← Book details Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 81 OF 141

Sashe 81

Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sun same ta cikin kuzari, abin ba'a cewa komai, sosai ta kama jikin ta tamkar ba ita ba, a nan likitocin suka basu salama, ta sa direban da ya kawo su ya dauke su ita da Malan ya yi makaranta da su, suka sauka sannan ya wuce da su Malan din tana sanar masa in sha Allah zasu shigo da sun dawo

Sannan ta barawa ANAS msg cewar sun yi safiya, kar ya damu tuni suna makaranta kuma ba abinda zai musu yanzu, da an jima dai kawai idan ya fito ya zo makarantar kai tsaye

Sannan ta turawa IMAD msg cewar suna makaranta tuni, kuma an saki Mama
Kafin su isa office dinta ta cire nikaf din nata ta haye kujerarta tana kuna computanta tare da sake hade fuska, domin sam bata ba Farhana fuskar kawo mata wasu zancecekun ba, kuma ta yiwa kanta alkawarin a yau sai ta fada masa ya tarbi bakin FARHANA sanan a yau sai ta masa maganar gida, shi yasa tun yanzu dan ma ta nunawa matarsa ita ba wai tana jiran wani abu daga gare ta ko ta raba ta da mijinta take nan ba, hakin haihuwa ne da biyayar da yake mata ya sa ita ma ta shaku da shi......, ama daga yau zata gani in har zata kuma jiran shi, addu'a kuwa a ko'ina idan ta masa zata tarda shi ne, ita ba fushi take yi da su ba, sam bata fushi da kowa, rainin da ake mata ne ta yiwa kanta alkawarin samawa kanta mafita tun kafin ta yi tsufan da za'a kasa hakuri da ita kamar yadda ita take yi da Tata uwar mijin.

A lokacin da message din Anna ya shigo wayar Anas, wayar na dakinsa jikin caji, shi kuwa yana falo yana karyawa saboda sai zuwa tara da rabi haka zai fita dan ya zamo yana isawa goma ta kusa sai kawai ya dauko su, domin a yanzu fira suke yi da mahaifiyarsa na harkar kaurar su da take ta magana, bayan shi baya son maganar kaurar nan, gidan nan ba abinda ya yi, kawai su yi hakuri mana su yi zamansu a nan

Mamansa dake ziga shayi ta sake dubansa a tausashe ta ce" Anas, Ni wai yaushe zamu kaura wannan falelen gidan ne?, na ga gidan nan baya bukatar komai sai kujeru kawai, wa'inda su ma na san ba zasu gagareka a yanzu ba, ga gida mai dauke da dakuna barkatai Masha Allah duk wani tarkacenmu zai iya dauka, kai Allah ka karawa haihuwa albarka, ban taba tunanin ganina a gidan bulo irin wannan na, Ama sanadiyar haihuwa gashi zan shi in rayu a ciki, Allah jikan Malan yanzu da yana nan ana mora rayuwar nan da shi fa"

Sake duban ta ya yi, cabdijan, ai akoy aiki ja a gaban mamansa, wai dan Allah da gaske fa so take yi ta ce a gidan nan zata zauna? To ai gidan falonsa daya jal, falon nan kuwa ba zai rabu da sarakuwarta ba, kai shi sam ma ba zai iya hada matarsa da mamansa ba, to ai ba wata morewa, sabon auren da yake so idan yayi ya more rayuwa ya karya ba gaba ne take so ta shige gidan? Ai mama jira zata yi har a ga abinda hali ya bada, kawai zamanta zata yi da yara a gidan nan gaskiya, ba abinda yayi , bai jima da musu gyara ba, hatta kayanta ba abinda suka yi, mema zai sa ta nemi kari in ba mama ba???

Dan ya kaucewa firar ya ce" Wai mama, kin kuwa san yarinyar nan da ake ta nema, wace sanadiyar ta sir ya dawo anguwar nan da zama, wannan yayar ta Imtee ce? Ashe wai maman nan nata da ta zo nan ita ta dauke ta tun tana jaririya?"

Shayin ta dire tana kallonsa hadi da zaro ido dan mamaki ta ce" Ban gane ba"

Yayi dariya ya ce" Ke dai bari, Ni da kaina jiya da na je na ga su Nur a gidan nan sai da mamaki ya kama Ni, shi ne suke sanar min wai ashe A'isha ita ce yarinyar da ake nema...., hum Ni ai abin ya matukar Bani mamaki"

Da mamaki ta ce" Wai kama nufin yarinyar nan yar uwar Nur din nan ce yar wajen maman oganka ?, innalilahi to ya aka yi haka?"

Anas ya dage kafadu ya ce" Wa ma ya sani, wannan abin ai abin mamaki ne, maman nasu nan ita ce ta dauke A'isha tana jaririya "

Maman Fa'iza ta tafka salati tana dubansa ta ce" Ka san Allah, shi yasa sam matar nan ke bani tsoro, kana ganinta fa ka ga muguwa........, ikon Allah dama matar nan barauniyar yara ce? Haba gaske y'ar nan Tata bata kwonta min ba, an girma a hannun barauniyar ya'ya ai tabbas itama wata rana sai ta sata"

Ido ya zubawa maman nasa kafin ya ce" Mama ai ba ita ta haife ta ba, kuma kina gani kin san mahaifiyarta mutun ce mai natsuwa, kawai wannan fa matar babanta ce ba wani abu ba, kina ganin nur ai kin san yarinya ce mai nutsuwa"

Mahaifiyarsa ta Dube shi da kyau kafin ta gyara zama tana dubansa ta ce" Kai yanzu a arzikin da kake ciki ba zaka so ace ka auri y'ar maman mai gidan ka ba? Wato ka zama kanin mai gidanka? "

Da mamaki ya ce" Ban gane ba Mama "

Mamansa ta sake gyara zama ta ce" Kai fa ke fada min irin shakuwar matar nan da mai gidanka, Ni da kaina sheda ce dan na gani sau daya da na je gaishe shin nan......., kai ka san du Wanda ya fito auren yarinyar nan ta gidan su sai ya samu alkhairin da zai kafa masa tarihin arziki har jikokinsa...., ka duba ka ga kama direbansa ma ya baka gidan nan da mota ina da ka auri kanwarsa???, yarinyar nan ai kallon kanwarsa yake yi mata kai ka sani!"

Da mamaki ya ce" Wai kina nufin Ni in auri A'isha?"

Mamansa ta gyada kai tana dubansa ta ce" Kwarai, idan ka auri yarinyar nan ina mai tabbatar maka ka gama da jan su matsayin direba, zaka zama ɗan gida, sai dai a ringa shawara da kai, a gaban nan sai dai ka ba wani motar hawa, ba dai a baka ba"

Da tarin mamaki ya ce" yanzu mama dan kawai an ga y'ar wajen mama sai ki ce in na aureta na zama kanwar sir?"

Maman da fara'a a kan fuskarta ta ce" kai da kanka ka san matsayinka ya tashi daga direban gida ya kara matsayi mai daraja, bale idan muka kaura gidan nan da ita na ringa riritata Ni na san wata rana sai ka ga oganka yana kai muku ziyara dan ya ga lafiyarta in kuwa ya ga ana bata kulawa kai ka san ba kai ba, harta ni sai na samu alkhairin haka ko?????"

Da sauri Anas ya girgiza kai yana dubanta ya ce" Allah kiyaye mama, ina ina auren A'isha? To ai in na auri A'isha ina mai tabbatar maki sai na samo irin Imtee na kara aure"

Da zakuwa ta ce" To dama ai ban hana ka aurenta ba, Ama ka fara aure ita mai darajan!"

Yanzu kam sai da ya saki baki kafin ya ce" wai in auri A'isha kuma in auri NUR?"

Mamansa ta ce" kwarai kuwa"

Sai da Anas ya dafe kirji ya ce" Astagfrullah, to ai haramun ne ma wannan ko?"

Da mamaki mahaifiyarsa ta ce" Anas, wani irin haramun kuma? Shi uban na Nur shi yayi cikin A'ishan a wajen maman ogan naka ba??"

Da karfi ya ce" Astagfrullah mama, ina hadin baban su NUR da Wannan?"

Ta sakar masa harara ta ce" Da yake babanka ne har kake shedar shi, Ni ba wannan ba, ai idan y'ar wajen maman ogan ka ce ubanta daban mamanta daban ko? Meye na haramcin dan na ce Ni da kaina na yarda ka aure ta daga baya idan A'ishan ta yi haihuwa biyu uku haka???"

Kai ya girgiza da sauri ya ce" A'a gaskiya, Ni ai ba zan iya auren A'isha ba sam, kin ga yar uwar Nur ce, ko da wasa NUR ta ji maganar nan tana iya ki na, bayan wannan mama ki bar maganar gidan nan, idan aka yi aurena da NUR ciki zamu tare in sha Allah, kin ga falon gidan nan daya ne a hade, ai ba zata sake ba in tana ganin ki a falon "

Kallonsa take yi har ya mike ya shige dakin sa ya shiga cenza tufafinsa

Zuciyarta ke kuna, da irin kunar da bata taba ji a kansa ba, kwarai ranta yayi mugun bacin da bata yi da shi ba sai yau

Har ya gama ya fito tana zaune a inda ya barta, ya zo zai tafi ya ce " Mama zan tafi"

Kanta ta daga tana dubansa ta ce" Anas, bari ka ji, in dai ni na haife ka , na zan taba saka albarka a aurenka da yarinyar nan ba, auren auren sha'awa, kai da baka yiwa komai biyayya irin jikinka a rayuwa....., to wallahi bari ka ji idan ba A'isha ka fara aure ba sai na tsinewa aurenka da yarinyar nan, ba yawuna a ciki, ba albarka ta a ciki, tun baka aureta ba kana neman fara bijire min da nuna min ba zaka saka ni a gidan ka ba, ba damuwa ai, Ama ita ma ta yi kadan ya shiga gidan nan dan ubanta in dai ina raye, sai dai ka bijire min ka sakata bayan ka bijire min ka aure ta, yarinyar da ba sonka take yi ba kowa ya sani, aikin banza aikin wofi kawai!"

Daga haka ta mike ta nufi dakin ta zuciyarta cike da tunanin Bama zata iya barin wannan masifar ta sameta ba!

Ya jima a tsaye tamkar an yi masa dukan tsiya kafin ya daga kafa da kyar ya karasa cikin motarsa yana hangen kaninsa ya bude masa get din gidan ya ciri wayarsa ya zuba mata ido, nan ya samu msg din Anna wanda ya sa da sauri ya tashi motar ya dauki hanyar makarantar zuciyarsa a cinkushe sosai da sosai
Chapter 81 · 0% Book details