Sashe 61
Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hankalin ANAS neman mugun tashi yake yi, ya zauna da kyau yana duban mamansa ya ce"Mama, du fa baki gane wacece Nur ba, shi yasa kike tunanin har bata so na ko kuma bata da tarbiyya, kuma Mama har ki ce ta nuna zata bige ki a ina? Zuwanta gidan nan ina ce bai fi sau daya ba? Ko akoy ranar da ta zo har ta maki rashin kunya ban sani ba????"
Ya yi tambayar yana dubanta
Shiru ta yi ta kasa cewa uffan
Ya sauke ajiyar zuciya ya ce" Mama, irin yarinya mai tarbiyyar NUR sun yi ƙaranci a zamanin nan......, ba kowani namiji ne yake son da ya latsa a bashi....., mama yan matan nawa nawa ? Du wace na tare na nuna ina so kamar wace ke jira kawai sai ki ga har yarinya na kirana a waya , hakan na nufin kowani gaja fa ya tare ta zata bashi damar su yi soyayya ne, ga tarin rashin sanin ciwon kai, mama na rantse maki kaf din su da ina zina da na saka ki uku a gidan nan da kukan jarirai......, ki yi hakuri gaskiyar kenan, ina daraja a nan? Ina sanin ciwon kai a nan? Ina tarbiyya a nan?, mama har yanzu bamu yi zance ga Ni ga ita daf da daf ba bayan iyayenta sun bamu damar hakan......., mama quality dinta da yawa wa'inda suka isa su sa in jure ta shiga hannuna....idan ta shiga hannu na in tana so karma ta so nin, Ni zan mana son na Ni da ita gaba daya....., yanzu kam ki yi hakuri Ni ita na zaba ita nake so, kuma ita nake so ki so, ki shirya gobe ko jibi in sha Allah in na sauko zamu je ki gaishe da iyayen nata, kawai sai ki sako maganar ina so in turo magabata na, kin ji mama? Bari in yi wanka shop zan leka in muku siyaya da ita ma, ta yiwu in na kai yau a amsa, idan ma basu amsa ba zan kawo in tara mata cikin kayan da nake ajiye mata a dakina......., Ni ba ruwana da wata diyar iyayenta in dai zasu bani a yanzu na kai matsayin da zan iya da su baki daya, ina zuwa"
Ciki ya wuce jikinsa har yana bari, saboda Bama zai dauki maganar wai wani ta sako masa maganganun ba zai auri IMTEE ba!, shi fa bai ga wani aibun IMTEE ba gaskiya, ko me ta yi har zuwa yanzu gaskiyarta da dacewar ta da shi ya gani, dan haka kawai hakuri zata yi ta so ta, dan iyayenta basu da shi shikenan sai ta tsane ta??? Hum.
Kisan mummuke 36
Maman ANAS kuwa suman zaune ta yi cikin tunani mai zurfi gaske har ya fito daga dakin ya wuce , su Fa'iza suka shigo cike da murnar mota , ta zauna tana fadin" Mamanmu baki fita kika ga motar Ba fa"
Maman su ta Dube ta , ta ce" Fa'iza ke ta mota kike?, Fa'iza anya yarinyar nan ba asiri ta yiwa yayanki ba?"
Fa'iza ta dubi mamansu da yanayin rashin jin dadi dan ta san tatsuniyar gizo bata wuce ta koki ,ta ce" Asiri kuma Mama?, a ina IMTEE zata iya yin wani asiri Mama?"
Mamanta ta Dube ta cikin daurewar fuska ta ce" kanwar uwarki ce ita da har zaki daure mata? Ko da ita kike kwana daki daya?, to bari ki ji idan bata masa asiri Bama to maya ce, dan na rantse maki yanyanki ba a hayacinsa yake ba......, wato ma Ni zai dauka ya kai gidan da na je muka yi uwaka ubanka da iyayenta da ita? Ni kam na ga jaraba ganin idona Fa'iza kin janyoin jangom!"
Fa'iza na duban mamansu a dan tsorace ta ce" Mama ina kika je kuka yi fadan wai? Mama na dai gidan su Nur ba? Innalilahi mama gidan su kika je kuka yi ba dadi????"
Mamanta ta sakar mata harara ta ce" Ke tashin min daga nan dan Allah, tashi kawai ki bani waje, iskancin banza, sai ya kai nin in gani, ko kuma sai ya auretan in gani, ai kuwa da sai dai bayan raina in har ya auri yarinyar nan!"
Fa'iza ta mike jiki ba karfi ta nufi kicin din su ta zauna ta shiga feraye doya zuciyarta a cinkushe.....
Ita fa bata ga wani laifin ƴaƴansu ba,
Kwanaki ne take jin haushi da ganin laifinsa a lokacin da ƙarara IMTEE ta nuna bai yi mata ba saboda Na'ima ta zageta ta ringa gasa masa aya a hannu, har ya zama kamar zai zauce dan tunani da saka damuwa a rai......, daga baya da ta hakura kuma komai ya zama normal sai ta daina jin haushin itama ta sauko.....domin yanzu ko a makarantar tana kula shi kuma a mutunce......., kawai mamansu bata sonta ne dan du a cikin yan matan da yayi ba wace iyayenta basu da shi kamar Imtee, haka kuma ba wace bata ringa biyo shi tana nuna masa soyayya ta hanyar yiwa mama da su kansu hidima, shi kuwa yana wulakantata ba sai IMTEE da sam bata ma nuna wannan ba ................., to Ama me kalaman mama ke nufi? Hala gidan su IMTEE ta je ne suka yi wani abin rashin dadi?????
Da sauri ta girgiza kanta a ranta ta ayyana ' A'a, da ace ta je gidan su Nur da ta Nur ko A'isha daya ta nuna min hakan, saboda sam basa hada lamarin iyayensu da kowa a duniya....kai irin yadda Nur ke daukan lamarin iyayenta na tabbata da ta haramta ya'yan nawa....., sai dai in a yau ta je , a yau kuma ai bata je ko'ina ba, sai dai in tana da niyar zuwa....in kuwa haka ne zan sanarwa yayanmu dan ya hana ta, dan in dai ta je ta yi wani abin da zai zubar mata da girmanta ta gama zubar masa da nasa girman shi ma a gidan da yake neman aure ai, kai wallahi Ni mama har mamaki take bani, ko bata ganina a gabanta ne? Idan aka min haka fa???? Hum'..............
Anas kam shi yake shagali, domin siyaya yayi ta mamaki dan ya kaiwa Nur siyaya irin ta abayoyi da takalma da hijabai kamar zai hada dan karamin lefe domin harda turaruka da kayan kwaliya.....kai kudin da yake jibgewa dan yayi gini ya tsakura ya kashe mata sosai ya kudurta sauran na neman aurenta ne da duk bukatunta domin maganar gini kuma ta kau ai yanzu...............
Cike da zumudi ya nufi gidan bayan ya yi sallar isha'i
Ya yi haka ne dan ya samu Aba a gidan , dan burinsa ya bashi dama ta amshi kayan nan
Yana zuwa kofar gidan ya kashe hasken motar sakamakon mutane uku da ya gani a kofar gidan a tsaitsaye sunna magana
Shi ma Aban yara dake ta dauki ba dadi da yaran sai ya samu kansa da rage murya sosai ya ce" ina ga manemin auren y'arka ne, Wato HALLAH"
Malan ya waigo lokacin da Anas ya karaso yana rage tsayinsa kamar zai duka hadi da basu hannu suna gaisawa kafin ya dan soke kai da mamakin wai dama mutumen na uku SULaimana ne? Wato yayan NUR, shi kam ai kamar ma ya shiga uku ko?????????
Da girmamawa ya sake gaishe da malan bayan Aban yara ya gabatar masa da shi yana sanar masa baban su Nur ne, shi ne baban amininsa kuma shi yake musu alwali
Sosai suka gaisa malan na ta addu'a da sanya alkhairi a lamarin kafin Malan din ya ce" A yi maka magana da ita ko?"
Anas cikin sune kai ya ce" A'a baba, ai Bama zancen dare da yawna nake zuwa, dama abin alkhairi uban gidana ya min, kyauta irin ta daraja , mota da gida , shi ne nima na je na yi mata siyayya dan itama in yi mata mata kyautar, shi ne na kawo da fatan dan Allah a taimaka a amsa kuma a bata dan Allah baba, ka yi hakuri ba take dokar ka na yi ba, ba kuma raina nata suturun na yi ba baba, kawai kyautatawa ce da aka min nima na yi mata ita da mahaifiyata da kanaina"
Malan ba murmushi ya ce" Masha Allah Masha Allah, sulaimana maza je karbo, maza kama masa, je kamawa kanin naka, Allah ya kara budi, Allah ya sa matarka ce yaro"
A dole sulaimana ya bi bayan Anas, suna tafiya Baban yara ya ce" Malan ya haka? Kar ka amshi abin hannunsa, idan fa ba matarshi bace? Kuma Ni tsoron ya'yan nan na zamani nake , ka san fa kadan suka yiwa yaro abin alkhairi zasu biyo kadu......, kar saboda hidimar da yake yi ya nemi wani abin wajen yarinyar nan, ko kuma idan ita din ba rabonsa bace yace zai sa mu yi ramuwa......"
Malan ya kama haba ya ce" Dan shine Mi'ara karshen lisafi?, Allah na tuba dan shi ne matsiyaci? To ai bamu roke shi abin hannunsa ba, shi yayi niya ya kawo, zamu karba kuwa ko shiga goma zai yi da leda, kar dai a saman abinda ka dora min yarinya Ahmadu? To kai tsakani da Allah ai sai an koyawa yara sanin zafin yan matan nasu, idan basu iya shigowa da leda ba ai akoy damuwa, gwara ya iya yi mata dan abin alkairi wala Allah ya ci gaba idan ta fara hayayafa .........., ai in me ya bata a karba a sanya albarka shi da kansa ai ya dan ba aure na daura masa da ita ba kenan bashi da wani karfi a kan tunanin an bashi, ko sadaki ka bada ai ba zaka sakankance ba bale baka bada sadaki ba......., idan kuwa ya zama matsiyaci yace a biya shi sai mu hau Shari'a da shi, in abin ya zama ya kayar da mu sai in sigar da shanu a biya , Ama kam wannan sako an fara amsa kenan , ita din ma zan fada mata, kar ta roka Ama idan aka bata ta amsa ta yi godiya, sannan duk rintsi kar ta bari a lalatata du shegen da ya yiwa yaran nan maganar banza sai na kwashe kayan iskancin........"