Sashe 47
Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Murtalab ya sasauto yana dubansa a raunane ya ce" na sani, harda abinda baka san na sani Bama duka na sani, kuma dare guda ya isa in yanke in zan dauka a haka ko zan bari....., ban ce ina so saboda kai ba, ban ce ina so dan in yi taimakon ta ba...., ban kuma ce ina so dan in kaita in wulakantata ba...., kai ka san waye abiey, ka san me yake iya kyalewa da wanda baya kyalewa, idan y'ar wani ma na dauko abiey na iya tsaya mata bale kanwarka....., ka san waye Ni, ka san inda nake iya buya koda ina tsoron a gani....., ba abinda ya shafe Ni da abinda ake tunani a kanta, koda haka ne na ji na gani..........matsala ta daya ce yanzu in samu Tata amincewar, ........dan ina tsoron saurayin nan nata ya fi Ni power a wajen ta...., Ama ka ga? Abiey yace to meye dan zan zauna a wajenka sai na fada masa???, zan zauna har burina ya cika, idan ka ga na juya dan in je a zo a amsar min aurenta in juya da ita ne...., plz idan a matsayin ka na ƴaƴanta ba zaka taya ni wannan rigimar ba, ka bani dama in yi da amincewar ka........., plz broth?????"
A gaskiya mamakin Mutalab ya fi komai yiwa IMAD yawa.........
Yakan yi mamakin idan ya ga Abdul bassit ya dage yana wasu abubuwan a kan Matarsa......
Rashin kunya fa take masa sosai, Ama idan zai je gidan sai ka ga tsaraba kala kala , kuma su shaida ne ta sha yi masa rashin kunya ya fara rarashinta ya bata hakuri....., su sun nemi waje sun ajiye shi kawai, saboda Abdul Fatah shi dama gaskiya neman kudinsa ya fi masa komai mahimmanci, kai shi fa in ba dan nutsuwar jikinsa na tare da matarsa ba sai ya manta da ita ma, bai cika saka damuwa a ransa ba ta wannan fanin, shi kuwa IMAD har ga Allah a wai yake kallon lamarin....., to shi ya sha su yi fada da MAZNA irin ya so jin ya kasa samun NUTSUWA idan basu shirya ba, sai kawai ya ga sai me.......idan ta ga dama ta sauko an shirya din, Ama Abdul bassit? Daban ne, hakama alamun da suke gani na Mutalab zai biyo sawun Abdul bassit ne.....
"Hum, Allah ya tabbatar mana da alkhairin dake tare da ku....." IMAD ya fada ya mike yana nufar cikin dakin inda su Abdul bassit suke
Murtalab ya dira yana ji a ransa kwarai zai zauna kuma zai yi abinda ya sa ya zauna din, ita da shi za'a ga mai taurin kai, ya yarda da kansa kuma zai nuna mata a shirye yake tsaf ko me saurayin nata yake da shi shima ya taka!
Bayan ya bude kofar ya ce" Ku tashi mu je cikin gari"
Abdul Fatah ya dauke kai ya ce" ba inda zan je!"
IMAD ya shige yana nade hannun riga ya ce" Ohk, bari mu zauna , Ama zamu cire raini Ni da kai!"
Da sauri Abdul Fatah ya mike yana dira gefe ya ce" Broth mu je, mu je kar ka min danyen aiki dan kai ba gajiya kake yi ba, ba kuma zafi kake ji ba!"
Abdul bassit dariya yake yi yana dubansu, a ceb cikin zuciyarsa kuwa yana ji a ransa zai yi mugun missing din IMAD ....., duda ga waya ga komai, Ama ba kamar idan suna tare a cen ba......, sai dai kuma ya dan hakan shi ya fi alkhairi, IMAD shi ne baba a gidan su, kwarai suna da bukatarsa a cikin gidan nan.
A ranar sun fita sun yi yawo sosai a cikin baban birnin Niamey........, sun je manya manyan kamfanonin da ya gina sun bi waje waje, ya zamo sun dauki mota daya ne sun tuka kansu, har sai da Yama ta yi sosai sannan suka koma gida
Da dare ya yi aka kai su Abdul Fatah aéroport suka bi jirgi suka juya, ya rage Mutalab da IMAD a kasar Nijar.
Washe gari ma da su IMTEE suka je makaranta sai da Imtee ta je office din Anna, yau ma a rufe, haka ta juya jiki a mace zata nufi masallacin su Malama ta yi kiranta ta sa ta zauna ta fada mata abinda bata gane ba ta sake biya mata sosai sannan ta salameta ba tare da tace da ita Anna ce tace ta yi mata ba........
Haka suka koma gida zuciyarta cike da cewar Anna fiye da tunanin bawa, kuma a lokacin ne ta tuna bata tambayi mama wayar nan ba dan haka bayan sallar la'asar ta je ta samu Mama a daki ta zauna ta ce" Mama, Ni ina na ajiye wayar nan dan Allah? Na duba inda na ajiyeta ban ganta ba"
Maman yara ta dago da sauri daga irgen kudin dake hannunta ta dubi Imtee, gabanta na dan bugawa saboda wayar ita ta dauketa kwana uku kenan ta fansar da ita
Ture tunanin ta yi zuciyarta na samun NUTSUWA da ta tuna ga damar da zata sa in ma saurayin ya zo ya ji wannan ba matar aure nace tana dubanta ta ce" IMTEE, Ama kin bani ajiyar wayar nan ne??"
IMTEE ta girgiza kai ta ce" A'a mama Ni kika ce in ajiye kuma a cen na ajiye, shine da na duba jiya ban gani ba nace to ko kin cenza mata waje??"
Maman yara ta mike da sauri ta yi wajen jakar
Gaba daya ta zazage jakar ta zubar da komai dake ciki kafin ta dafe kai tana kwasar salalami ta ce" Na shiga uku, wayar nan ma an dauketa? Na zata iya sarkar nan da nace ke na ajiyewa Mai tama biyar wace da aka saida gonar babana na yi, nace idan na tashi maki aure zan baki ki je da su kadara ne, ashe harda wayar nan aka hada aka dauke? Na yi shiru na kasa yin magana saboda a gidan nan waye yake shigowa dakina? Daga ke, sai A'isha, sai auntynku, ina da tabbacin ku biyu dai ba zaku taba daukan abu ba in ba baku aka yi ba, saboda Ni na raine ku ban koya maku sata ba, ama kuwa abin nan ba zan iya kyalewa ba, idan Ni an dauki nawa na yi shiru naki fa? Irin yadda Malam ya sakoni a gaba kwanakin nan ai sai yace bakin ciki nake son maki bana son ajiye maki dukiyarki......, gaskiya ba zai yiwu ba, ba zai taba yiwuwa ba"
Jikin Nur ya kwashi rawa, saboda tsoro da tashin hankalin fadan da mama ta kwasa har ta fice daga dakin ta nufi filin gida
A gidan kuwa babansu baya ma nan, bale ya yiwa abin tsawa, kai bama wannan ba shin auntynsu mama ke son cewa ta dauki waya? Ama auntynsu ta yi me da wata waya ma? Auntynsu bata taɓa damuwa da wani abin da ba nata ba, sam ba ruwanta, to ko nata nawa aka lalata bata daga kai ta kala ba bale har ta dauki wata aba waya? Kuma da mama ke son yin fitina a kan maganar waya , wayar da ita tace a Boye abansu bai san da ita ba idan ta daga hankali har ya ji batun nan ai an shiga uku ko??, yanzu wai me yake shirin faruwa haka ne kuma wai???, kai innalilahi wa Inna ilaihi raj'une!
Maman yara kuwa fita ta yi ta tarar da auntyn yara na nunawa A'isha yadda zata yi kamun Koko ta ja ta tsaya ta nuno auntyn yara ta ce" Ke bani waya!"
Auntyn yara ta dubeta da mamaki ta ce" Maman yara waya kuma?"
Maman yara ta sake hade rai ta ce" Kin ga rahama bana son rainin hankali, na tabbata ke kika dauki wayar nan, dan haka tun kafin ranki ya kiya ki bani waya!"
Da sauri Imtee ta karaso tana dan kamo hannun mama ta ce" mama dan Allah ki bar maganar wayar nan, tunda ba'a san inda take ba ai shiKenan"
Maman yara ta dubeta ta ce" In bar maganar waya? Wayar da a zamanin nan jaka dari uku ba zata baki ita ba? To hauka ake ace in bar maganar waya???"
Auntyn yara ta mike tana duban maman yara cikin ido ta ce" Maman yara, kin bani waya ajiya ne ? Na manta wai maganar wace waya ake yi haka ne???"
Maman yara ta dubeta da mamakin kalaman da ta fada daga bakinta, gashi hankalinta kwonce ba wani dari dari ko tsoro
Dakewa ta yi ta ce" Har Ni zaki tambaya in na baki ajiyar waya? Ni banda wajen ajiyeta ne?, wayar Imtee da saurayinta ya bata ta ajiye a dakina kuma yanzu bata ganta ba, bayan Ni banda mai daukar min kaya!"
Auntyn yara ta dubi IMTEE da A'isha da suka tsaya kamar su fashe da kuka,
Ta dauke kai ta juya zata ci gaba da aikin ta ta ce" To sai dai ki nemi barawon a wani wajen, Ama Ni ban gani ba gaskiya!"
Ta baya maman yara ta janyo rigarta da karfi ta ce" Ke rahama ki dago mu yi magana dan Ni ba sa'arki bace da har zan zo ina maki magana ki juya min baya, waya kam tabbas sai kin fadi inda ta shiga, dan ke kike da mashayi kuma barawo a dakinki!"
Da karfi auntyn yara ta fincike rigarta ta juyo idannuwanta na sake soyewa ta kalli mama, a kausashen da yaran kansu basu taba gani ba, hakama ita din da kanta maman , auntyn yara ta nuno Imtee dake tsaye jikinta na rawa ta ce" Waya kika amsa a hannun saurayin da ko rana ba'a saka muku ba? To du inda aka saka waya a tabbatar da an nemo ta an mayar masa da abinsa, idan waya yake so ki rike ya bari idan kika shiga gidansa ya siya maki, a yanzu bashi da dukiyar da zai kawo ta cenza ra'ayin mahaifinki a kanki, ko kudinsa kika san kin taba ci ki fada a hada a mayar masa, kin ji abinda na fada maki?"