← Book details Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 100 OF 141

Sashe 100

Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Komawar FARHANA da gudu ta zubo ruwa a kofi ta juya yayi daidai da shigowar Anna, wace isowarsu kenan tare da direba.........

Cikin yanayin tashin hankali da ganin yadda aka talabo Aban yara ana ƙoƙarin taimaka masa, Ama jikinsa sai bari yake ta yi waje da sauri tana sanar ma su Aliyu abinda yake faruwa hakan ya sa Aliyu fita da sauri ya yi soron gidan, yana zuwa kawai ya nemi da a bashi waje domin Nur a rukunkume take da shi tana kuka hadi da kokarin girgiza shi, sai dai fir ta ki matsawar har sai da Anna ta kamata ta dagota tana dybanta a tausashe ta ce " Nur kin ga, ki yi hakuri kin ji???, ina Auntyn naku take?????"

Sai a lokacin AUNTY ta daga kaffafuwanta da suke rawa ta nufo cikin soron , a lokacin ne kuma Anna ta musu nunin su je su bi bayansu......., sai dai tun kafin su isa din sun ja motar sun nufi asibiti da shi, hakan ya sa Nur sake fasa wani kukan gaba daya kamar zata zare

A birkice Anna ke fadin" FARHANA yi kiran Numbar Aliyu, mu ji asibitin da suke, sannan ga wayana yi min kiran Anas ya zo mu wuce tunda shi ma nan wajen gidansu yake ko?"

Da sauri FARHANA ta shiga yin abinda Anna ta ce, ko da ta yi kiran Anas ma bata tsaya ta ji komai na kawai tace da shi ya zo nan gidan su nur yanzu yanzu zai kai su gari in ji Anna, ta kashe tana duban A'isha a tausashe ta ce" A'isha, ke ma kukan kike yi? Ku yi hakuri kar ku rikita AUNTY kun ji? Dauko muku hijaban ku A'isha kafin Anas din ya karaso"

Sai a lokacin A'isha ta juya ta shige ciki dan ta dauko musu hijabai sannan ta kashe wutar ta rufe komai ta kuma rufo dakin auntynsu, dama dakin mama a rufe yake AUNTY ta ki yarda ta koma du yadda abansu yayi cewar a mayar da kayan maman dakin AUNTYn ita ta koma cen tace a'a ita ba inda zata koma a barawa mama ɗakinta zata dawo ne............

Anna ce ta sakawa NUR nata hijabin ita ma, sannan ta dubi AUNTY da jikinta ne kawai ke rawa, Ama ita kukan ma ya kasa zuwar mata, sai cen ta ɗora hannayanta saman kanta, sai kuma ta sauke ta shiga dawurwuri irin dai idan mutun na cikin halin kaka naka yin nan ................

Ajiyar zuciya Anna ta sauke ta duba time, magariba ta shigo tuni , sai dai kafin su yi sallar Anas ya zo, hakan ya sa suka shige motar kawai FARHANA na karanta masa sunan clinik din da Aliyu ya rubuto mata , wanda hankalin ANAS ke tashe, gaba daya ya kasa samun nutsuwa, tukin kawai yake yi Ama hankalinsa du a jikinsa ba, tsoro yake yi kar aje ko Aba ne ba lafiya? Idan aba ne kar aje abinda ya faru da shi ne ya sa haka?????, sun isa gidan Anna tun kafin mamansa ta fita daga mota tana ta kara nuna masa ya kwantar da hankalinsa ita bata yi haka dan wani abu ba sai dan su yiwa yarsu fada dan kar ta kuma shiga hurumin aikinsa domin ta kula in bata raba ba, tabas sai nur ta ja wata rana ya rasa aikinsa baki daya, kar fa ya wani damu, ko zagin Aban yara ta yi ba abinda zai yi saboda ba zai taba yarda ya rasa siriki mai kudi ba, domin kaf anguwar nan ai yana farko farkon masu abin kansu....., in dai NUR ce ya kwantar da hankalinsa har sai mahaifinta ya roki su fito a hade ita da A'isha, Ama kam tana kan bakanta, sai ya auri A'isha sannan ya auri wata NUR!

Suna zuwa asibitin alwallar suka fara yi saboda maza tuni suna masallacin asibitin dake jikin asibitin

Sallah suka yi a saman manyan tabarmun da aka shinfida tsaftatu na yan rakiyar majinyata mata dan yin sallah, ya zamo tun kafin su gama sallar IMAD ya wuce cikin asibitin inda Aba yake, ya shige dakin da likita ya gama duba shi har ya jona masa karin ruwa...............

Zaunawa yayi saman kujera saboda idannuwan Aban yara a bude, Duda waje daya ya kurawa ido wanda ke nunin sam bai ma tare da mutanen dake dakin, sai ya zauna hadi da zuba masa ido a tausashe ya furta" Aba.......????"

Da sauri aba ya kifta ido, ya maido dubansa kansa, lokacin da likita ya shigo tare da Anna da Auntyn yara suka karaso yana murmushi ya ce" Bismillah Hajiya, jininsa ne ya hau sosai, Gayanan mun jona masa karin ruwa na maganin da zai taimaka masa wajen samun hutu, idan ya huta sosai sai a ɗora shi kan magani......."

Hankali tashe Auntyn yara ta dubi likitan, sam bata kula da budewar da Anna ta yi Nur ta shigo ba, a tsorace ta ce" Hawan jini? Likita Malan bashi da hawan jini..... Innalilahi wa Inna ilaihi raj'une, likita Malan ko ciwon siga bashi da shi, ......Malan abinda ya faru da mama ne ko? Na yi na yi mu zauna da kai mu yi magana Malan ka kiya Gayanan zai hadasa maka ciwo irin na hawan jini.....???"

IMAD ya dago ya sauke sunansa a kan Auntyn yara, haka kuma ya mayar da duban nasa a kan Nur, wace gabanta ke kallon Anna, fuskarta a kirjin Anna, ta shige jikin Anna da rungumar da ta saka shi yi mata kallon mamaki, ya sake duban Anna din itama da kanta da wani mamakin abinda zai iya cewa kwarai ya bashi mamakin, domin tana dan dadaba bayan NUR kamar tana rarashin jariri hakan ya sa ya yatsina girarakinsa ya dauke dubansa saboda likita ya maida hankali ne yana yiwa AUNTY kwatancen cewar ba lalle dan wata damuwa bane hakan ke iya faruwa, bale idan har a lokacin da aka yi damuwar ba'a ga wani dan alamu ba, saboda shi ciwon nan yana tafe da shekaru ma, a gaskiya a shekarun Aban yara idan aka ce bashi da shi lalle hankali zai iya tashi , Ama kar ta daga hankalinta tunda har bai samu kafa daya hannu daya ba da sauki, idan aka samu ta sauka kadan za'a yi du abinda ya dace, dukan gwaje gwajen da ya dace za'a yi kuma in sha Allah zai samu sauki sosai.........................

AUNTYn yara ta gyada kai tana sauke ajiyar zuciya, Ama zuciyarta ta gama yi mata rauni sosai, hankalinta du ba a jikinta ba...........

Likitan ya sake fuskantar IMAD ya kara yi masa bayanin da ya sa ya sake duban Aban yara a tausashe ya ce" Docter, zaku rike shi kenan?"

Docter ya ce" Eh sir, zamu rike shi dole ta yiwu zai yi kwanaki a nan, ya danganta da yanayin samun saukinsa, yanzu a bar shi ya huta saboda maganin barcin da muka saka masa ........"

Kai IMAD ya gyada , ya kai dubansa a karo na ba adadi inda su Anna suke, ya mike da nufin juyawa Aban yara ya budi baki, muryarsa cen ciki sosai ya ce" Auta.......zo nan"

Inda ya kalla yayi maganar ya juya , ai kuwa du irin yadda muryarsa ke kurya haka ta juyo ta taho da dan sauri ta duka kusan gadon tana riko hannayen sa

Kallonta yake yi, kafin a tausashe ya ce" Ki daina kukan mana, ina Y'ar uwarki ne?"

Fashewa ta yi da wani kukan tana dora fuskarta a tafin hannayensa a raunane sosai ta ce" Aba, Aba dama baka da lafiya??"

Ajiyar zuciya ya sauke a gajiye ya ce" A'a, ciwo ne Daga Allah....., kin ga kukan ne bana so kin ji?, ki yi hakuri kin ji?......, "

Kai ta ringa gyadawa tana dubansa ta ce" Abana Allah ya baka lafiya"

Kai ya gyada shi ma, kafin ya dubi AUNTYN yara dake kusa ita ma a hankali sosai ya ce" Ke ma kukan kika yi??"

AUNTY ta sada kai, bata ce komai ba, Aban yara yayi murmushi ya ce" Gobe da safe, in sha Allah, ku je rumfa ku ciro kayan miyar nan, sai ki yi anfani da su, kar su lalace kin ji? Kuma ki ciri kudin nan ki maku dukan amfanin da ya dace, idan Allah ya sa na fito sai in zuba wasu kayan kin ji???"

A tsorace ta Dube shi, haka ma Nur wace ta daga a tsorace tana dubansa......

Anna ta ce" In sha Allah ma zaka mike Malan, ka yi hakuri ciwo ne kawai, zaka mike in sha Allah, kuma kana nan idan ba damuwa mu wuce gida da su, tunda ka ga asibitin nan sai dai a zo a ga jikinka a koma, masu jinya ne da su likitoci dake kula da mararsa lafiya, bale Auntyn yara ta zauna, kuma ka ga bata saba zama gidan ita kadai ba, idan har ba damuwa kawai mu je gidan da su, ka ga da motsin mutane ma ba zasu saka damuwa a ransu ba ko?"

Aban yara yayi dan tsai yana tunanin maganar, Duda barci ke fuzgarsa ama haka yake fuzgewa shi ma......

A dan tausashe ya ce" Hajiya ba takura?"

IMAD dake tsaye, hannayensa harde a kirjinsa, ya dubi bawan Allahn nan, kwarai ya gama karantar cewa mutun ne mai matukar kiyaye lamarin duniya da abinda ke cikinta, yana da taka tsantsan sosai a lamarin duniya........................

Bai ce komai ba, sai Anna da ta ce" Lah, wace takurar? Haba dai, ba wani abu , ka kwantar da hankalinka"

Aban yara ya gyada kai a hankali ya ce" Allah ya saka muku da alkhairi, Elhaji Allah ya saka da alkhairi, ban san da wace kalma zan gode ba......."

Sai kuma yayi dan shiru, ya dubi AUNTYN yara ya ce" Rahama......, dan Allah ko da wasa.....kar ki yarda ki bari yaron nan ya kuma rabar inda Nur take....., ko mutuwa na yi a yau ki kular min da wannan, sam ba mijin aurenta bane, na soke komai dake tsakanin su kin ji?"

Du a tsorace suke kalonsa, Imad da ya fuskanci wannan ne a tausashe ya ce" Bismillah, ku mu je .............ku bar shi ya huta "

Waje suka yi, banda Auntyn yara da ta duka a tsorace ta ce" Malan jikin naka ne?"
Chapter 100 · 0% Book details