← Book details Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 141

Sashe 12

Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daga haka ya dau samirar abincinsa ya shige dakin auntyn yara , ita kuwa ta kara hasken fitilar kwonta ta bude musu kwanon ta kawo masa ruwa ya wanke hannunsa suka shiga ci tare, bale da ya kula kamar bata son ci sosai din nan sai kawai ya ringa tursasa mata har sai da ta koshi sosai sannan ya kyaleta hakanan yana mamakin auntyn yara ba zata taba girma da yan rigingimu ba irin na tabara, wanda hakan ke sakawa a kulun yake Dada yi mata uzuri du irin laifukan da take yiwa mama wa'inda maman ke fada kullum ta Allah, sai ya tashi da karfi zai salameta ma sai ya ji tausayinta ya kama shi, idan ya salameta ina zata je? Ai ko ya rabu da aurenta baya jin in zai rabu da ciyar da ita da kula da lafiyarta a karkashin innuwar gidan nan, gwara dai a ci gaba da mata fadan da nasihar ta yiwu idan ta kara girma ta daina rashin ji. ( ita shagwaba a gaban miji na sakawa mace har su kai ajiye jikoki a duniya yana yi mata kallon yarinya karama, har ta tsufa a idannuwansa da zuciyarsa yarinya karama zai ringa daukanta, anfanin hakan kuwa shine idan har yana daukan ki a yarinya karama tabas zaman sai ya fi armashi, zai ringa yiwa duk wani abu da zai shiga tsakanin ku uzuri na bacin rai, zai ringa mararin yin fira da ke yana murmushi , zai zamo yana tsokanarki ne idan kuka zauna dan kawai ki masa yar rigimar nan yayi dariya, zai zama alkali tsakanin ki da kowa ne, zai zamo baban malami , baban masoyi a duniyar ki.........😁🤌🏻)

Maman yara sai da ta ga sahu ya dauke sosai da sosai sannan ta shige ciki ta tada Imtee ta fito da ita falo suka zauna

Kasancewar Imtee bata da nauyin barci ko kadan , nan da nan ta wartsake daga barcin da take yi tana kallon mama hankalinta na neman tashi dan ta tabbata ba lafiya ba

Mama na dubanta ta ce"💅💅💅💅💅💅💅💅💅💅
*KISAN MUMMUƘE*
💅💅💅💅💅💅💅💅💅💅

_PAID BOOK_

*BY*

_SAJIDA NIJAR_

*Yan Naija Mutanen mu 1k ne a kan wannan account number 0225962748 Amina Maikudi Abdullahi GT Bank* sai a bani shedar biya ta layi na kamar haka +22793811618

*Yan Nijar mutanen mu zaku turo da hoton kati ta airtel ta dala dari , wato 500francs cefa a kan Numbarna kamar haka +22793811618*

*Na gode, sai kun zo.....taku ce SAJIDA NIJAR*

Na zo muku da alkhairi ......, Zance ne a kan Meta Force, wanda muka ci, muke kan cin ganiyarsa a kwonce a dakin mu ...... Bismillah

*JAMA'A NAZOMUKU DAWANI TSARI NASAMUN KUDI TA HANYAR AMFANI DA WAYAN HANNUNKU
WANNAN TSARIN SHINE METAFORCE

MENENE KASUWANCIN METAFORCE* ????

*Metaforce kasuwancine ingantacce halattacce Wanda yake biya 100 💯 Wanda ake Gudanar dashi da wayar hannu,METAFORCE is also a part of network marketing,is a 100 percent decentralized project da aka daurasa Akan Blockchain technology Wanda babu wani mahalukin daya Isa YAYI editing,hacking ko deleting wani abu acikin sa,Kuma yanada matakai yanada rassa Wanda kowane reshi ka rike a METAFORCE to ka samu GUDUMAR DUKAN TALAUCI*🌎

METAFORCE ANASAMUN KUDI ACIKINSHI SOSAI MATUKAR ZAKAYI ABUNDA AKEBUKATA

zaku iyahada miliyoyin kudi aranadaya acikin wannan kasuwanci me albarka in sha Allah

Duk wacce tashirya zata iya tuntubanmu akan wannan number
09136899615
Hajja Data
*7*

Maman yara na dubanta ta ce" Ban ji da kyau ba batun saurayin da kuke yi ke da A'isha"

Sai da Imtee ta sake jin ta wartsake sosai , domin yawanci kawayensu sukan nuna idan suka yi saurayi iyayensu na masu fadan a taka a sanu, a kula, a bari a kara girma kafin a fara tunanin yin kule kulen samarin nan, wasun kuwa sukan ce gaba daya an musu fadan da ba zasu kuma yinkurin kula samarin ba sai dai mijin auren su, hakan ya sa ta dan daburce kafin ta shiga kame kame ta ce" Mama, am, dama, ehin, um, dama fa yayantan nan ne , wannan da akace yana aiki a gidan cen na bayan layin nan, shine wai yake wasu abubuwansa, ama Walahi Walahi mama ni babu wani abu da yake iya sakawa in yarda , banma kai soyayyar ba ai!"

Gaban Mama ya kara yankewa ya fadi, zuciyarta ta nemi sake cinkushewa da wani baki......, kai, soyayya? Saurayi ne Imtee zata yi A'isha ki sinsinowa bata yi ba? Saurayin ma mai wani mukami ? Yaya za'a yi zuciyarta ta iya daukan wannan lamarin......?, yaya za'a yi tana ji tana gani rahama ta fi ta da wani abin??????

Ta jima da ta yi shiru, tana ta sake sake, lokaci daya ta samu kanta da yin murmushin gefen baki a lokacin da ta ji a ranta kwarai wannan din ma wata hanya ce da zata iya amfani da ita dan ta sa zuciyar rahama ta kumbura, ........tabbas Idan har ta iya takunta wannan hanyar itace ta fi dacewa da itadasa cuzgunawa Rahama bakin cikin da zai sa zuciyarta ta kumbura.....

"Mama, dan Allah ki yi hakuri, in sha Allah Ni ko inda yake Bama zan yarda in kala ba, Ni da kaina na san ban kai wajen nan ba mama sai na girma ki?????" IMTEE ta fada a raunane , dan shirun na mama ya yi yawa

" In ji uban wa? Innalilahi Imtee me kike fada? Baki kai soyayya ba so kike yi in kwada ki in cinye ko so kike ki tsofe min a gidan nan?, wani munafukin ne ya saka maki wannan shirmen a kwakwaluwa bayan ƙatuwar budurwa kike gakinan komai ya bayyana ya gama nuna? To ahir din ki, kar na kuma jin wannan batu, da ace ma wani sakarai marar katabus ne Bama zan yarda ba, dan nan da kika gani ban ga amfanin badi ba rai ba, ba zan taba yarda in bari ku kula banzan namijin da bai ajiye ba bai ba wani ajiya ba irin Sulaimanan gidan nan, asara ce, fitina ce, tashin hankali ne auren talaka, sai ma ka zo zama da shi kunci yayi kunci ga shegiyar gabar tsiya da fuska uwa kunun safe, ba'a saki fuska ba bale a ji dadin zama sai dai a kare da auro wata karshe ma a koro min ke ina ciyar da ke da ya'yansa, ki ji da kyau gobe in sha Allah da Yama zaki koma ki yi alamun kin zo ku gaisa da kawar taki, ki tabatar da kin zauna har ya shigo sanan ki maido batun soyayya, kin ji ni da kyau?" Maman yara ta karashe tana riko hannayen Imtee da ta yi suman zaune jin hudubar mamanta ta sha bamban da ta iyayen kawayensu da suke fadin an fada musu ..........

Tausasa murya sosai Maman yara ta yi tana dubanta ta ce" Ai na san cewa kin san du duniya babu mai son ki sama da Ni ko? Kin yarda da Wannan ko?"

A hankali Imtee ta gyada kanta tana sauke boyayiyar ajiyar zuciya

A tausashe maman yara ta ce" to ki kara yarda, Ni MAMANKI baki da wani sama da ni a duniyar nan, baki da wani wanda ya san ciwon ki sama da Ni, haka kuma shekaruna sun tabbatar maki na fi du wani makusancin ki sanin duniya da abinda ke cikinta ko?"

Imtee ta gyada kai zuciyarta na fara amincewa da batun Mama

Maman yara ta murza hannayanta kasa kasa sosai ta ce" Maganar ba zaki amshi abin hannunsa ba, kanmu ne zamu cuta, kuma idan Allah yayi shine mijin ki Walahi ba zai baki ba in ya aure ki, kin kuwa san irin burin da na ci a kanki? Burina ki samu mijin da zaki huta, burina ki samo miji mai kudi Imtee....."

Ta karyar da muryarta sosai ta ce" Ki duba ki ga a dakin da muke, ki duba ki ga yadda nake wahala idan ina son siya Miki dan kwalli sai na yi ta asusun kwana da kwanaki kafin in damu yadda nake so in siya Miki, ina so in ga kin yi kudi, kin dauke Ni daga Ni sai A'isha mun yi tafiyarmu, mu bar wancen da baya son mu da kuma wace ya zaba fiye da mu su yi ta zama a wanan wahalalan gidan kin ji imteena????"

A hankali bayanan ke ratsa zuciyar Imtee, har ta ji a ranta kwarai zata iya komawa goben, sai dai bata san idan ta koma din yaya zasu kwashe da shi ba, abu daya ta sani shine a gaban nan idan ya bata kudi tabas zata saka hannu ta karbo ne.........

Sai da ta tabbatar cewa ta gama dorata a kan abinda take so ta salameta kan ta koma ta kwonta,

Ko da Imtee ta koma ta kwonce zuciyarta cike da sake saken abubuwan da zata daura aniyar yi dan ganin ta cire mamansu daga kangin talaucin nan da ta tsana fiye da komai, ita maman nasu, ciki kuwa farkon matakin shine ANAS.

*Saudi Arabia, aéroport international din sarki ABDUL AZIZ na JIDA*

Karfe biyar na yama jirgin su ya sauka a wannan baban birni , wanda ya dauki yan lokuta kafin ya gama tsayawa a wajen da yake tsayuwa bisa jagorancin ma'aikacin kasa dake tsaye yana yiwa matukin jirgin alamu da magana da Yaren turanci dan sake nufar da shi inda zai tsayar da jirgin sa cikin nutsuwa
Chapter 12 · 0% Book details