Sashe 139
Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Nur ta dauke idannuwanta da nufin juyawa dan ta ci gaba da aikin ta, sai dai bai bata damar haka ba ya karaso ya riko hannunta ya ja ta ya fito daga bayin da ita hadi da janyota jikinsa ya rungumeta da karfi , zuciyarsa na bugawa ya ce" Please, kar ki daga min hankali plz"
Kuka kawai ta fashe da shi, kuka mai daga hankali, domin zuciyarta ta rike mata sosai, hankalinta na tashi sosai
A rikice ya riketa a jikin nasa ya dauketa ya karasa bakin bed din FARHANA ya zauna ya riketa a saman cinyarsa yana shafa bayanta idannuwansa du sun rikice, ya ce" Plz, kar ki daga min hankali, i'm sorry bab, menene, menene"
Fuskarta dake cikin kirjinsa take gogawa murya cen ciki ta ce" Ban san ko zan iya jurewa ba, shi yasa na tashi da tunanin ba zan taba auren mai mata ba......, ban san ko zan iya ba, ji nake yi kamar zan mutu, ba zan iya jurewa ba......"
Idannuwansa ya rintse, zuciyarsa na ci gaba da bugawa, a hankali ya dago fuskarta ya shiga kissing din bakinta......
Da ace ta san halin da ya kwana yau da sai ta tausaya masa
Eh kwarai, ya samu wani abin a wajen Mazna, sai dai har yanzu jikin Mazna bai gama dawowa yadda ya kamata ba, juriyar da ya santa da ita a da, a yanzu babu ita, du irin yadda ta dage, dan ta karbe shi sai da ya tausaya mata, domin ko alama ya kasa samun nutsuwar da take son ganin ta samar masa....., da kyar ya rarasheta ya nuna mata ba komai saboda hankalinta da ya tashi, ya kuma nuna mata shi yasa yake so ta kara hakuri kar tace zata yi gagawa, rashin lafiya fa ke samuwa lokaci daya, lafiya kuwa sai an jure dai a hankali..........da ta san irin yadda ya kwana da begenta da tarin jin rashinta a zuciyarsa da sai ta tausaya masa
A hankali ya sake riketa a jikinsa yana duban cikin idannuwanta bayan ya talabe kumatunta ya ce" Zaki iya.........., zaki iya nur, na san AKOY wahala, Ama zamu hadu mu jure hakan........., zan koya maki yadda zaki yi ki iya, saboda ba zan iya barinki ba....., Nur ba zan bari ki barni ba....., koda bamu zama abinda muka zama ba kin saka min kaunar ki, tun kafin in aureki kike saka Ni fita hayacina idan kin zo waje....., a yanzu ba zan iya barawa kowa ke ba....., plz ki daina kawo maganar na zaki iya zama da Ni ba, ki tausaya min, ki yi hakuri da Ni a haka....., bani da yadda zan yi, Mazna matata ce, da ace ba matata bace, da tuni na baki abinda kike so....plz kar ki daga min hankali , kar ki sa in gaza gane kaina..........."
A hankali ta sake shigewa jikinsa tana sauke wata irin ajiyar zuciya cen ciki tace" Ka ce kana so na, plz ka ce min kana so na"
Rungumeta yayi yana lumshe idannuwansa sosai ya ce" Ina son ki, ina son ki........."
Ajiyar zuciya ta ringa saukewa tana jin zuciyarta na daukan hakuri da nutsuwa, sai kuma kunya ta nemi lulubeta...........
Cen kasa ta furta" Ka yi hakuri dan Allah......., ka yi hakuri"
Sake riketa yayi a jikinsa, a kunnenta ya ce" Kar ki damu....., a duk lokacin da kika ji kina son fada min damuwarki ta haka.......ki fada, ki min kuka, ki min rigima......in sha Allah zan saurare ki, har sai na ga kin yi hakuri sannan in barki......"
Ya dan sasauta a hankali ya ce" Ni ma hakan na nuna min cewa......U love me"
Murmushi ta yi ta yi shiru a jikin nasa ba tare da ta tashi ba, shi din ma sai ya barta a haka ba tare da ya nemi wani abu a wajenta ba, domin kuwa lokacin fitar Mazna a girki bai yi ba, ya kara zaunawa ne ma saboda Mazna na barci, maganin ta mai saka barci ne mai nisa.
Kwonci tashi har aka gama gidan su Aban yara suka kaura , wanda ranar kauran cen yan matan gidan su Anna suka wuni tunda safe sai da dare kowa ya je ya dauki matarsa....., kuma sun yi wunin ne da Fa'iza wace ta ringa fadawa Nur halin da gidansu ke ciki a yanzu, cewar ƴaƴanta kanti ya buga a kofar gida, yake kawo kayan miya da kayan abinci, sai dai kasancewar bai iya neman kudi irin wannan ba, gaba daya komai baya shigowa sai dai asara, an kai yanzu mamansu ke tsaron kantin dan a samu na cefane, kuma ta yi ta yi su je yace shi yanzu tsoro yake yi su kara zuwa a kore su, saboda tunda ya tafi bai je aikin da aka bashi ba, yana tsoron Aliyu sosai....., karshe dai Nur din tace musu kar su damu, idan suka kara zuwa ta san zasu samu Imad din zata musu magana sai su hade su bashi hakuri kawai ya ci gaba da zuwa bakin aikinsa......., da wannan albishir din ta koma gida, wanda ya zama tana fadawa mamanta Shikenan mahaifiyar Tata ta dauri aniyar bin hanyar gidan su Aban yara , kusan kullum sai ta je ta gaishe su hadi da tsumayen ganin Nur, sai dai bata sani ba, Aban yara ne da kansa ya saka dokar kar ya ji kar ya gani suna biyo hanya kullum zuwa wajen su, kowace ta zauna a ɗalinta, bale NUR da yanzu du wata sai ta je awo to wannan awon ne kawai take zuwa, har aka gama nata ginin ta koma ɓangaren ta a yan watannin da basu gaza uku ba, rayuwa ta ɗora da sama da kasa wato kwonci tashi asarar mai rai.
A hankali cikin Nur ke kara girma, ya zama su A'isha kam sai yanzu suka samu shigarsa, domin ita nur har ya fita daga wata na takwas wanda ake duban haihuwarta rana kusa, ya zamo a yanzu babu wanda ke bata lafiya harta Anna sai ta yi shiga bangarenta uku a wuni tana dan lekawa ta bige da fadin wani abin ta je nema, Sai ya zamo ita din da kanta zuwa take yi ta wuni a cen da tulun cikinta, wanda hatta Mazna ke Binta da sannu idan ta ganta a falon Anna, ko idan ya fita da su wajen shakatawa ta kama nan nan da ita kenan.
A yau da ta tashi ta shiryawarta, da taimakonsa ta saka katon hijab dinta da nikaf da Safa saboda gidan su auntyn yara zai kaita yau, zasu hade da su Farhana a cen ne, hakan ya sa yana zaune yana dubanta bayan ta gaba ta tsaya tana murmushi ta ce" Ka tashi mana kar mu yi rana baka kai Ni ba ANDADI"
Murmushi yayi ya mike a nutse yana dubanta a tausashe ya ce" Ji nake kamar ki yi zamanki, bana son fitar ne"
Nur ta yi murmushi tana amsar jug dinta mai dauke da maganin zaki wanda mama ke dafa mata tana dubansa ta ce" Ka san fa likita tace in riinga tafiya mai nisa......, a cikin gidan nan bana yin tafiyar da zan ji na gaji sosai ......, Ama ka ga yau nace maka zamu dawo a kafa tare da su Farhana, ka ga kuwa ai zamu dan taba tafiya ko?"
Ajiyar zuciya ya sauke yana gyada mata kai, sannan ya rike mata jakarta suka fita yana rungume da gefen hannunta, ya zamo sunna fitowa ALIYU sada kansa har sai da ya bude mata gefen da zata shiga, ta shige sannan ya shiga shima ya kuma rufo, Aliyu ya tashi motar suka dauki hanya, domin tuni suka yi Salama da su Anna
Bayan ya ajiyeta sai da ya shiga ya gaisar da su auntyn yara sannan suka wuce, sai kara jaddada mata yake yi idan ta ji ta gaji ko a ina ne ta fada masa zai tarbota, bale yau yana gida, WEEKEND ne zai zo ya dauketa ko a ina ne kawai ta tsaya ta masa msg.....
Ita dai murmushi kawai ta yi har suka tafi, sannan ta kwashe kayan nauyin nan tana duban FARHANA dake fama da gurji ta zauna tana fadin" Wayo Allahna, in ba dan ina tausayin kar ya kasa zama ba, da babu mai sakani saka nikaf din nan, zafinsa nake ji sosai da sosai"
A'isha da ta fito da kunu daga kicin din auntynsu ta daga murya tana fadin " Aunty, yau ma da irin rigar ta fito wallahi, dan dai da yar abaya a sama, Ama dai rigar kam itace a kasan hijabin"
Auntynsu ta leko da yar muciyarta karama a hannu domin tuwo suke sha'awa shi take girkawa ta ce" Ai kin ga auta, kin ga auta, sai na mayar da idon babanku gefe na mayar da sunanta gefe na tatakata, idan haihuwa ta kama ki da wannan rigar yaya kike so mu yi"
Nur ta yi dariya saboda Farhana da ta bita da kallo tace tab da mun shiga uku
Nur ta ce" aunty sai a yi mai yiwuwa kawai, ai haihuwa ce"
A'isha ta rafka salati, auntynsu kam sai ta koma domin kuwa idan ta ja fa zata iya jiyo wani barambaramar daga bakin auta, sai fatan Allah ya shirya.
Nan suka yi rabin wuni, domin kuwa tuni rana ta yi suka karaso
Yama na yi suka mike bayan sun shirya suka dauki hanya
A'isha ce ta yi kiran Fa'iza, wace kwarai take basu tausayi irin yadda suke ta dakon neman hanyar da zasu hadu da IMAD abu ya gagara, ta sanar musu cewar Nur tace yau yana gida, kuma su ma yanzu zasu nufi gidan, su hadu a cen da maman nasu.
Hakan ya sa suka dauki hanya harma suka rigaye su isawa domin kuwa su a abin hawa suke, su nur ne ke kasa suna takawa a hankali
A nutse suka nufo katon get din gidan Anna, su ukun su,
Nur ce a tsakiya , daga cikin hijabinta tana taunar awarar da ta dauro a leda daga gidan Auntynsu, A'isha na rike da jug dinta, Farhana kuwa da jakarta, dan kuwa ta yi baban ciki ba laifi.