Sashe 102
Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Fitowar su Anna yayi daidai da lokacin da Nur ta dauki maganar, sai dai nata ya fi na sauran zafafa sannan ya fi na sauran amo, wanda ya kai hankalin su Anna bayan Auntyn yara da ta duba wajen da sauri a lokacin da Nur ta ce" Bayan wannan kalaman wadine mahaifiyarka ta fadawa mahaifina?, so nake yi in san komai ta yadda zan san irin ramuwar da zan yi a irin abinda aka min..........
, dan na rantse maka wannan karon ba zan kyale ba, babu wani mahalukin da ya isa ya nunawa iyayena yatsa ba tare da na karya yatsar na yi watsi da ita ba ko waye, sai ka fada min abinda kuka tarda mahaifina har wajen neman halal dinsa kuka fada masa, ka fada min irin wulakancin da kuka yi masa a wajen da yake da mutunci......, wato dan bashi da kudi ko? Dan Bashir da kudi ma ai bai je Bara gidanku ba........., Anas ka fada min!"
Ta fada da karfi tana kokarin cuje hijabin jikinta domin ji take yi yana shaketa yana hana ta motsawa yadda take so, kai ita fa idan ta samu a yau ko ita ko Anas kafin ta kai inda mahaifiyarsa take!
Kafa auntynsu ta daga da sauri ta nufi inda suke, tana zuwa ta zuba musu ido da tarin mamakin irin yadda horon da Nur ta samu ya sa bata tsoron yin abinda ta so a idon da ta so, Bama kamar idon manya da bakin sani, haka kuma fada kam sai dai in bata samu abokin yi ba.
A hankali ta ce" Madallah da ke, nace madallah da ke, Ni nunawa duniya baki da tarbiyya aunty, me zaki yi? Hijabin zaki cire a nan? To Bismillah dauke shi in gani......."
Ta fada tana yiwa Nur kallon da ya sa ta Dube ta kafin ta fara magana tana fashe mata da kuka ta ce" AUNTY, kin san dai a banza abanmu ba zai fadi maganar da ya fada ba ko?, ashe mutanen nan da kika hana Ni tarda su ranar nan ne ta sake kwasar tsohon jiki ta kuma tarar da abanmu runfa ta............."
Dauke fuskarta da AUNTY ta yi da gigitacen mari ya saka shi rintse ido da karfi kafin ya juyo a karo na ba adadi ya sauke dubansa a inda suke idannuwansa sun gama kadewa....., ya zuba duban nasa a inda Anna ta je da sauri tana riko Nur ido waje ta ce" Subahanalahi, Auntyn yara ya da duka kuma harda mari? Kun ga, ku wuce mu je , ku mu tafi....."
AUNTYn yara ta saki bakinta da ta cije ta ce" Ki yi hakuri Anna, ama rashin kunyar yarinyar nan ya gama kai Ni inda bana tunani......, wato ma ita da su din meye banbancin su? Ki duba ki ga yadda yake daga murya du ana kallonsu a zamanin da fada ya zama abin kallo da birgewa? Ya zama abin dauka da yadawa? A zamanin da abu kadan zaka tsinto a duniya kowa na bayar da bayanin da ya ga dama? A gaban mutane masu daraja ? Ki dubi hijabinta take son cirewa dan an yi mata horon yawo ba dan kwali ba wata damuwa bace a gaban tarin mutanen nan?, so take yi yi ta zagi mahaifiyarsa a gabansa ga dukan alamu saboda tsabar rashin tarbiyya da yarinyar nan ta samu a wajen uwakintarta?, Nur Hallah Ahmad so kike yi ki kwabe ku daku da namiji a gaban wadinan mutanen ko????????, kenan baki da bambanci da ke da su din da suka dauki wulakanta mu ba a bakin komai ba?, mace taki kalar tarbiyyar zaki nuna a nan ta hanyar zagin manya ko me........"
Aliyu kam kasa hakura yayi, ya dan dubi ogansa dake tsaye kikam idannuwansa a kan su, a tausashe da girmamawa sosai ya ce" Sir, ina iya shiga lamarin cen?......"
Ya ɗan sake dubawa a tausashe ya ce" Ina iya daukan matakin da ya dace ?......, ko in bari su gama su taho da kansu.....? "
Idannuwansa ya lumshe..........kansa na mugun Sara masa, gumi na neman tsatsafo masa.........., yana ji a ransa idan har zai iya budar baki Dan ya yiwa yarinyar cen fada tabas abinda bai taba yi bane zai fada mata wanda zai matukar dagawa kowa hankali......, ashe bayan rashin hankalin da take fama da shi wanda Anna ke nunawa ba haka ba harda rashin sanin ciwon kai?, soyayya kuma? Ita wannan yaushe ma aka haife ta da har zata wani damu da wata soyayya??????
A hankali ya shige motar nan, ya mayar da kansa jikin kujerar nan yana cire hular tasa ya sake ta a nan a hankali ya furta"a yi dltng din du Wanda ya dauke ta a waya................"
Yayi dan shiru yana jiyo kukanta bayan ya shiga motar ma, hakan ya sa ya dago daga jinginar da yayi a hankali ya mika hannu ya ce" Aliy.....bani ky din motar...... and.......ka sako su ciki..........idan ka gama kwa zo kai da Anas......tl hm zan gan shi ......but ba yau ba....."
Ya kara yin shiru saboda yadda Aliyu ke son yin magana ama yannayinsa na son bashi tsoro........, sai dai a hankali ya ce" Sir, plz ka bari in tuka ku.............., ka yi hakuri kadan bari in sako su mota sai in kai ku gidan"
Idannuwansa da yake lumshewa ya bude a hankali ya furta" ..........ALIY..........................ta yi shiru da kukan da take yi............., jiri yake saka Ni...........plz ta kyale ........................" Ya karshe yana dafe gaban goshinsa a hankali ya furta"
🥹🥹🥹🥹ita wannan yar gidan na Aban yara ya haka? Zata gigita mana bawan Allah bata san shi bai iya wannan hayaniyar ba?🥹🥹🥹😁Kisan mummuke page 63
A tausashe sosai ya furta" Bani ky din,......ka ce ma Anna su taho"
Daga haka yayi shiru yana sake rintse idannuwansa
Ba yadda Aliyu ya iya, a dole ya mikawa IMAD ky din sannan ya juya da gagawa ya je ya rage tsayi yana sanar da Anna abinda OGA ya fada
Nan take Anna ta hade hannun FARHANA da NUR ta janyo A'isha ta musu nuni su je mota, sannan ta kama hannun AUNTYn yara ita ma suka nufi motar da ita a tausashe tana fadin" Ki yi hakuri Auntyn yara, kin ji? Ki yi hakuri, ki daina yi mata maganganu irin wadinan, na san ba halinki bane, kuma ki gane ita ma a zamana da ita ka gane cewar du abinda zai taba mutuncinku bata son sa.......kar ki yi fushi da yarinyar ki mai tsananin kaunar ku, ki yi hakuri, kuma ko me kike gani a tare da ita ki yi ta adu'a in sha Allah zata dawo yadda kike so kin ji?"
Kai ta gyada a hankali ta furta" Na gode sosai Anna, Allah ya saka da alkhairi....."
Anna bata ce komai ba har suka karaso suka shige bayan motar, nan ta ga Farhana ke gaba zaune, sai kuma ta ga IMAD ya ja motar domin a kune take ac du a kunne
Juyowa Farhana tana zarro ido kafin ta mayar da dubanta gaba tana ta addu'a, domin ita dai da wayonta ba zata ce ga ranar da ta ga ƴaƴanta na tuki ba, Anna da kanta bata iya yin motsin kirki ba, ga Nur bata yi shiru da kukanta ba domin ji take yi inama mama na nan a yau? Da ta tabbata zata hana auntynsu hana ta yin fadan nan, kuma da sai ta je ta ramawa abinda aka yiwa Aban ta......, gaba daya ta tsani maza, ta tsani abinda ya shafe su, a gaskiya ita kam me zata ce da soyayya? Dama da ta fara ta kamar ta yi mata shigar karfi ne, kuma har zuwa yanzu bata idasa tantance me take nufi da ita ba har ta ajiyeta, ita kuwa me zata kuma yi da wata soyayyar? A haka a matsayin Anas yana son ta kenan, da ace Anas baya yi mata irin son da yake yi mata tabas da auren A'isha zai amsa kuma ya dawo ya danfareta, koda kuwa ba zata bashi aishan ba da sai yayi yadda yayi ya saka musu wata fitina a gidan su...........
Tukin yake yi a nutse,......sai dai du shashekar kukan nan nata ke sakawa yana ji kamar ana ƙoƙarin yi masa kidan bori marar kyau a kwakwaluwa.......
Du yadda ya so yin banza da lamarin sai da ya ji numfashinsa ake hari, hakan ya sa ya taka birki a dai-dai inda ba'a zata ba a kausashe ya juyo baya ya sauke dubansa a kanta ya ce" Do you borrow the wisdom to shut your mouth now?........."
Du a tare suka sake zuba masa ido, banda ita da ta ɗan kara sake wani shashekar da ya tafi tare da bugawar zuciyarsa........
Hannunsa ya miko, daidai inda yake kyautata zaton fuskarta ce a nan, ya dage abinda ya rufe mata fuskar a cen cikin makoshi ya furta "Will you finally be wise enough to keep your mouth shut now?”
Motar ce tasake daukan tsittttttttttttttttttt, Nur ya budewa fuska kuwa, ta cikin hijabin A'isha ta leko fuskarta dan ganin abinda ya sa aka tsaya da kuma jin Muryar bawan Allahn nan yana turanci tsantsa.
Idannuwanta ne suka shiga cikin nasa, a hankali ta bi karan hancinsa da hannunsa da kallo kafin ta yi saurin rintse ido saboda wani irin dokawa da nata kirjin yayi a karon farko......
A tausashe, cike da tarin mamakin ganin hannun Imad a kan wajen da fuskar Nur take......Anna ta ce" Sorry Andadi, bata cikin yanayin dadi ne Please kar ka Tsorata ta....."
"Ya Allah " ya furta cen cikin makogwaronsa yana janye hannun nasa ya bi hannun da kallo kamar wanda ke son karantar wani abin tashin hankali a jikin hannun .......
Huci ya fitar kafin ya bude wajen driving din ya zagaya da kansa wajen da Farhana ke zaune kai a kasa, ciki cike da abin fade sai dai ba halin fadar......., ya bude, hakan ya sa ta Dube shi da sauri, ganin ya mata alamun fitowa sai ta fito da sauri tana dubansa, dan har ga Allah a zuciyarta sai ta riga tsoron to ta yiwu yau kandalar Anna ta janyo musu tafiya a kafa ko? Ta yiwu zubar da su zai yi ya karasa da babarsa gida....................