Sashe 94
Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Gaba daya shawarar nan ta musu, hakan ya sa suka shiga shiryawa da gagawa kafin su fito su sauka su samu Anas da ya gyara mota ya loda su suka dauki hanyar saloon, wanda suna tafe Nur na dan jan shi da firar da har ga Allah bai taba ganin tana masa irin sauƙin kan nan ba, su kuwa sun yi gum kowacce na tunani har suka iso saloon din , ya zamo su biyu sun fita daga motar , Nur ta fito ta koma gaba tana murmushi ta Dube shi ta ce" Ya Anas, idan muka fito plz zaka kai mu gidan su iyayen saurayin FARHANA zamu sanar masa sakon Anna ka ji? Please yaya Anas ban taba tambayarka komai ba sai yau, dan Allah ka min"
Anas na kallonta yana murmushi , duda karkashin zuciyarsa cike da tunanin gidan su saurayin FARHANA kuma? Sai dai shagwabar da aka yi masa ta yau ta gama halaka masa tunani, hakan ya sa yana doka murmushi yana duban ta tamkar ya janyo ta ya rungume yake ji ya ce" Lafiya dai ko? Ina fatan sakon mai mahimmanci ne"
Nur ta kara shagwabe fuska ta ce" Sosai, sakon na Anna ne ai"
Ya gyada kai yana tafka murmushi ya lalubo aljihunsa ya ciro kudi ya ce" To shiKenan, zamu je ama minti biyar zan baku ku fada mu wuce kin ji?, ga wannan na gyaran kan ne amaryata"
Fyskarta ta rufe da hannayenta kafin ta fita tana dariya ta ce" A'a, Anna ta bamu, na gode yaya Anas"
Ta yi gaba da dan sauri irin ta ji kunyar nan tasa , wanda hakan ya sa ya sake lekawa yana washe baki hadi da sake sakin murmushi soyaya na yawo da shi a gajimare ya wani gyada kai yana jin a duniya a yanzu ai shi lafiya lau yake, komai zanzan , Nur ta fara kaunarsa, a yanzu kam ya yarda ta fara son sa......
Sunna shiga aka fara yi musu gyaran kan, Nur na sanar musu yadda suka yi kafin ta dubi A'isha ta ce" ikon Allah, ashe haka mazan suke? Kawai kato da kai daga yi maka alamun zan yi kuka sai ka amsa cewar zaka yi? Lalle maza zasu shiga uku a hanuna, to ai Ni gabanan harta abanmu alamun zan masa kukan nan zan yi in zan roki kudi, ta yiwu a dace"
A'isha ta gyada kai ta ce" Madallah, shagwaba kike yi, dama ai kina yiwa Aba, Ama gaskiya yaya Anas bashi da wayo"
FARHANA ta yi dariya ta ce" Dan Allah ku bari a min gyara mai kyau Ni da zan hadu da masoyi, in Anas ne? Ai haka yake a lamarin mata"
Kallonta nur ta yi da alamun son karin bayani, sai dai Farhana ta dauke kai, dama da biyu ta fada, kuma ta tabbata sakon ya je inda take so domin yannayin fuskar Nur ya nuna tana son karin bayani, ita kuma ba zata bata karin bayanin ba, karshe ma sai ta sa a fara wankewa NUR din kaffafuwa da gyaran hannu harda su saka gashin ido domin ita ne tace a yi mata dan Allah dan ta ga kalar da zata koma.
________________________________
IMAD bai koma bangarensa ba sai da aka yi sallar la'asar, ya salata Sannan ya nufi bangaren , har yanzu fuskarsa ba sakewa ko kadan, domin ko da ya je wajen Malam yayi ta yi masa tambayoyin lafiya dai ko? Ama ya nuna masa kalau, daga baya ma sai Malan din yayi tunanin dan Anna tace masa ya yi hakuri ya zauna da saurayin FARHANA ne ransa ke bace har yayi ta kara yi masa nasiha da sake nuna masa mahimmancin yiwa mahaifiyarsa biyayya da kuma nuna masa a yi ta addu'a alkhairin kenan, karshe ya baro bangaren nasa bai ma ga mama ba domin barci take yi sosai na magungunan da aka bata , ko Anna bata ganta ba haka su Farhana basu je Bama domin Anna ta sanar musu su bari ta farka.
A lokacin da ya shiga ya samu Jauhara da MAZNA ke falon baba suna kallon séries a Babar tv din dake falon.
Bayan Salama da yayi, bai tsaya ba ya wuce bangarensa, wanda hakan ya sa Jauhara duban MAZNA dake dan fama da kanta wuni guda tana ta fama da shan magani ta ce" kamar fuskar big broth a daure, lafiya kuwa?"
MAZNA da ita ma abinda ya sa ta yi dan tsai kenan ta dubeta ta ce" dazu fa ya fita ai, ya zo ya ga jikina lafiya kalau ya fita, bari in leko shi"
Mikewa ta yi ta nufi bangaren nasa ta bude har dakin da yake shiryawa ta ga bayi a rufe ruf hakan ya sa ta zauna tana jiran fitowarsa, ita kuwa JAUHARA ta yi zamanta bata wani tashi ba.
Ya jima kafin ya fito yana goge sauran ruwan da bai goge ba a jikinsa ya nufi inda kayansa suke a nutse ya ciro wani lalausan yadi mai kahirin shiga zuciya a kallo daya idan ka masa, mai ruwan baki sidik , da hular da zata tafi da shi ya ajiye ya fara bin jikinsa da turare sosai sannan ya shiga sakawa ba tare da ya kula inda take Bama bale har ya nuna ya san da wanzuwar ta a wajen
Hakan ya sa ta gane eh ransa a bace ne, dan haka ta shiga kokarin ganin ya kula ta, da tarin tambayoyin wani ya bata masa rai ne? Har ya gama shiryawa yayi mugun kyan da ya sa ta zuba masa ido a raunane ta ce" Akul, me yasa yanzu ka cika fushi da Ni ne? Me yasa yanzu kake fushi to? Me na yi?"
Zuba mata ido yayi, duba na yan lokaci kafin ya juya ya fita
Da sauri ta bi bayansa tana kiran sunansa har suka fito falo, hakan ya sa ya dakata ya juya yana kallon ta saboda ganin Jauhara na falon har ma ta juyo tana dubansu, bayan a cikin abubuwan da ya fada mata ko da wasa su kiyaye harda yin maganar da ta shafe su a gaban kowani bakon halittar da ba su ba, ko waye!
A hankali ta ce" Me na yi maka nake son sani dan Allah"
Agogon da ya daura a hannunsa ya gyara saboda bai dauru da kyau ba, a hankali ya furta" ba abinda kika min"
Daga haka ya juya ya fice a falon gaba daya
Jiki tamkar kwai ya fashewa kaza ta koma ta zauna tana hada tagumi hannu bibbiyu ta ce" Du idan ya yi irin wunin nan da mahaifiyarsa sai ya shigo min a birkice, Allah ya rabani zama da matar nan!"
Jauhara ta Dube ta, kafin ta dage kafadu, domin ta gaji da fadawa auntynta gaskiya tana takewa........, ta yi abinda ta ga dama, ita gabanan ba abinda zata ce mata Walahi!
A duniya tana mamakin soyayyar da auntynta ke yiwa mijinta, soyayyar da sam bata son mahaifiyarsa, in ba rashin tsoron Allah ba yanzu AUNTY ce zata ce wai Anna na hadata da mijinta? Anna fa? Hum ta dai ci gaba da yin abinda take yi, wata rana sai labari.
_______________________________
Tunda suka shanyo kwanar gidan su Jafaru Farhana ta zubawa bangaren gidansu ido da mamakin taron da aka yi, alamu ya nuna kauyawa party ake yi, wanda hakan ya sa ta sake zuba ido kida na tashi sama sama ga DG a tsaye da lasifika yana gabatar da nasa aikin dake karawa lamarin kaimi
Motar ya tsayar , hakan ya sa suka fito su ukun sunna kallon yadda yan mata ke rawa irin ta gada, abin ban sha'awa du sun sha ankon zani daban da riga mai dauke da hoton amarya da ango wanda FARHANA ta kurawa hotunan jikin rigunansu ido gabanta na faduwa da karfin gaske...........
Abinda ya sa ake ganin filin ƙarara saboda irin yadda masu kidan suka gyara wajen an bar gaban a bude ne sai kujeru da suka zagaye wajen , mutane na daga ɓangaren kofar gidan su JAFARUN ya zamo sosai ake ganin filin da kyau da kyau
Dg ne ya daga murya yana fadin" Wannan biki na yan gata, biki na dan gata ne, isashe ne wanda ake so, in ba karfin soyayya ba yaya za'a yi a wannan zamanin ka aure kawaye biyu, ku tafawa ango dan Allah, ango mai capacity ya shigo fili da amaransa su cashe, kar a manta idan aka shigo filin nan dan a yi liki ne kawai, capacity capacity..... capacity capacity Yauwa....."
Hannun HALLAH Farhana ta damko da karfi a lokacin da angon ya fara shigowa yana bin kidan capacity din nan yana rawa hadi da daga Babar rigar da ya saka shi da abokansa anko yana rawa hadi da juyi ana ziga shi ana masa kidan capacity capacity.....amaren kuwa su ma kawayensu suka musu rakiya aka bar su a filin angon na casu suma suna yi kowace na son nuna itace ai asalin capacityn
Muryarta na rawa ta ce" Nur, Jafar ne nake gani ?....."
Nur na son kallon inda ta nuna din, kawai FARHANA ta janye kujerar dake gabanta ta shiga ta nufin inda ango ke juyi yana kwaso shoki ana tafa masa.........
Da sauri Nur ta bi bayanta , haka ma A'isha dake waige waige dan bata gane komai ba, su ai ba saninsa suka yi ba bale su iya sheda shi......
ANAS da mamaki ya sa ya fito daga motar ransa bace da nufin kiran su su taho su yi tafiyarsu ne, yana fitowar zai taka ya karasa tafkekiyar motar nan ta parke a Daf da shi, a irin pakawar da tsayuwarta ta gama matse masa wajen da ko shi aljani ne ba zai iya bacewa ba...........
A haukace ya dafe kirjinsa, jikinsa ya dauki rawa a lokacin da idannuwansa suka sauka a cikin na Ogansa , ya masa kallo daya kafin ya mayar da idannuwansa inda yake hange a lokacin da DG ya dakatar da kidan yana fadin" To fah, me yake faruwa angonmu mai capacity jikinsa ke rawa? Ango me ka gani haka ne ? Ga wata tsaleliyar budurwa mai suna capacity a kusa da wannan balarabar......, kar dai ku ma kuna cikin soyayyar angon nan??????"