← Book details Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 141

Sashe 17

Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kwarai ta tsani baiwar Allahn nan, bata son abinda ya hadata da ita, domin gani take yi ta samu damar da bai dace ace talaka marar galihu irinta ta samu ba, wato irin yadda ta shaku da IMAD hankalinta ba zai dauka ba! Sanadiyar ta ne IMAD ya fara tunanin mayar da su anguwar nan, saboda a lokacin da ta samu wani ciki nakuda ta kama ta, mijinta wanda shi ne mai malamin baban su IMAD ya dauke ta ya kai ta wata yar karamar asibiti a nan anguwar wace itace asibitin anguwar ta haihu, a ranar aka nemi babyn aka rasa, sama ko kasa, sun ce mace ce, wannan dalili ya sa du idan ta fita sai ta nufi asibitin har abin ya so taba mata kwakwaluwa sai kawai shi IMAD din ya shiga lamarin tun bai gama karatunsa ba ya sa aka fara siyan asibitin da komai da komai har ya dawo kasar ana ta kokarin mayar da anguwar yadda zai iya bincikensa son ransa, har aka kwashi shekaru goma ya yanke shawarar attitude din kanwarsa da kuma wannan dalili zai sa ya mayar da kowa anguwar, farkon dalilin fara siyan filin nan da fara ginin, haka kuma daidai auren su ne....., ya zamo har yanzu ba'a ga yarinyar nata ba, dalilinta an dawo da su anguwar nan an zubar.........

Sai ta biyu kanwarsa, wato FARHANA

A da sunna mugun shiri da Farhana, bayan an aureta ma kafin su kaura anguwar nan ta talakawa sosai suke shiri da Farhana dan bata cika zama Bama ita bale har a samu sabawa da ita, sai dai daga bakin lokacin da ya yi ginin nan ya mayar da kowa cen ita ta ringa nan nan tana kaucewa zama idan baya gari , ita din ma Farhana din ba so take a san nan take rayuwa ba, ama tsabar raini da shiga abinda ba'a sakata ba sai Farhana ta fara tsanarta har ma suka fara fito na fito da ita, domin abu ƙalilan take jira ta yi mata karan tsaye a lamuranta ko na kannanta, wa'inda kannenta namijin ke son farhanar ama kiri kiri tace masa ai ba zai taba yiwuwa su hada shirgi daya ba dan kyar ta san kyar ne, domin shima mutun ne marar jin magana sosai, kuma hanya ta san hanya ne.

Sai tsananin tsoro da tunanin yaya mijinta zai rayu a gari irin na Niamey, garin da yan mata ke kwatar miji ido da ido......, a garin Niamey kina ji kina gani idan gabdi ta rike mijin ki sai dai ki hakura, ko ku rabu, ko kuwa ki jira idan ta gama cinye duk wani abu da ya tara sai ta Bara maki katon kawai.......

Kwarai mijinta yana da kamewa, yana da aji, bata tunanin ajiye wata yar balaja'u da zata janye shi da gaggawa.....sai dai tana tsananin tsoron MACE, domin a garin nan ta gama baza karya da kuri ta yadda da yawa na jiran damar da zasu hadu da mijinta dan su dandana ko su ga abinda ya da take wannan dan banzan rawar kan!

Abu na gaba shi ne batun aikin nan da ta je aka yi mata, ta shiga cikin wannan lamari ne dan ta san idan ya jima a Nijar a shekara yayi wata uku ko hudu, yawanci yakan zo ne ya yi sati Daya ya juya saboda komai nasa a Saudiya ne , ta san cewa watanni shidan da likita yace ta ringa komawa ana yi mata binciken lafiya zata ringa yi hankali lwonce ba tare da hankalin kowa ya kai kanta ba, saboda ko anna tana iya shafe wata biyu bata leka inda take ba, dan bata wani yarda ta sabawa anna zuwa gidanta ba bale har a mayar da abin dole!

Innalilahi, nan da karshen watan da har ya kai tara? , nan da karshen watan nan zai zo Nijar da nufin yin watanni tara ko fiye da haka har sai ya yi niya ya zo hadj ko umara ko kuwa ya zo su gana da abokansa.....?

Wace irin rayuwa ce zasu yi a yanzu kenan?

Yaya zata yi yana kusa da ita ta iya gudunsa har na wata shida??????.....

Tabas dole zata je Turkiyya a gobe gobe dan ta gana da likitanta, zata fada masa ne babu wata dama da zata iya hana ta saduwa da mijinta nan da sati uku, idan da wani abu da zai iya yi a kai tabbas ya zama wajibi ya yi ko menene, dan ba zata taba bari ya sake yin dogon lokaci bai samu abinda yake kira gishirin zaman aure ba..........

( Wannan kenan)

Da asubahi bayan ya dawo daga Masallaci ya zauna saman cafet, sai ta zo ta zauna a jikinsa ya zamo ya wara kafafuwansa tana tsakiya a zaune, bayanta a kirjinsa a lafe

A hankali ya shafa cikin ta yayi dan murmushi yana Ayana abubuwa da yawa a ransa, ciki kuwa harda bincike a kan maganar da ta fada, dan shi ba jahili bane a jiya ya saurareta ne yana mamakinta......kwarai zai waiwayeta a lokacin da bata shirya ba.....

Ba wai bai yarda da matarsa ba, ko daya.......ya yarda da ita sosai da sosai

Sai dai akoy abinda idan aka fada hankali bai cika gaggawar dauka ba................hmmmm

"Anna ta jima tana hakurin nisa na da ita....., na yi mamakin da na ce maki zan dawo daf da ke........., irin kusancin da du dare kina saman kirjina....irin wanda du safiya zan tsotsi leben ki in ji yaya kika tashi........Ama sai kika kasa mikewa kina dira dan murnar haka........., girl........ar u stilll lv ur hsband ????"

Da sauri ta zarro ido ta juyo tana kallon sa......., to ita in bata so mijinta ba ta yi me a duniyar nan?, kai.........

Da magana mai fitar da iska irin ta tarin mamakin kalamansa ta riko hannunsa tana duban fuskarsa ta ce" What? Anya akoy aikin da na fi jin dadin yi irin na soyayyar mijina kuwa......?????"

"You're lying....." ya fada cen kasan makoshi.......

A dan birkice ta rike hannayensa duka biyu ta ce" believe me, ina son ka fiye da rai na......., kawai banda lafiya ne jiya, Ama yanzu cikin ya fasa ciwo gaba daya......."

Jikinsa a mace , muryarsa cen ciki din nan ya ce" the blding stopped too?....."

MAZNA ta lumshe idannuwanta a hankali ta girgiza kai, cen cikin kunnansa ta furta" Ina iya aiki da ......da............"

"No............" Ya katse ta a hankali ya mayar da ita irin kwoncin da ta yi da farko a jikinsa, cen kasa ya ce" Ban san yaya wasu mazan ke samun nutsuwa da haka ba....., Ni kam a'a, its ok."

Ajiyar zuciya ta sauke bata ce komai ba

Sun jima a haka kafin ta ce" Yaushe zan koma?"

Bai bude idannuwansa ba ya ce" Yau , akoy jirgin sha daya shi zaki bi zuwa Nijar......"

Ba yadda ta iya haka ta gyada kanta, ta kwonta a jikin nasa kawai a ranta tana tunanin tun kafin ta shiga jirgi zata sanarwa kaninta ya je aéroport ya cirar mata tikitin tafiya Turkiya , tana sauka a nijar ta wuce Turkiya idan da halin haka, ko nawa za'a cire shi maza ya je ya cira.........., haka kuma ta yiwa kannanta msg cewar su hada du wani abin bukatarsu dake gidan su na plateau su kai gidan anna kafin ta dawo sai su koma gaba dayansu cen dan idan ya sauka ya same su a cen din.........

Karfe goma na safe sun gama shiryawa, suka fito , nan ya samu direba da kuma daya daga cikin masu masa aiki duka shiga daukan kayansu sunna kaiwa motar dake kasa

Kasancewar da mota biyu suka zo manya lafiyayu sai kawai ya amshi ky din guda a mutunce ya sanar musu su gama da Salamar hotel din sai su kai kayansa dake nan gidan sa.

Daga haka ya ja motar ya nufi aéroport da su a nutse cikin kwarewa

Sunna tafe tana yi masa yar fira a hankali, yana amsata a nutse har suka karaso filin jirgin

Da kula yana dubanta ya ce" Gine ginen kamfanin tatar mai ya yi nisa tuni....., na makarantun reshen nawa na nan ma, haka kuma sauran kamfani irin su harkar shopping da sauran su..........., ki shirya zama da mijinki a kusa ok.....?"

Murmushi ta yi ta ce" Na fi kowa murnar haka, Allah ya kawo min kai lafiya...."

Daga haka ta fita daga motar, ta nufi sama, yana kallonta sai da ta shige wajen da kawai zata karasa ne a yi mata duk procédure din da zai bata damar zuwa wajen da zata zauna daga jirgi ya zo sai shigewa , wanda aka tabbatar masa nan da minti ashirin zai sauka, nan da minti goma zasu rufe enregistrement (registration), sai tafiya Nijar.

Motarsa ya ja ya nufi gidansa dan sai ya huta sosai zuwa yamma sai ya je gidan su Abdul bassit, domin yana son ganawa da mahaifin su, wato sir .

MAZNA kuwa bata tsaya bata lokaci ba ta wuce sama ta zauna lokaci daya ta shiga kiran yan uwanta, kowane ta bashi aikin da zai mata, sannan ta kashe wayar ta ringa maimaitawa zuciyarta cewa komai zai je mata yadda take so, zata je ta samu abinda take so a kan kari, kuma zata magance damuwarta......,

Ana daf da fara kira wanda ke kula da harkar tafiye-tafiyen su ya zo mata da komai bayan ya gama yiwa kayanta registration ya bata

Cike da jin haushin sa ta amsa ta mike tana saka bakin glasss din ta ta nufi filin da jirgi yake da jakarta ta hannu karama mai dauke da yan abubuwan bukatar ta, kwarai yana bata haushi wannan Aliyun domin mutun ne na gaskiya wanda babu wata hanya da zaka iya bi ka sa ya ki bin umarnin uban gidansa, kuma in dai a nan ne ta ciri tikiti to tabas sai an bashi allrt, shi yasa ta so daga ta tashi ta yi shatar mota a kai ta RIYAD wato baban birnin Saudi Arabia ta je aéroport din cen direct ta samu jirgi a filin jirgin sarki Khaled (RUH), sai gashi sun bata mata komai........

(Wannan kenan....)💅💅💅💅💅💅💅💅💅💅
*KISAN MUMMUƘE*
💅💅💅💅💅💅💅💅💅💅

_PAID BOOK_

*BY*

_SAJIDA NIJAR_
Chapter 17 · 0% Book details