Sashe 65
Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
A hankali rana ta ida fitowa, lokaci ya ringa ja har karfe goma na safe ta yi, shi din ma bai shigo ba bale su Aba......, zuwa yanzu kam su Dukansu zuciyoyinsu sun gama karaya, hankalinsu ya gama tashi fiye da kima....., bale da Nur ke duba karamar wayar abansu tana ganin time sai kawai ta dubi auntyn yara ta ce" Auntynmu......ko in tashi in bi baya Ni ma? Sha daya har ta wuce Aunty"
Da sauri auntynsu ta girgiza kai tana dubanta hadi da riko hannayen ta ta ce" a'a, ba zaki je ba, idan fa an sace su? Kema sai a sace min ke?, a'a ku zauna ke da y'ar uwarki, bari Ni in je, idan kuka ga na dauki awa uku ban zo ba ku bude mamanku, ku duka ku mata kuka ku mata magiya in sha Allah ba zata kashe ku ba, in sha Allah zata kula da rayuwar ku, ku zauna in zo"
Yanzu ne ai suka ainahin idasa rikicewa, sai kawai suka saka mata kuka sunna rike hannayen ta tana kokarin zaunar da su suka ji an bude dakin soro da karfin tsiya
A tsorace auntynsu ta mayar da su bayanta ta zubawa hanya ido , saboda daga dakin ta ba'a iya hango soron kofar, haka kuma suka yi shiru sunna jiran gadowar maman yara dakin da wukar nan, kowane ya yi shirin ko ta kwana domin a cikin su babu wanda zai yarda a cimma ɗan uwansa , ita ma auntynsu kuma ta gama sakawa ranta sai in maman yara ta kashe ta zata cin ma ƴaƴanta!
Da sauri ya nufo dakin yana fadin" Officer bari in kirawo su"
Ya karaso yana duban yadda suka yi tsuru tsuru ya shigo dakin yana duban Mama ya ce" Mama, ku fito mu je, su Aba ashe a hannu suke, maganar da nake maki zuwan da suka yi jiya ashe da suka fadi abinda suke nema, da ranar da lokacin da komai da aka dauko litafin da ake rubuta komai aka duba aka kara dubawa basu ga sunan mama ba da tace a cen ta haihu , sai kawai sunan wata mata zuwai da ta haihu a ranar a nan, wace case dinta ke nan , ba wanda bai sani ba wai, a ranar da aka fada a irin lokacin aka dauke mata y'arta wai........, maganar dai da nake maki da aka yiwa su aba tambayoyi kawai aka kai su aka rufe sai yanzu da safe da inspector ya zo aka zauna da su ne har aka dauke su aka je gidan mutanen.....ku fito dai mu je kawai"
Gaba daya suka biyo bayansa saboda du a gigice suke dama...., shi ne ya rufe ko'ina har gidan sannan suka nufi motar dake tsaye bak'a sidik dauke da polise biyu, sai kuma wace ke dauke da sojoji , ya je ya sanarwa sojan dake cikin motar nan cewar iyayen nasa ne, sai kawai aka ce su je bayan motar nan su shiga, wace idan ka yi laifin nan ake dauko ka a ciki, mai terere din nan .....ya zamo cikinta suka je suka shiga, har sai da ya kama auntynsu wajen hawa ta shiga din sannan ya shige shima ya kuma rike hannun auntynsu , hadi da na A'isha sannan Nur ta ɗora kanta a saman kafadarsa zuciyarta cike da kunci tana kallon mamanta da kanta ke saman nata cinyoyin , gaba daya tsufan ya idasa fitowa, hankalinta du ba a jikinta ba, hakan ya sake karya mata zuciya sosai da sosai
Tashin motar suka yi suka dauki hanya.................
Idannuwan Nur a saman hanyar nan har suka nufi wajen da ta tashi tana hange Ama kafaffuwanta basu taba shiga ba....................
A hankali ta dubi sulemana a lokacin da suka karaso baban sojan nan ya fita ya sake nuna katinsa aka bashi damar shiga ya koma motar suka yi cikin gidan bayan an bude musu ya zamo Nur ta zauna tana bin gidan da kallo a raunane ta ce" Sule, ina ne nan???"
Sulaimana ya harareta kafin ya ce" Inda kika aike mu ne!"
Auntyn yara itama a tausashe ta ce" Sule, ka bamu amsa, ina ne nan? Na zata polise station din za'a je da mu?, Sule gidan nan ba shi bane na bayan layin nan namu???"
Sulaimana zai bata amsoshin tambayarta aka bude musu wajen sauka aka umarce su da su sauko........
Saukowar suka yi, sannan aka sauko da maman yara hananyenta da ankwa a daure, hakan ya sa Nur duban A'isha a rikice ta sake duban maman yara a lokacin da aka sa suka je kofar wani tamfatsetsen falo, a rikice ta ce" A'isha.........., ankwa ce a hannun mama.....A'isha ankwa ce a hannun mama??????"
FARHANA dake tsaye a baya daf da falon su, tana sauraron Murtalab da ya tare ta yana mata zanceceku saboda ita fitowa ta yi daga falon sakamakon bakin da aka yi suke zantawa da yayanta, hakan nea ya hana su fita makaranta da wuri yau, gashi har sha biyu zata yi, sai kawai ta tsinkayo Muryar NUR, hakan ya sa da sauri ta shanyo kwanar tana sauke dubanta a kan mutanen dake wajen da kuma nur wace kanta ma ke waje saboda hijab din wuyan ya mata girma, haka kuma daga kasa kamar zai tade ta ne ta fadi, du ba a hayacinta take ba, du a gigice take, .......furkarta ta yi fayau da ita , karan hancin nan ya sake fitowa zuwat da shi.......lebunanta kuwa sun yi pink sosai kuma sun bushe kamasss
Da mamaki bayan ta karaso , haka ma Mutalab da ya biyo bayanta ta ce" Kandalar Anna ?"
Da mugun sauri Nur ta juyo jin Muryar FARHANA
Farhana ta nufo ta hankali tashe, kamar yadda ita ma ta nufo tan suka kama hannayen junna
Farhana hankalinta tashe ta shiga duduba fuskar HALLAH da ta yi fayau kamar wace bata da jini a jikinta a lokacin da sojan nan suka yi magana shi da Aliyu ya sanar masa su jira har a bada damar su shiga, dan haka ya musu alamun su ja baya su jira din nan, Ama kuma sai bai yiwa su farhana da Hallah ba, wace a hargitse ta ce" Kandalar Anna lafiya? Me yake faruwa ne na ganki da sojawan nan da yan sanda?, magana kuka tabo? To Ama in maganar ce ma kuma nan za'a kawo ki???, innalilahi ke zo mu je wajen annar ki"
Sai kawai ta ja hannun ta suka nufi hanyar baban falo
Duda Aliyu na tsaye bata tsaya ta bi ta kan alamun su tsaya da ya musu ba, sai kawai ta ja ta da sauri suka yi ciki , shi ma ya bi bayan su dan ya fitar da su......, sai dai sunna shiga Anna ta dago dubanta daga sauraron abin tausayi abin firgitarwa da da Aban yara ke fada bayan Malan mijin mama ta gidan ya gama yin nasa bayanin du abinda ya faru a ranar, shi ma sai yake bada nasa bayanan dala dala suka ji an shigo da sauri
Niyar Farhana ta wuce hanyar matakala ba tare da kowa ya gansu ba su haye sama, sai dai dagowar da Anna ta yi ta ga Nur da Farhanan a yanayin nan kirjinta ya buga da tunanin kenan dai Hallah din ce ba yar bawan Allahn nan ba? Ya Allah
A tausashe Anna ta furta" NUR?"
NUR na ganin Anna, bata tsaya wata wata ba ta karasa da sauri ta kai gwuiwowinta kasa a gaban Anna ta ɗora kanta a saman cinyarta ta fashe da kuka tana rike hannayen Anna dake riko ta itama a rikice ta ce" Anna, kin ji wai an rufe abanmu, kin ji wai an rufe abanmu, wai an ce aishana ba yar abanmu bace, wai an ce satar ta mamana ta yi, Anna sun sakawa mamana ankwa , Anna kin ga sun zo sun sako mu a mota kamar barayi, Anna kashe Ni zasu yi, mutuwa zan yi Anna wuyana wayo Allahna "
Farhana dake tsaye ta gyada kai tana tabe baki kafin ta dan saci kallon Ƴaƴanta......
Ganin idannuwansa a kan Anna din shi ma saboda abin kamar daga sama da irin yadda hankalin Annan ke neman tashi ya sa ta karasa ta kama hijabin na Hallah tana dubgureta a boye kasa kasa ta ce" Ba dole wuyanki ya rike ba, dila daga Ni in cire maki, ba fa mala'ikan mutuwa bane ya dafata Anna hijabin nan ne ya tumurmureta, Dilla daga Ni in janye!"
Sai yanzu Anna ta kai dubanta itama tana fitar da ajiyar zuciya dan wallahi ta Tsorata
Ita din ma Hallah da Farhana ta ja hijabin sai da ta ji numfashinta na dira da kyau, tana fitar da ido tana laluba wuyanta ta furta" Au, walahi na zata zuciyata ce ta buga, kuma har abin wukar yankan wuyan da ake yi na fitar rai na ji a wuyana shi yasa nake fadawa Anna komai na san zata bi baya......."
Sai kawai Farhana ta dibe hijabin nata gaba daya tana duban ta zata yi magana idannuwanta suka sauka a kan rigar dake jikin Hallah, wace ita gaba daya kanta ya fasu, sam ba ta nan take ba
Da sauri ta waiga wajen yayanta, sai ta ga a lokacin ya dauke idannuwansa daga kansu ya sauke kan Aliyu da yan yatsun sa biyu ya masa alamun yin baya....., ai kuwa Aliyun yayi bayan da sauri ya koma
A tsorace Farhana ta sakar mata hijabin kasa ta ce" innalilahi zir kike yawo????"
A firgice Hallah ta kali jikinta, domin wani tsoro ya kamata kar aje hijab din ne kawai a jikinta ........