Sashe 75
Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Farhana kuwa takan saci duban Nur da du ta zama kamar ba ita ba kafin ta saci duban Anas wanda du ya fice a hayacinsa sai ta tabe baki, karshe ma sai kawai ta shiga tunani kamar haka' Ina, ba zai yiwu ba, kai din banza, ai sam Bama zan iya ganin haka ba, ta bin yan matan ka yi ko ta tsayar da kanka a wajen daya mai daraja, ba zaka taba tsayar da kanka a wajen ta ba, ba zan taba iya saka maka ido kace kana son ta ka hanata ci gaba ba, to kai kowa fa so kake yi, yan matan ka nawa na sani, nawa ka kawo suka gaishe Ni, nawa ka tabawa jiki a gabana, sai yanzu zaka ce.....mtssss no, kandalar Anna baki isa ba, ba nan na ajiye ki ba, no sam ba nan ne ajinki ba, ba zan iya bari ba sai dai wani ikon Allah, idan kuwa kuka fi karfina sai na tabbatar da ya shiryu zai iya baki kulawar da ta dace koda ....kai ina aaaaaaaaaaa!'
"Sister, dama kin san wife dina??" Ya fada a hankali yana duban Farhana da ta share shi yau
Da mamaki ta Dube shi, tana dan zarro ido, ta ce" Wife gaba daya? To kai da kandalar Anna kake so Ama kake abinda na sani sannan baka min biyayya?????, kana da aiki ja a gabanka................Olalalala kana da aiki a gabanka Broth"
Shiru yayi yana tuki yana kallon ta da tsoron kar ya ja maganar ta bude baki tace yana da yan mata da yawa ta balo masa ruwa......., dama har yanzu shi da rigimamiyar tashi bai gama gane inda ta dosa ba bale har yayi wannan garajen......, hum lalle , ashe da yake yiwa sauran yan matansa haka dama suka bashi? Yanzu ga yarinya karama dai yana tsoron ta ji abinda ranta ke iya bacewa, dan bai san irin matakin da zata iya dauka ba........
Nur kam sai ya zama takan kalli A'isha, bakinta cike da magana, Ama ta kasa sakewa harma ta fada kanta tsaye, A'ishan ce ma ke ba Farhana amsa idan ta yi wata tambayar da NUR din ya dace ta bata, har suka shigo cikin baban clinik din ya parker motarsa dai-dai da ta ogansa a ransa yana tunanin kenan OGA na nan? Koda yake dole ma ya zama yana nan, ai matar nan Mama ta gama samun OGA gaba da baya...........
A lokacin da ya tsayar da motar, har cikin ran FARHANA ta so ta bude ta tare Nur su nufi bangaren Emargency din clinik din, sai dai kamar an ce ta kali wajen wata rumfa sai ta hango ya'yanta saman kujera a zaune, Aliyu na daf da shi kadan ya rage tsayinsa ga dukan alamu magana yake yi masa
Haka kawai ta samu kanta da bude motar ta ɗan fara yin gaba kafin ta dakata tana jiran karasowar sauran.......
A'isha ma bayanta ta bi, Nur kuwa na fitowa Anas ya tare mata hanya yana murmushi a hankali ya ce" Bamu gaisa ba fa, ba zaki min magana ba? Ko dan kin gani a wajen aiki ne????, wai me yasa bakya sakewa da Ni ne????"
Nur ta ɗan dago idannuwanta ta dube shi kadan kafin ta kara sada duban nata ta yi dan murmushi hadi da murza gaban goshinta bata ce da shi komai ba
A irin lokacin ne kuma ALIYU cikin girmamawa ya ce" Sir, lokacin hutawarka ya yi, ka ga baka samu barcin kirki ba yau, haka kuma baka ci abinci ba, shayi kawai kake ta sha, me zai hana mu je gida ka yi wanka ka ci abinci ka dan huta sai in dawo da kai????"
Idannuwansa ya dago daga dana wayar da yake yi, ya fara duban Mutalab da du ya yi laushi saboda sunna tahowa ya sa direba ya kawo shi shima, a zuciyarsa yayi niyar cewa ka kai Mutalab ya huta sai ku dawo........yayi niyar tsokanar sa hakan ya sa yayi dan murmushi zai yi magana sai kawai idannuwansa suka sauka a kan FARHANA wace ita ya fara ganewa kafin ya gane ANAS dake yiwa wata budur.......wata........
A hankali ya sake sauke dubansa da kyau a kanta........, lokaci daya ya sake duban fuskar ta kafin ya dauke idannuwansa daga kan nata ya dago hannunsa mai agogo ya dan zubawa agogon jiki ido, a hankali ya sake kai dubansa sakamakon wani abu da ya tino....., abu daya jal da ya tuno wanda ya sa a yanzu kaffafuwansu ya zubawa ido na dan lokaci har ta zagaye Anas ta sake juyawa ta harde hannayen ta a kirji ta yi magana hadi da girgiza kai kafin ta juya tana murmushi ta karasa inda su FARHANA suke tsaye ta saka hannunta a cikin na Farhana suka dauki hanyar da zata kai su Emargency...........
A hankali ya dauke idannuwansa a karo na biyu, wanda tunda yayi kallon farko , ya dauke ya sake yin na biyu Aliyu ya kai dubansa inda yake kallo, saboda ya san maganar da yayi tana da amsa kuma zai amsa ne, sai ya ji shiru, har sai da ya dawo da dubansa a hankali yana yamutsa goshinsa a hankali ya furta " Me ka ce???????"
Aliyu ya dan zubawa bosss dinsa ido, a hankali ya kalli Mutalab da yayi murmushi ya shafa kai ya mike yana fadin" Yauwa bari in zo kuma Ni tunda Farhana ta karaso, bari in amshi sakon nasu a hannun Anas in kai mata, Allah sarki Farhana"
IMAD ya bi bayan Mutalab da kallo da yayi gaba , a hankali ya sake murza hannunsa ya sake maido duban nasa kan Aliyu da ya kuma maimaita tambayarsa cike da girmamawa
Idannuwansa ya lumshe, a hankali bayan ya ji din, cen cikin murya mai nuni da ta masa nauyi a bakinsa ya furta" Idan aka gama gwaje gwajen ma tafi in sha Allah"
Daga haka ya ci gaba da duba wayarsa, ba tare da ya kuma cewa ufan ba, shi kuwa Aliyu sai ya ja ya tsaya nesa da shi kadan cike da tunani kala kala a cikin zuciyarsa
Mutalab na zuwa ya ce da ANAS " Anas kawo sakon nan in rike kawo"
ANAS ya dan fido ido da mamaki yana rikewa ya ce" Kai haba dai OGA, wannan ai aikina ne bari in rike"
Mutalab ya girgiza kai ya rike basket din ya ce" A'a , aikina ne gaskiya, kayan Farhana ne ai, to kuwa Ni zan rike mata"
Anas ya sakar masa a dole sannan ya shiga bin bayansa a ransa yana Ayana ' Dadina da soyayyar larabawa, su fa matansu na iya aiken su, hum bari dai a bani IMTEE, ita da kanta ta isa ta aikeni gaskiya, kut, Ni a yau ma sai na mata siyayya duda ban san kayan nan a cikin wa'inda na siya mata ba, Ama dole ma in je in mata siyayya mai suna siyayya, saboda na kula in har ta sa kaya a nan ne ake asalin ganin wacece ita, tabbas ya yi baban kamu sai hamdallah, yarinyar ga aji, '
Sunna shiga suka samu yan matan ne kawai zaune, an yi kiran Anna dakin da Mama take ta shiga dan ya zamo tana tsaye za'a yi mata wani gwajin, sannan a lokacin likitan kwakwaluwa ya karaso wato na jijiya hade da kwakwaluwa, hakan ya sa tana tsaye aka kai mama dakin skan
Ajiye musu basket din Mutalab yayi sannan ya zauna yana duban Yan matan yayi murmushi ya ce" Plz ki zo mu karasa magana mana FARHANA"
FARHANA dake jin zuciyarta na tsalle du idan ya matse mata waje ta zuba masa ido da kallon tsanaki ba tare da ta mike din ba.....
Anas yayi tsuru tsuru, shi da ya biyo bayan nan fa dan ya sake samun wata dama ne ya kebe da mutuniyar tasa, sai dai a gabansa ana watsa abokin uban gidansa shi din waye shi? Kar dai Farhana ta kara koyawa Nur halayar yiwa samari wulakanci, to shi idan haka ta faru yaya zai yi kenan?
Murmushi Mutalab yayi ya mike ya karaso inda take ya saka hannu ya dauki wayarta ya juya ya fice daga dakin
Da sauri FARHANA ta mike yana zarro ido kasa kasa ta ce" Innalilahi, dan leken asirin ya dauki kwandon asirin, ina zuwa....."
Da sauri ta bi bayanshi hakan ya sa Nur sakin murmushi tana duban A'isha ta ce" Ta ki yarda babu wanda ya Turo bawan Allahn nan, ji take yi wani zai sa ya zo inda take yace yana son ta????"
A'isha ta yi yar dariya ta ce" Ni da kaina ina mamakinta, Nur ki tashi ki je ku gaisa da yaya ANAS mana?????"
Nur ta waiga wajen da yake tsaye yana doka murmushi ta ɗan zuba masa ido
Zata yi magana Anna ta taho tana murmushi ta karasa ta zauna tana rike hannayen A'isha da NUR ta ce" Yan matana, kun ci abincin kuwa????"
Nur ta yi murmushi ta ce" Anna, mun ci fa, kali ma wankin kan da Farhana ta min"
Anna ta ce" Farhanan ?, taho in gani? Duko in gani?"
Nur ta sauka ta duka a gaban Anna a nutse ta janye dan kwalinta baya, dai-dai lokacin da IMAD ya karaso a nutse da nufin zuwa kiran docter, wanda yanzu yanzu ya sanarwa Aliyu su zo ......hakan ya sa kansu tsaye suka nufi ciki dan su karasa wajen likitan
Tsugunon da ta yi, da irin yadda rigarta ta sauka ta baje a kasa da kuma yadda ta mikawa Anna kanta kawai suka sauka a cikin idannuwansa
Tafiyar da yake yi ya ja ya tsaya , wanda ta sa Aliyu ma tsayawar, sai dai da ya duba dan ya ga ko wani ya tare musu hanya sai shi ma idannuwansa suka sauka a yanayin nan
Yanzu ma idannuwan ogansa ya ƙalla, sai ya ga a inda idannuwan nasa suke, hakan ya sa da mamaki ya sake juyowa ya kuma duban IMAD wanda ya dauke dubansa ya kai kan agogon da sam ya rasa duban me yake yi mata...................
A nutse Aliyu ya shiga yana yin Salama a hankali, ya dubi Anas dake wajen
A nutse ya karasa inda yake ya ce" Ka dan fita waje, Sir zai je ciki ne"