← Book details Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 101 OF 141

Sashe 101

Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Malan ya girgiza kai idannuwansa na lumshewa sosai ya ce" Jikina da sauki sosai alhamdulilah, abinda na yanke da y'ayana kenan, ki tsaya min koda bana nan, kuma ki bar kukan nan, idan kika yi ta kukan nan su fa? Ki jure, ki min addu'a da sauki sosai kar ki damu da wannan"

Yana maganar kamar wanda ya sha wani abu ne, barci na daukansa , ita kuma tana kallonsa har barcin yayi awon gaba da shi, hakan ya sa ta shiga yi masa addu'a tana ta tofa masa ........

A kofar dakin nasa kuwa suna fitowa , Nur ta yi gaba kamar zata kifa tana rangaji kamar bishiya idan iska na kadawa......., kafarta kuwa dama takalmin wari da wari ne, wato na sulaimana dake kofar dakin abansu ta warta ta haɗa da wani silifas din Aba dake nan........, sai hannunta dake jimke su duka biyu.........

Idannuwansa a kanta har ta bacewa ganinsa....., har ma ya zubawa hanyar da ta bi ido kafin ya maido dubansa inda Anna ke murmushi tana kallon sa ta ce" Ina fata ba laifi da na ce su taho mu je ?"

Idannuwansa ya dan fitar , kafin ya sakar mata murmushin da ya sa itama sake sakar masa wani murmushin a hankali ta furta" Allah ya maka albarka"

Hannunta ya kama ya yi kissing din bayan hannun kafin ya sake kai dubansa hanyar da Nur ta bi ta fita...........

A tausashe ya furta" Ina mota Anna"

Kai ta gyada masa sannan ya juya ya fita .............

A lokacin da ya fito filin asibitin, idannuwansa ya ringa budewa dan ganin abinda bai san shi yake nema ba, har idannuwan nasa suka sauka a kansu ......su hudu................, Nur na tsaye hananyenta harde a kirjinta tana jijiga, Anas ya hade hannaye yana ta magana da karyar da kai, A'isha na yi masa wani kallo mai tafe da harara, Farhana ta kame haba kamar maganar da suke yi na bata mamaki ne ko me???????

A hankali ya dauke idannuwansa, wanda yayi dai-dai da sake duba wajen da Aliyu yayi......

Yana sane ya bar lamarin nan faruwa

Yana sane ya bar abinda yake tarewa faruwa......
Kuma a abinda yayi niya gabanan zai ringa barin irin haka na faruwa......., in sha Allah zai ringa barin haka na faruwa a kan idannuwan da ya dace su gani

A nutse ya nufi motarsa.............., kuma yana zuwa Aliyu dake tsaye ya dan risina yana gabatar masa da dukan bayanan da ya dace ace ya bashi na dukan abinda yake faruwa na harkar kudin asibitin, kudin gwaje gwaje, komai da komai da ya dace ace an biya dan Aban yara ya samu kulawar da ta dace, masu jinyarsa ka su mutun biyu maza majiya karfi kuma likitoci aka dauka........, hakan ya sa a nutse ya shiga yi masa bayani.......sai dai yana gamawa hannunsa kawai ya dan daga masa kafin ya sake juyawa a yanayin da bai san haka ya aikata ba, ya sake zubawa inda bai gane nan yake kallo ba ido, kirjinsa na daukan zafi, zuciyarsa na bugawar da bai san cewa lafiyar ce ta sa haka ba, lokaci daya ya mayar da dubansa kan agogon hannunsa yana yi mata kallon dake nunin kamar yana son gane shin da wani launin fata aka yi ta, fatar wani daba ce aka yi anfani da ita dan kera rantsatsiyar agogon nan...............................

A lokacin ne Nur ta sake duban Anas ranta bace ta ce" Anas, Ni fa ba zuwa na yi nan da mu yi ta cacar baki da kai ba, abinda ya faru tsakaninka da mahaifina nake son sani, dan Walahi na san a banza abanmu ba zai yanke maka hukunci irin wannan ba!"

A'isha da fuskarta ta yi wani irin daurewa ita ma ta ce" Yaya Anas, kai ka san kullum a bayanka nake, ama a yau ba zan iya goyuwa da bayanka ba, maimakun ka ringa bata hakurin laifin da bata san wani iri ne ba ka taimaka ka fada mana abinda ya faru, yaya ANAS abanmu faduwa yayi fa, faduwa yayi, kuma an ce Hawan jini ne, ka taimaka ka fada mana abinda yake faruwa mana dan Allah!"

Ta karashe tana sakin kukan da bata yi ba a Dazu, wanda ganin irin yadda NUR ta rikice ne ita sai ta saki ta yi hakuri ta jure har da Anna tace su taso su je wajen Aban, likita ya nuna a'a fa, ba za'a cika dakinsa ba, ita sai ta hakura tace NUR ta leka musu jikin Aban......Ama a yanzu itama hankalinta ya gama kaiwa cewar ko meye daga Anas ne! To Ama a ina ya ganshi ne?

FARHANA ta sauke ajiyar zuciya tana kalonsa ta ce" Broth, boye boye bashi da wani anfani.........plz ka fadi abinda yake faruwa mana?"

Ajiyar zuciya ya sauke yana duban FARHANA idannuwansa sun gama yin ja kamar zai fashe da kuka dan tashin hankali ya ce" Sisi, mama ce ke son saka ni a halin tashin hankali....., ba yadda ban yi da ita ba, ......"

Ya maida dubansa kan Nur a raunane ya ce" Ba yau da safe nace maki Akoy maganar dake damuna ba wace nake so mu yi?, to maganar ce yanzun ma mama bata bari ba, cewar bata amince da aurena da ke ba har sai har sai............"

Ya yi shiru yana duban A'isha,

Nur a kagauce, bayan ta yi masa duban tsakani ta ce" na dan bata son mu'amalata da kai, saboda ta zo gidan mu ta fadawa mamana da Auntyn mu, .........., maganar da nake son sani me ka yiwa Abanmu da ya zamo a halin da yake ciki ya iya yi n maganar ba Ni ba kai yaya Anas.....?"

Ta karashe a raunane tana murza gaban goshinta zuciyarta na ci gaba da bugawa

A sanyaye ya ce" Ama yaushe aka yi haka? Yaushe maman ta je gidan????"

Ran nur a bace ta girgiza kai, ganin ba amsar da take so zai bata ba ta juya da nufin nufar motar nan da ya kawo su a ciki

Da sauri ya bi bayanta yana fadin" Nur ki tsaya mana mu gama magana, dan Allah kar ki bata ranki a kan abin nan, ko menene zan yi maganinsa, mama kuwa zata je da kanta ta ba Aba hakuri saboda tana son abinda nake so, ki kwontar da hankalin ki, aba ba zai raba mu ba........"

Da wani bacin ran ta juyo, tana rike kugunta da hannunta na dama, da dayan hannun kuwa ya shiga nunawa ranta na tafasa, sannan a yanzu amon muryarta ya dagun da du mai ji zai iya jiyo ta, rai bace ta ce" Kai wani irin mutum ne? Abu daya na roke ka, ka fada min abinda ya haɗaka da mahaifina, ama sai zancen wani shirme wai shi soyayya kake son jaddada min?, Yaya Anas mahaifina ne ke kwance a yanayin da Ni dai ban taba ganinsa a ciki ba, mahaifina mutun ne mai tsananin jure wahalhalun rayuwa, ban taba ganinsa a irin yanayin nan ba, ban taba ganin ya yi gaggawar yankewa Abu hukunci ba, ina fada maka abinda nake son ji wanda shi ne zai sa in ci gaba da ganin kimarka kana min maganar soyayya?, kana tunanin a yanzu da ya yanke min hukuncin nan Ni HALLAH zan kuma dubanka?, in ce maka me? Ka ce min me?, kana tunanin Akoy wani dadi da zaka iya bani a duniya sama da farin cikin mahaifina???????"

Sai wasu hawayen suka bale mata, saboda har cikin zuciyarta take jin radadin wannan wulakancin, gashi ya ku ya fada mata abinda yake faruwa sai zagaye yake da ita

Idannuwansa dake lumshe yana ta kankarar agogon hannunsa ya bude a hankali ya sauke dubansa a fuskar Aliyu, wanda kansa ke ƙasa..........., maganar da yake son fada ya ji ya kasa fada hakan ya sa ya sake kai dubansa a wajen da bai fi taku goma ba da inda motarsa take , gashi kuma ya kasa shiga motar tasa bale ya iya zaunawa..........

Anas kuwa da dan sauri ya ce" ki yi hakuri plz .....Dazu ne mama ta sa muka je wajen Aban, shi ne take fada masa cewar ba Ni ba ke, tace in kuwa ana so mu yi aure sai idan na auri A'isha sannan a bani ke, shi ne nake son kwatanta maki cewar ki kwontar da hankalinki, ran Aba ne kawai ya bace, in sha Allah komai zai daidaita , zamu yi auren mu!"

Jikin Nur ne ya fara yin wani irin sanyi, kafin ya dauki rawa

Bata san lokacin da ta daga murya sosai ba ta ce" ANAS, wace A'isha? ......."

Sai kuma ta kai dubanta inda A'isha ta zarro ido tana ja da baya ta ce" Ke ki bar kalona, ba da Ni yake ba"

FARHANA kam da ta ga expression din Anas sai ta gyada kai ta shiga tafa hannu ta ce" Innalilahi wa Inna ilaihi raj'une, Anas mahaifiyar taka ce ke cewa ka auri A'isha sannan ka auri Nur? Hala bata san A'isha yayar nur bace uwa daya uba daya???? Ko zuwa ka yi ka sanar mata abinda yake faruwa a mention???????"

Anas ya dubi Farhana yana girgiza kai ya ce" Ba fa haka bane, ita ai ta san cewar A'isha yar mama ta mention ce, shi ne take fadan haka, Ama ai Ni ba wani yarda na yi ba!"

Rai bace A'isha ta ce" To ka ma yardan mana, nace ka ma yardan mana......., waye yace maka Ni yar wani ce bayan Abanmu?, to bari ka ji banda wani uba dama da iyayena, Nur kuwa Y'ar uwata ce ta jini ko mutuwa mijinta yayi Ni A'isha ba zan taba aurensa ba!"
Chapter 101 · 0% Book details