← Book details Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 122 OF 141

Sashe 122

Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A tausashe ya rage tsayinsa sosai ya ce" Sir, dan Allah ka yi hakuri kan abinda ya faru, wallahi ban kai su wajen nan da sanin abinda yake faruwa ba kenan, cewa suka yi sakon Anna zasu sanar, ka yi hakuri ka bar Ni a bakin aikina in sha Allah gabanan babu inda zai kai su sama da inda aka saka Ni"
Abdul bassit dake murmushi yana shafa gemu ne ya ce" Anas, kana nufin kana so a bari ka ci gaba da tuka Nur abinka ko?, kana da gaskiya Ni da kaina ina ga ya dace ace kai ne ke tuka su NUR, idan ma suka koma cen gidan sai ka ringa dauko ta, oh sorry dauko su kana kai su du inda ya dace, sir a duba masa plz a bashi aikinsa plz "

Kallonsa kawai IMAD da Aliyu suke yi, Abdul Fatah kam sai ya jinjina kai dan ya sani in dai Abdul bassit ne, babu abinda ya gagare shi............, Mutalab kuwa gaba yayi dan shi bai cika son ana hada shi gwagwarmaya da sirikinsa ba, sam baya son daga hankali a yanzu kam

IMAD ya dauke kai yana dantse lebe, kafin ya dubi Anas yana jin wani haushinsa ma ke neman taso masa....................

Kafadar Anas ya dan dafa a hade ya ce" Haka na yanke"

Sai kuma ya dubi Abdul bassit da hadewar fuskar zai
Zai yi magana suka ji ladan na magana ta lasifika a tausashe yana sanarwa kamar haka" ASALAMU ALAIKUM jama'a, in sha Allah da yama muna gayyatar daurin aure a gidan Elhaji IMAD, muna gayyatar daurin auren mutun uku da Yama in sha Allah a gidan Elhaji IMAD.............., bayan sallar la'asar muke gayyatar daurin auren, Allah ya bada ikon halarta, mun gode......." Sanarwa ce da ya bada da yare uku, wato Hausa, turanci da kuma Larabci

Da mamaki ya dubi su Abdul bassit harda Mutalab da ya dawo da gudu, a hankali ya ce" Wani Elhaji IMAD din?"

Abdul bassit ya dage kafadu, a hankali ya ce" Ina ga kai ne, ina ga fa kamar sun yi meeting ne kan a daurawa yan matan nan aure baki daya, ba ka ji nace maka aby na son magana da kai ba?, su anmy ma zasu taso ne yau da dare fa, ina ga da FARHANA, DA AISHA, DA NUR ake nufi"

A zabure du suka kalle shi

Kusan a tare suka hada baki, IMAD ya ce" HALLAH?"
Anas ya ce" NUR?"

sai kuma suka kalli juna, kafin IMAD ya ji kansa ya Sara masa........ya Salam....... Anas auren Nur ya sake nema? Yaushe aka yi? Yaushe ta amince? Why Nur zata hadasa masa ciwon da bai san maganinsa ba?

Juyawa yayi ya nufi gida har kamar baya ganin gabansa kai tsaye ya nufi falon Anna

Ko da ya shiga bai iya tsayawa ba, duda wace ya gani sun taho ita da kannenta , yannayinta du a firgice domin sanarwar ta ji , a rikice ta fito dan kuwa haka kawai zuciyarta ta bata sanarwar nan kamar ita za'a saka a halin ha'ula'in rayuwa......domin bata san wasu yan mata uku da za'a yiwa aure ko samari uku dama da yan matan nan ba, kuma bata san dayarsu da wani sama da mijinta ba, gashi suna cikin halin bacin rai ita fa mijinta, kar dai ya tayar mata da hankali ta hanyar auren yarinyar nan ????????

Bai iya tsayawa a falon ɗan sake gaisawa da su Anna ba, elevator ya shige idannuwansa har rufewa suke yi, hakan ya sa Anna mikewa da sauri tana kiransa, sai dai ya riga ya rufe, a dole suka tsaya har ya fita sai su shiga su Dukansu ukun, domin hankalinsu bai tsaya kan Mazna ba, yanayinsa ya daga musu hankali , du irin karar Anna jikinta sai ya ringa rawa

Yana fita daga elevator din, dakin Farhana ya karasa da karfi ya shiga bugun kofar, sannan ya dafe gefen kofar da hannunsa idannuwansa har kamar zasu rufe

Ya zamo a lokacin da suka turo Nur dan ta bude saboda kwarai sun gama gane bugun nan ba na lafiya bane, a lokacin su Anna suka bayyana, ya zamo Nur na bude kofar, idannuwanta suka shiga cikin nasa.......a mugun gajiya, muryarsa a shake sosai......., fuskarsa ta dau jajajir, a raunanen da muryarsa ta samu saboda tarin firgicin da ya samu zuciyarsa a ciki...........a rarrabe yana duban fuskarta ya ce "KISAN MUMMUKE PAGE 78

A hankali ya furta" dama du abinda kike fada karya kika min?, Nur........dama son sa kike yi? Aurenki za'a daura da shi???????"

Idannuwansa ya rintse saboda bugawar da kirjinsa ke yi ...........ya sake budewa ya ga ta matso tana kallon fuskarsa da son yin magana ama ta gaza

A hankali ya rike hannunta ........., a raunane aunun ya ce " Ama idan Ni baki damu da bata min rai ba, idan Ni Bakya tsorona.........ai aba ne yace ya raba ki da shi ko?........, kina tunanin ya fi wani son ki ne HALLAH ?"

A hankali ta ce" Yayan farh......."

"Ki ce min IMAD......., ki ce min kin tsane ni........ki ce min bana gabanki ke.......ama NUR ni ai......"

"Yayan FARHANA.........."

Ta sake fada kirjinta na neman fashewa, harshen ta na daukan rawa ........., zuciyarsa na neman balowa ta fito daga bakinta

Hannayen nata ya kara jimkewa a nasa , ya kuma sake janyota jikinsa ta yadda a yanzu babu wani space a tsakaninsu mai yawan da zata samu damar yin abinda bai bata dama ba, ko kuma bacewa ganinsa.............

Ido Anna da Mama suka zarro,

Dama ita Aunty tun Dazu take hajijiya, ta jima da bada baya tana neman Hanyar fadawa dan buya...........
Dama ita Aunty hanyar da zata samu ta mayar da ita kasa take yi Allah ne bai nuna mata ba.....................ga kuma matar sa da ta bayana daga wannan jirgin mai haudawa da saukewa .....

"Na fi shi son ki......, nur na fi shi son ki ..........., yaya zaki aure shi bayan Aba ne da kansa ya hana hakan? Yaya zaki aure shi bayan gani kuma na fi shi son ki......................?" Ya idashe maganar yana tsare lebenta da kallon da ya zarce misali......., idannuwansa suna kara kumburowa dan tarin tashin hankali..........kirjinsa na bugun da ya wuce misali..........., hannayensa kuwa na kara daukan rawar da suke yi tare da nata.... .

Da karfi Farhana ta furta" To ai shiKenan "

A lokacin ne kuwa su Anna suka juya a tsiyace , hakan ya sa suka karu ita da Mama, da sauri suka damki hannayen junna suka kuma zarowa juna ido kafin suke nufar elevator din

Sai dai a nan suka ga JAUHARA hannayanta saman kai, idannuwanta waje...........ta saki hannun yayarta da take ja dan kar su zo ..............

A hankali Anna ta ce" MAZNA........"

MAZNA da ta sankare a tsaye ce ta saki gigitacen ihun da ya dakatar da shi daga yinkurinsa............har ma ya lumshe ido jijiyar dake goshinsa na harbawa da dan karfin da yake daf da fitar da shi hayacinsa............

Zubewar da ta yi ba numfashi ya sa gaba daya iyayen nufarta suna girgizata hadi da kama sunanta

Juyowa yayi , hannunsa rike da na NUR, idannuwansa a kan su Anna da suka kama MAZNA suka kinkimeta suka nufi dakin Anna da ita saboda shi ya fi dacewa kuma shi ya fi kusa , ya zamo JAUHARA na biye da su a guje suka fada dakin sunna salalami

Idannuwansa ya lumshe, a hankali yana lashe lebensa da yake jin ya bushe masa kau sannan ya juyo da dubansa kanta a lokacin ne ya ga irin yadda fuskarta ta nuna firgici, da tarin tashin hankali

Ajiyar zuciya ya sauke, ya sake duban ta kasa kasa ya ce" I love You, kuma Ni zan amshi aurenki a wajen Aba.........sai dai idan ya hana min........, ki koma.....ki saka hijabi kar ki sa zuciyata ta kumbura saboda yawo a haka plz"

Daga haka ya saki hannunta yana kallon ta har ta iya jan kafa baya idannuwanta waje, kafin ya ga an dano kofar da karfi, alamu sun nuna da mutun a bayan kofar dake jira a basu waje dama, kuma ya tabbata ya'yan Anna ne, sai kawai ya dauke ajiyar zuciya ya ringa shafa gemun sa, kafin a nutse ya nufi dakin na Anna, domin daga inda yake yana jiyo ihun dake nuna alamun sun farfaɗo da ita, kuma ya tabbata da wahala su iya mata

Murmushi kawai yayi, ya bude dakin ya shige

Ikon Allah ya tsaya kallo, kokowa ce suke surmukawa da ita, suna kokarin mayar da ita saman gadon, sai dai kukan da take tana kara riko hannayen Anna a gigice tana maganganu kamar haka" Anna, Anna ke ce uwata, ke ce ubana Anna, fushin da yake ne ya da zai aureta Anna, Anna ki fada masa zan je a cire min komai da aka saka min Anna, ki fada masa zan tafi a cire min, Anna asiri ta masa, ta yi anfani da halin da yake ciki ta masa asiri Anna, Anna dan Allah kar ki bari a kashe Ni, idan mijina yayi aure mutuwa zan yi Anna, Anna zai aureta ne kawai dan ya rama abinda na masa, shi yasa ban fada masa ba tun farko dan ja san a cikin horon da zai min harda wannan, Anna dan Allah ki hana mijina yin aure, mutuwa zan yi, mutuwa zan yi Anna"

Gaba daya ta gigita Anna, sunnanta take kira tana fadin" Mazna, ki nutsu, ki nutsu Mazna, ki daina daukan abu da zafi irin haka dan Allah yarinyata, ki nutsu mu yi magana"

Mama rai bace ta ce" Kar ma ta nutsun mana, dan za'a maki abokiyar zaman ne zaki mutu? To ki mutu mana, na ga ai ba a kanki aka fara kara aure ba bale a kare a kanki ko? , to a kan me ma zai tsaya zama da ke daya jal kina neman kashe shi? Aure kamar ya yi ya gama kuma babu wanda zai hana!"

Rai bace Mazna ta ce" Allah sa Malan ya maki kishiya, Allah ubangiji ya da ya auro matar nan da ta sace maki y'a ta idasa ki ko na yi zaman aure lafiya da mijina "
Chapter 122 · 0% Book details