← Book details Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 141

Sashe 4

Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ido ya dan kikifta, sai kuma kasa kasa ya ce" Ba dai wancen yarinyar bane ta ja ake zaginki? Sai na ci ubanta a gidan nan yau, dama ai ke ne, kike fifitata a kaina, idan ta min rashin kunya ku hadu ku rufun min, zata dawo gidan nan ne munafuka, kuma kin ga ki daina shiga sabgar matar cen, gaba daya kama da munafukai take min a kullum ta Allah, baki ga Ni bana harkarta ba?, gaskiya ki daina shiga sabgarta dan sam kamar bata da gaskiya, yaushe zaki iya zagin mutun in ba munafurci ba? Kin tashi kin mika mata y'arki gayanan du ta koya mata munafurci, wallahi dai na fada muku idan na kuma ganin ƙatuwar Y'ar cen ba hijab a layi tabas sai na balata, bari in samo maki ruwan sanyi ki sha ajiye masa cefanansa , ai sai ya sake kin in gani, aikin banza kawai su sako ki a gaba suna zagi, wallahi ki fita harkarsa, ba ke ba shi a gidan nan kar a sa in yi danyen aiki dan kuwa ai kece babata, gaskiya biyayar da nake masa fa ba zata sa eh ina kallo ya wani ringa maki eyane ba, na fa girma sosai tam!"

Bai tsaya ya ji daga gare ta ba ya wuce yana muzurai

Gaba daya sai ta rasa murna zata yi, kuka zata yi, ko alhinin maganganun yaron nata?, tabas Sulaiman na cikin dabar layin nan wa'inda sam basa jin maganar kowa, shi yasa yake abubuwan da basu da kyau ko kadan.

A hankali ta talabe habarta tunani na zuwar mata kamar haka.......... A lokacin da ta samu cikin Sulaiman, irin tashin hankalin da ya faru a gidan ba na wasan yaro bane, har ta haife shi , domin bayan rasuwar mahaifin baban su Sulaiman din ne ya aurota a lokacin da ya samu gidan nan , matarsa da suke tare shekara da shekaru bata samu haihuwar ba tukunan, dan ba abinda bai faru ba har irin yadda yan uwanta ke fadin shine baya haihuwa ya salameta ta auri wani, da zuwan ita maman su Sulaiman din da samun cikin nan, har sai da aka ringa fadin ba nasa bane, sai dai Allah da hukuncinsa Sulaiman da ya zo duniya sai ya zo kamar an yi kaki an zubar na mahaifinsa, tak da tak kamaninsa ke ba yan Barka amsar yaro fa d'an ubansa ne.........., shekara biyu tsakani kuma ta samu wani cikin, a lokacin ita din ma Allah ya azurtata har ta samu aisharta domin tsakanin Sulaiman da A'isha wata tara ne, tsakaninsa da imtee kuwa shekara biyu ne.
Ko a lokacin haihuwar imtee ba karamin dauki ba dadi aka sha a gidan ba, saboda imtee ta ci mahaifiyar Babarta ita mama Ramatun ne, wannan lamari ya kawo rigima kala kala domin maman A'isha kanainayewa ta yi ta nuna a kan me, ta yaya za'a aikata haka? Daga baya sai kawai ta shigo da batun to ta yiwa yarinya nak name da imtee, ba yadda ita maman su Sulaiman din bata yi wajen nuna a'a ita ga sunan da take so a ringa kiran yarinya da shi wato Nur ko khairy , Ama aka ci karfinta aka nuna mata a so danka ma ai kai aka so, bale mahaifinta da aka gama siye masa zuciya da cewar ai ba kamar mai son d'anka, sai kawai yake horon mahaifiyar su nur din cewar ta iya kawar da kai ta iya yin kara a kan wanda ke son d'anta, a dole ta yarda tafiya ke mikewa cikin hargitse da ZARGE kala kala na yau da gobe har zuwa yanzu da ta gama yarda da abinda ke faruwa da duniyar ta kamar wace ake yiwa shigo shigo ba zurfi da lalata tarbiyyar yarinyarta ta hanyar nuna mata kauna ana so a Sakata a uku ta yadda ba zata taba iya kwatar kanta ba a rayuwar yau da gobe??????
To in ba wannan ba Fisabililahi yaya za'a yi ace wai soyayya ce ake gwadawa yarinya mace ba shara, ba wanki, ba girki ba wanke wanke ba koyon tsafta ba duk wani abin alkhairin da aka san cewar shine adon mace, uwa uba ba maida hankali a karatun bokon ko na addinin, kulun cikin sangarta da shirme? Wani irin soyayya ce haka an sakawa y'arta ta cikinta batun ta tsaneta? An saka mata batun bata son ta? An koyawa yarinya rashin kunya?????, imtee na iya sa in sa da du Wanda ta kama, tana iya dambe a duk inda ta kama, tana iya fita ba hijab ba mayafi ta ratsa layi, kai du inda aka ga imtee sai an nunata saboda ko tsarin halittarta ba irin ta A'isha bace, ba zaka taba yarda cewar A'isha ce ta girmeta ba, dan kuwa shiga ido ne da ita sosai da sosai, Ama a haka ake tafe....????, to wai, wa zata fadawa wannan maganar ya yarda da abinda ke ranta bayan hatta gidansu ta gama siye mutanen gidan nasu cewar ana son ta ana son y'arta Ama ita sai wani abu take yi marar dadi...... Shi yasa ta fi gane kwatanta fito na fito dan samawa kanta mafita.. a yanzu, ama tana tsoron hukuncin malam.....

Dawowar Sulaiman da magani ya saka ta mike dole ta amsa ta sha domin a chemis ya amso maganin, sannan ta samu a hankali ta ringa dan jansa da fira tana nuna masa ba laifin mahaifinsa bane, ba kuma na kanwarsa bane, hakama ba na matar babansa bane, an samu rashin fahimtar juna ne kawai, domin ba zata taba so maganar ta yi nisa ba, shi kuwa abinda ya fi tsana kenan , irin yadda shi ba makaho ba, shi ba kurma ba, Ama a kullum mahaifiyarsa ke shigewa bayan wa'inda suke muzguna mata...., karshe mikewa yayi ya fice kawai a gidan gaba daya, wanda a kan idannuwan maman yara ya fice din dan ta dage labulenta tana jira ta ga zata fito ta ɗora girkin ne ko yaya?

Tsaki ta ja, a ranta tana ayyana ' Dan iska kawai, kai ai bakin cikinka kadai ya isa ya kashe uwarka!'

A hankali suke tafe ita da A'isha bayan sun sauko daga islamiyyar

Har yanzu fuskarta a hade take, idannuwanta kuwa tun kumburin kukan da ta yi na Dazu basu saku ba, domin ba wahala take so ba ko kadan

Ita A'isha tana tunanin kar su je gidan su tarar da wata fitinar ne ya sakata kashe kafa, dan har ga Allah ita ba wani son an yi an yin nan take ba,
ita kuma Imtee ta gama fadawa cikin sake saken dake hargitse mata tunani lokuta da yawa, Bama kamar irin wa'azin da aka musu yau, domin bakon malami ne suka yi wanda ya musu wa'azi a kan girma da darajar iyaye a musulunci , a wajen Allah.

Sun shanyo kwana kenan suka dakata sakamakon kiranta da kawarsu ke yi tana dan sauri har ta cin musu tana murmushi ta ce " Sis A'isha, dan Allah ki saka baki mana Kawata ta min kunshin nan, Allah biki ne na manya, ina son halarta cikin shigar da ba za'a raina Ni ba tun daga tufafina har yanayin kwaliyata, na san da ba zata min mak'up ba, Ama ta min kunshin ya wadatar "

Imtee ta lumshe idannuwanta ta ɗan kirkiro murmushi a hankali ta ce" Ama kin san mamanmu ta hana Ni yin kunshi da kitso ko?, ki je wani waje a maki mana "

girgiza kai ta yi ta ce" Ama yanzu mama zata hana ki min Ni? Zan je in tambayeta da kaina"

Da sauri A'isha ta ce" A'a , kar ki damu zamu zo ta maki in sha Allah, kyaleta sai ta maki kunshin nan"

Farin ciki ya sa ta kama hannun A'isha da murna ta sanar musu tana jiran su sannan ta wuce layinsu cike da murna , suka ci gaba , domin basu da nisa sosai da juna, kuma tana ganin motar da yayanta ke ja ta mai gidansa ta cika da zumudi ta shige gidan dan ta san yau kam sai ta more da yan kudade, domin yayansu direba ne, yana jan daya daga cikin motocin gidan wani hamshaki dake cen bayan layi. Wanda tunda ya kauro anguwar ya gama siye gidajen anguwar domin ko gidan su Imtee sai da masu kula da harkar gidajensa suka zo neman babansu ya siyar da gidan ya nuna ko daya ai gidan nan sai dai idan ya mutu magada sa siyar, makotansa kuwa du sun siyar sai shi kadai

Har sun kusa shiga gida a hankali imtee ta ce" Yaya za'a ce wai idan ka batawa mahaifiyarka...wato wace ta haifeka ya zamo tana fushi da kai Allah zai kona ka? Yaya za'a yi ace darajar ta ta girmi ta mahaifi bayan ita tawa sam bata so na?, yanzu ana nufin fa darajar tawa ta girmi ta mamanmu? Ke shaida ce bata so na, bata kaunata, Shikenan sai a hada soyayyar da mamanmu ke min da Tata? Ni kam ko jikina duka kunnaye ne ai ba zan iya lamunta da wata fadar ba!"

A'isha ta dubeta, duba mai dauke da ma'anoni kala daban daban

A hankali sosai dan sun zo daf da shiga gidan nasu ne ta ce" Fadar Allah ce ai aka sanar mana ba fadar wani ba, na tabbata kuwa babu wanda zai tsara dan ya birge mu,....to ke a taki fahimtar ta yaya za'a hada wace ta dau nauyin cikinki na wata tara, wani tudu wani gangare wace jarabawa har kika zo duniya, ta shayar da ke ta kula da ke, da wanda bai yi hakan ba?, ban ce maki girman darajar babanmu bata da girma ba, ban kuma ce maki wai mamanmu bata son ki ba, abinda na sani shine........ko waye tabas zai biyo bayan mama karama a duniyarki ne!"

Daga haka ta shige gidan ta barta tsaye tana kalon bango.........

Shin me yake faruwa ne?

Me yasa abin nan ya mugun tsaye mata a zuciya ne?

Yaya za'a yi a rayuwa ta iya rabar mama karama ne bayan a bayane ta gane cewar idan ta samu dama tana iya kasheta?????

Ya Allah..........💅💅💅💅💅💅💅💅💅💅
*KISAN MUMMUƘE*
💅💅💅💅💅💅💅💅💅💅

_PAID BOOK_

*BY*

_SAJIDA NIJAR_
Chapter 4 · 0% Book details