jikinta yayi wani irin mutuwa ........
Suna zuwa Farhana ta rungume Anna ta fashe da wani irin kuka mai fitowa tun daga cikin kirjinta........,
Wajen dama mutanen iya su ne, hakan ya sa Anna bata ja ta ciki ba tana duban Aliyu ta furta" Me yake faruwa ne haka?"
Aliyu cikin takaici ya ce" Wancen ya kai su wajen Jafar, shi ne sir ya kama su a cen"
A zabure Anna ta dubi FARHANA tana buɗe ido ta ce" Wajen wa?"
FARHANA jikinta na rawa ta ce " Anna, na kasa samunsa a wayar ne, Anna na yi na yi in same shi a wayar ne na kasa, shi ne muka je dan mu fada masa sakon ki......"
Anna ta rintse idannuwanta, kafin ta bude ta ce" Kina nufin, yayanki na gari kika tarda yaron nan inda yake?, kin yi kunar da yanzu shi din ma Bakya tsoro?"
Hankalin Nur ya tashi, haka ma na A'isha
Da sauri Nur ta dubi Aliyu da tarin jin haushinsa ta maido dubanta kan Anna ta ce" Ba fa abinda ya kai mu ba kenan Anna, ba abinda muka je yi ba kenan, zuwa muka yi dan mu fada masa ana neman shi........"
"Ki min shiru a nan Nur!" Anna ta fada a tsawace, kafin ta ja ta nuna musu ciki ta ce" Ku wuce min ciki, ku wuce yanzu yanzun nan!"
Sumui sumui su FARHANA suka fara shiga, kafin Nur ta shige ita ma saboda duban da Anna ta yi mata
Anna ta dubi Aliyu ta ce" Kar ka yi masa komai, kai kuma ka tashi ka je ka wanke fuskar ka, idan ba Anas ba yaya za'a yi ka yiwa yaran nan biyayya?, ka je ka huta ba wani kora tashi ka tafi"
Anas ya mike yana ta haɗa hannayensa yana yiwa Anna godiya, ita kuma ta dakatar da shi ta hanyar daga masa hannu ta shige ciki ranta bace ta nufi inda yaran nan suka zauna suka layu
Tana zuwa ta tsaya tana duban su da yanayin fada ta ce" Wayon ku kenan? Ni na aike ku neman sa ne? Da baku same shi a waya ba ai ta dan yadda ake yi tana samunsa a wayar ko?, shi ne zaku tashi ku je gidan su saurayin da ake so ya fito a musu aure ku ce me?, so kuke yi iyayensa su ce ba zasu baku shi ba tunda ku ne kuka damu da shi?.....,ku min shiru da kuka a nan ko in sasaba maku kamani....., dama du baku da hankali? Daga cewa ku je ku yi gyaran gashi ne kuka je kuke neman hadawa kanku fitinar da ta fi karfinku, Subahanalah Farhana sam ba zaki taba jin maganata? a kan yaron nan sai kin hada Ni da hawan jini????"
A rikice Farhana ke girgiza kai, Nur da A'isha ma du sun fita a hayacinsu..................
Mikewa yayi a hankali ya kamo Anna a tausashe sosai ya furta " Ki yi hakuri Anna, zo ki zauna, bana so ki mata kuka plz"
Kujerar ya karasa da Anna, suna zaunawa FARHANA ta rarafa ta rike kafafun Anna tana kuka ta ce" Anna, ba abinda kike tunani bane, ba zan taba aikata haka ba, kawai ina cikin fargaban yaya ya min tambayar ina yake in rasa amsa, shi ne muka tafi, dan mu sanar masa ne kawai Anna dan Allah ki yi hakuri in sha Allah ba zamu kuma ba, dan Allah ki yafe mana Anna"
Anna na dubanta tana rike da hannun IMAD ta ce" ki ma kuma, ki ma kuma FARHANA, ai a kan yaron nan babu abinda ban gani ba da ke, Nur zo nan, taho nan, shi ne kika bi ta ko? Zo nan A'isha, shi ne kuka biyeta ko?"
Su ma karasawa suka yi, a hankali A'isha ta ce" Anna dan Allah ki yi hakuri..........., ki yiwa Farhana uzuri Anna ki yafe mana"
Nur kam a hankali ta ɗora kanta a cinyar Anna saboda ta rasa yaya zata yi da ranta, gana daya jikinta ya dau zafi ma, ji take yi kamar zata sike
A hankali ta fashe da wani kukan ta ce" Anna du fa ba laifinsu bane, Anna Ni ce na masa magana ya kai mu, kuma na ce masa ne ke kika aike mu, Anna, du laifina ne Walahi ba laifin Farhana bane, sai ma da tace ƴaƴanta na iya bata rai idan ya ji sai nace ba fa zama zamu yi ba, kuma Ni ma ban yi haka dan na raina shi ko dan in sa ta take umarninsa a kanta ba, ina tausaya mata ne tace an ce tace masa ya fito.......kuma kwana shida kenan bata same shi ba, Anna dan Allah ki saka baki kar a kori Anas, bashi da laifi shi ma, Ni ce mai laifin Ni ce za'a hukunta, ba mai laifi a nan sai ni !"
Du irin yadda yake hana kansa bayanuwar bacin ransa sai da yarinyar nan ta sa ya bude baki a kausashe ya ce" Idan kika yarda, kika kuma budar baki a nan, sai na maki hukuncin da hankalinki zai tashi HALLAH!"
Yana ajiye maganar, wajen yayi shiru, Anna kam da sauri ta Dube shi
Rai bace ya dubi Farhana ya ce" Har yanzu kina kan bakanki na shi zaki aura in koma in duka in roke shi ya haɗa da ke ya aure ku, ku uku?"
Da sauri Farhana ta sada kai, jikinta na rawa, hankalinta na kara tashi, kwarai tana son dukawa ta nemi yafiyarsa Ama ta san ba yanzu ba, ta san a yanzu kam ya kai kololuwar bacin rai, dan haka sai kawai ta lalubi hannun NUR ta jimke a nata
Hannayen nasu ya bi da kallo, kafin ya dubi Anna yana lumshe ido a hankali ya furta" ki shirya taron daurin aurenta, haka su ma....zan je in samu Aba, idan suna da tsayayu zan hade ........, za'a daura musu aure su duka nan da sati biyu, ......."
Ya ajiye maganar a tausashe sannan ya kai hannun Anna wajen kirjinsa a hankali ya ce" I'm sick......, zan je in ga docter "
Daga haka ya mike ya juya ba tare da ya sake bi ta kan yan matan nan ba da du suka firgice suka bi bayansa da kallo
A rikice Nur ta ce" Aure kuma? Nan da sati biyu kuma?, innalilahi bari in tashi in je gida"
A kausashe Anna ta ce" Ba inda zaki je, Ni zan tashi yanzu in je gidan in samu su Aban naku, maza ku wuce min sama a maki lesson, wannan shi ne hukuncin rashin ji, sai ku fitar da tsayayu a daura maku aure, domin Ni da kaina abinda zai fitar da Ni yanzu kenan, karya kuke ku ci gaba da daga mana hankali, ku dukan ku!"
Daga haka Anna ta mike ta fara Bara musu falon ta yi ciki
Nur ta mike ya kai sau uku kafin ta ɗora hannayanta saman kai ta cire dan kwalin ta wurgar ta nemi bajewa a kasa dan aikata burgima, domin tuni ta kai kasan tana ihu ta ce" Aure,? Innalilahi, to? Wani irin aure? Dan girman Allah kar a aura min Anas a yanzu, a bari ya zama namiji, a gabana Anas ke kuka saboda aiki, dan Allah a bari ya zama namiji, Walahi in aka aura min shi a yanzu yanzu na raina shi.....wayo Allahna aure? Ni gaskiya wajen Auntynmu zan je, wajen abanmu zan je, kun ga tafiya zan yi!"
Cike da jin haushi A'isha da ta tare ta saboda Mutalab da ya shigo sakamakon bashi damar hakan da IMAD yayi a yanzu da ya fita , cewar ya je su kara shiryawa sannan ya sanar a gida cewar idan sun shirya nan da sati biyu yake so a yi komai........ne ya daka birki yana dauke kansa daga kan Nur dake burgima a kasa ya tsaya yana kallon Farhana da ta tafka tagumi hannu bibbiyu cike da tarin tausayinta da kaunar ta a zuciyarsa
Rai bace A'isha ta ce"Rai bace A'isha ta ce" Wai ba zaki mike daga burgimar nan bane??"
Nur ta girgiza kai, tana ture hannun A'isha ta ce" da kin san ciwon kanki ke ma da kin yi burgimar nan, yaushe ma aka haife ni? Waye ma yace Ni ina da tsayaye?, to wai da wa za'a min auren? Gaskiya saurayina yaro ne, sai mun zauna da shi na masa fada gaskiya ba mai min aure da wurin nan, wayo Allahna........."
Sai kawai ta sake gangarawa daga saman cafet din tana ihun nan har ta ji ta daku da wani abin......
Bude ido ta yi dan ta ga ko kujera ta kaima karo, idannuwanta suka sauka a kan fararan yan yatsu tatas kamar na jariri Dan hasken fari da kyan kallo a ido
Da sauri ta zauna saboda yadin da ta gani ko hauka take yi zata gane ko na waye..........saboda a yau yadin nan da yan hananyenta tana iya zana shi a takarda idan aka ce ta zana
Kawai a tsaye yake yana kallon ikon Allah
Kuma shigowarsa FARHANA kanta bata gani ba sai A'isha da ta mike a tsorace tana kallon Nur tamkar ta dura mata ashar, sai dai ba hali saboda turus kawai yayi yana kallon ikon Allah
Dif falon ya sake dauka,
Ya yi mata kallon second goma bayan ta zauna tana jan rigar dake jikin ta tana gyara jikin nata kafin ya zagaye ya je wajen kujera ya dauki hularsa da ya ajiye ya bari tsabar ana neman lalata masa nutsuwa da kwanciyar hankalinsa
Hular ya dauka yana sake duba kiran Anna dake shigowa a karo na biyu, saboda tunda ya fita take kiransa dan ta ji menene yake damunsa? Yace zai je ya ga likita me yake faruwa da shi? Ya sanar mata idan ya je zai ji, sai kuma ta sake kira