← Book details Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 141 OF 141

Sashe 141

Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Zai sake yin magana Mama ta fito tana murmushi hadi da duban inda suke

Ai rige rigen fitowa daga motar suka yi, da gudu Mazna ta shige, inda shi kuwa ya kasa tsayuwar waje daya a lokacin da mama ke sanar masa cewar ta sauka, ta samu yan biyunta maza, sai kawai yake neman suma har sai da Aliyu ya kama shi, suka jira har aka mayar da ita dakin hutu sannan suka nufi dakin mai dauke da dangi, uwa uba Mazna dake rungume da babyn guda a hannunta, dayan a cikin gadonsa ta kalli wannan ta kalli wancen, farin cikinta bayanane ne........

A hankali ya karasa bakin gadon ya duka yana saka hannunsa cikin nata, a tausashe ya ce" Nur"

Nur ta bude idannuwanta tana kallon fuskarsa, kwarai a gajiye take, sai dai tunanin ta bata masa rai ya fi daga mata hankali, a hankali ta ce" Andadi, in sha Allah babu abinda zai kuma haɗani da ANAS.....ka yi hakuri"

Cike da tausayinta ya ce" Plz ki manta, ki yi hakuri daga maki hankali da na yi, ..........dubi ya'yanmu, kin gansu kuwa????"

Sai yanzu ya mike yana duban Mazuna dake rungume da su yayi murmushi yace" Ta gansu kuwa?"

Anna dake dauke cen ajiye nan, ga waya a kunnenta sai masa waya take harda su auntyn yara ce ta ce" LAH inaga kunyarsu ake ji, .....a boye take leka su..........., dadin abin ga mamansu nan ta dauki abinta"

Farhana ta yi yar dariya ta ce" Su kandalar Anna sai abin kai ake yi, yaushe kika fara jin kunya????"

Hararan da IMAD ya sakar mata ya saka ta kame baki hadi da tsakurar A'isha da hannu wace dariya ta kamata, ta mike tana kamawa Mama Nur suka gyarata da kyau ɗan ta ji dadin jingunuwa saboda ta shayar da su bayan ta sha jus din Mango din da akace a bata ta sha..................

Farin ciki ya gama mamaye duk wani halin gidan nan da yan uwa da abokan arziki

A lokacin da ake cikin hidimar bikin yan biyu Al'hasan da al'husain a lokacin ne kuma maman yara ke cen cikin tsananin halin ciwo, domin ita bata mutu ba, ita bata rayu ba, ya zamo ba kowa a gefenta dan an kaita dakin duhu sakamakon abubuwan da take yi, ciwon ta yayi tsanani sai yar uwar kishiyar mamanta dake nan , itama saboda kudin da ake zuba mata ne dan ta zauna a wajenta ba wani dan zumunci ba, domin ba wani zumuncin da za'a biya a yi mata......, sai amiyarta da rayuwa ta yiwa tsanani domin rana tsaka mijinta da tsohuwar matarsa suka dawo gidan suka kwace gidansu da dukiyarta baki daya kan fansar zaman gidan da ta yi, suka koreta ya zamo abinda zata ci sai ta yi bararsa, domin ko maza tace zata bi duniyar ta gama sakota kasssss ba kasuwa, dole a bi titin a wulakantar da kai a ci abinci kar a mutu............

A hankali taron sunna ya watse, nan fa Mazna ta fara rashin lafiya da tarin gajiyar taron sunnan da shigar cikin da take da shi, a dole ta kwanta ciwo , danma ba'a riketa a asibiti ba, ama ko daya babu wani abu dake shiga ko ya fita daga jikin mijinta dan kuwa Bama zata iya da jarabar IMAD a irin wannan yanayin ba, shi yasa kullum tana bangarenta tana lalaba kanta , sai idan ta so gannin ƴaƴanta take leka su bangaren Anna har suka yi arba'in ya zamo sunna shirye shiryen komawa dakinsu a yau ranar juma'a bayan an yi waina an yi sadaka dare yayi ta kasa mikewa ta tafi dan kunyar su Anna bayan tunda safe yake aiko mata da sakon ta fa dawo arba'in din ta yi , sai ta yi biris take zaune a falon Anna kamar ba yau zata koma ɓangaren ta ba

Mama ce ta shigo da carbinta tana ja ta sameta a nan da mamaki ta ce" Dama zagayowa na yi in ga ko kin tafi, ashe kina nan? Tashi tashi ki tafi bangaren ki, ba an zuba nonon a pidodinsu ba? Tashi mu je in raka ki maza yar albarka "

Cike da kunya NUR ta mike tana gyara hijabinta, dama tuni ta ja nunon yaran, domin tun bayan biki haka ake yi, bata kwonciya gado daya da su, sunna wajen Anna ko wajen Mama, da pidodinsu cike da ruwan mama, sai da safe idan ta yi wanka ta karya ake bata su ta saka su a mama........, hakan ya sa ta samu jego mia kyau da lafiya da kwanciyar hankali cike da gata, dan kuwa ko a cikin wunin ana iya wuni bata wani jima sosai da su a hannayenta ba, masu daukan nasu da yawa, Abdul bassit ya mayar da zuwa Nijar kamar zuwa gari kusa da kusa, domin a kwana arba'in din nan yayi zuwa ya kai hudu, dan ya ga ya'yansa ya koma, cewa yake yi a yi a cire su daga mama ya dauke abinsa, Imad kuwa sai dai ya kale shi shekeke ya kawar da kai, bai dai tanka masa ba, ama kuma bai ce eh zai bada din ba

Sai da mama ta kaita har falonta Sannan ta barta ta yi tafiyarta

A hankali ta mike tana jin kanshin falon

Murmushi ta yi tana jin kewar ƴaƴanta na son damunta, hakan ya bata mamaki saboda ko a gidan ba da su take kwana ba, koda yaushe Anna ke dauke abinta, ko a kaiwa Inna ta yi ta laguda ko mama ta dauke abinta....., wai ama yanzu sai take jin kewarsu a ranta.........

A nutse ta karasa kofar dakinsa ta bude hadi da shi a hankali tana yin Salama kasa kasa

Dagowa yayi daga saman bed din nasa ya zauna yana duban ta hadi da bude mata hannayensa

A hankali ta karasa tana cire hijabinta ta Yar a nan ta haye tana shigewa jikinsa hadi da lumshe idannuwanta sakamakon kanshin jikinsa da irin yadda yake goga mata gemunsa a wuyanta ke daf da sakata rikicewa

Cen ciki ya ce" Haka kawa......, ba addini ba.....a rabani da Dadina......, yau sai kin fanshe kanki.........yau sai na cinye komai dake tare da ke.....yau sai na..............."

A rikice ya juye da ita, wanda hakan ya sa na juya a guje, domin lamarin na yau kamar farautar zaki IMAD zai yi a baban birnin HALLAH.....Gani sai su ya su.......domin kuwa lamarin baba ne.........

A nan muka dasa ayar littafin kisan Mumuke......, Allah ya bamu ladan dake ciki, ya yafe mana zunuban dake ciki

ALHAMDULILAH ALHAMDULILAH ALHAMDULILAH

*Ina mai gabatar muku da tallar sabon litafina mai taken *TIRƘA -TIRƘA*......., KU TUNTUBENI A NUMBARNA KAMAR HAKA DOMIN SAMUN NAKU A FARASHI MAI RAHUSA.........93811618, SAI KUN ZO*
Chapter 141 · 0% Book details