← Book details Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 141

Sashe 19

Kisan Mummuke Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Anna ta yi murmushi tana sake riƙe litafin hadisin ta ce" Baki san cewa a makarantar nan ko wani aji kake idan kana da abinda ya shige maka duhu kana da damar zuwa ka fada, kuma za'a kula da kai har sai ka samu haske a lamarin? Ko kin san cewa a sababin dokokin da aka zuba bama za'a amshi dalibin da bai iya tada baƙi ba?, idan kuwa iyayensa suka nace a dauke shi sai sun saka hannu cewar aikin ba na makaranta kadai bane a dan kankanin lokaci ya iya tada baƙi ta yadda karatun ba zai bashi wahala ba?, yaya ake yi kuna iya shanye abcd kamar ruwa ba wahala aman alif ba'un ta'un ya zamo rikicin kwakwaluwar ku bayan duniya din nan hanya ce da muka shigo zamu wuce mu je inda zamu yada zango, wanda a hanyar nan tamu ne zamu yi guzurin abinda muka ga ya fi yi mana ta yadda zamu samu wajen zama a inda zamu tarda matsayin sakamako wato wuta ko gidan aljana?"

Imtee kawai ido ta zubawa matar ta kasa motsi, har sai da Anna ta ce" Hey....., kina fahimtar abinda nake fada kuwa? , shekarun ki nawa??"

Bakin Imtee na dan rawa ta ce" Sha....sha.....sha tara"

Anna ta lumshe idannuwanta, a hankali ta ce" To shikenan, its ok, kar ki saka tsoro a ran ki, in sha Allah kafin a zo tantance yan aji zamu yi kokari Ni da ke ya zamo kin karanta du inda za'a bude maki kin ji?"

Da dan tsoro Imtee ta ce" Tantancewa? Muma dake cikin makarantar a cikin hatsari muke mama? Ana iya korar mu?"

Anna ta fuskance ta, a tausashe ta ce" Kun fi kowa zamowa cikin hatsari, bale idan har baku mayar da hankali ba, akoy jarabawa da za'a ringa yi du wata uku uku, wace idan aka fuskanci kawai kai baka son karatun ne za'a salame ka, har sai iyayenka sun zo da kai ka fada da bakinka cewa zaka gyara, da wannan za'a baka dama , idan ka gyara sai a ci gaba , in baka gyara ba sai a salameka gaba daya, mai makarantar ya fada ne ba zai dauki du wani lako lako ba, du Wanda ya kawo d'ansa ya tabbatar da ya kawo shi a koya masa kuma zai dage ya koya.....ke Bakya sha'awar son ganin ki gobe a musabaka? Ko Bakya sha'awar ace gobe ga ki nan a Saudiya kin ciyo mana baban rabo....? Yaya sunnan ki ma????"

Imtee ta ɗan bude bakinta a hankali ta ce" Im....immmteee"

"No na kirki nake son ji" Anna ta fada a tausashe

Imtee ta ce" HALLAH ne"

Anna ta yi murmushi ta ce" Masha Allah, kin san tarihin mai sunnanki kuwa?"

Imtee ta girgiza kai

Anna ta ce" mu yi karatun idan muka gama sai mu je in baki dukan abin bukata na karatun, sai kuma mu ɗora lokacin da zan ringa koya maki kulun a nan, ya zamo idan aka tashe ku ne, ko kafin a shiga aji ne, ko dai-dai lokacin da ake baku na hutu da cin abinci... Kin amince?.."

A hankali Imtee ta gyada kanta sannan ta gyara zamanta ta nunawa Anna wajen, Anna ta shiga koya mata a hankali , a nutse, hade da fasara da komai, wanda minti ashirin tuni har ta shanye ras ya kuma zauna a kanta , a lokacin ne Anna ta mike ta fara yin gaba a nutse, Imtee na biye da ita cike da mamakin wai wacece matar nan? Suka nufi baban office din makarantar tana kula du inda suka zo ma'aikata sai su miko gaisuwar girmamawa har suka je kofar office din ta ga ta saka yar yatsarta wajen empreinte ya bude ta shige kafin ta juyo dan ganin idan imteen tan shigo, nan ta ga ta tsaya tana kallon ta ta kasa shiga din

Nikaf din fuskarta ta dage, yayi dai-dai da bugawar zuciyar Imtee sakamakon kyakkyawa, ni'imtaciya, sananiyar fuskar da ta bayyana a gabanta mai cike da kamala wace tsoron tashin hankali ya kamata a lokacin da ta gane dama fuskar nan fa ta taɓa gani sau daya jal a lokacin da aka musu wata gabatarwa ta baban screen din computer matar na murmushi kamar a fuskarta aka zano shi, sai hannun namiji a gefen kafadarta rike da nata hannun wanda ta ɗan daga ta sama sama haka ta rike, Ama nasa ya cika nata sosai alamu na namiji ne kuma namijin ma ba karami ba, sai muryarsa da ya yi larabci wanda suka jima suna kus kus din ai Balaraben Saudiya ne, meye meye dai sanadiyar basu da amsa suka zubar da zancen suka dangana.....

A hankali ta ɗan daga kafarta da nufin yin baya

Ku gane, ire Iren maganganun dake tashi a kan dangin baiwar Allahn nan ba kadan bane, kai hatta uwar dukiyar da ake hange daga waje ba'a riga aka shiga cikin gidanta ba cewa ake yi wai harda yankan kai suke yi......to ita ta ina, ta yaya zata yarda ta shiga office din nan daga ita sai ita ta wule kanta????

Kara daga kafa daya ta yi ta yi baya jikinta na rawa.....

A taudashe Anna ta furta" HALLAH, Bismillah????"

Imtee ta girgiza kai a hankali, kafin ta juya da sauri ta yi gaba harda dan gudu gudun ta.

Anna ta bi ta da kallo kafin ta yi murmushi ta rufe office din ta karasa ta yi bayi dan dauro alwallah domin lokacin sallahr azahar na kusa, ita kuwa dama takan yi alwallah ne ta yi jiran SALLAH wani lokacin har awa biyu saura ko fiye da haka.....

Imtee kuwa du ba a cikin hayacinta ba ta fice a makarantar da dan sauri domin lokacin sauka ya yi bai fi minti ashirin ya rage a sauko su ba, hakan ya sa mai tsaron dan matsawa saboda get dama tunda aka fara aikin nan a bude yake sosai ana kai kawo da harkar kayan gine gine

Cikin sanda ta fito a hankali ta dauki hanya tana tafe tana dan waige waige dan gudun kar ta hade da masu kula da su a cikin makarantar .................

Daf da ita yayi parking din motarsa, tunda ta fito ya saki murmushi domin ya fi minti talatin a kofar nan yana jiran tsamani dan a jiya da dare da ya matsawa Fa'iza kan lalle lalle sai ta raka shi gidan su ko ta bashi numbarta , fa'izan tace yayi hakuri yau ya zo su hadu idan ta bada damar ya je gidan su sai ya je, bata da waya an hanata rike waya a gidan su kwata kwata........

Tsorata ta yi sosai da farko, sai da ya zuge madubin motar ne ta ga ko waye sannan ta sauke wata boyayiyar ajiyar zuciya lokaci daya tana furta" Da kai ne.....?"

Da alamun tambaya ya ce" to wa kike jira da?, waye ya biyo ki kika Tsorata haka?"

Tana dan haki ta girgiza kai hadi da fadin" Ba komai "

Murmushi ya yi ya ce" Zagayo ko shigo mana in kai ki gidan , yau ke daya ce???"

Motar ta bi da kallo, a cenn kasan zuciyarta take jin kamar ba dai-dai bane haka kawai ta fada motarsa , domin bata ga wata shakuwa ko dalili mai karfin da zai matse musu waje har haka ba, sai dai hudubar maman yara ta gama rike mata zuciya a lokacin da ta tuno bayanan ta, da irin yadda ta nuna mata tashin hankalin da take ciki na rayuwa wanda ta tabbatar mata idan ba ita ba waye zai fitar da ita daga kangin talaucin nan ne? Sai kawai ta sake duban fuskarsa a hankali ta ce" Motar taka kake so in shiga????"

Kai ya langwabar, a matukar raunane ya ce" eh, idan har kin yarda da Ni, ki yarda cewar son ki nake yi, ba zan iya cutar da ke ba, ki shigo Mu je dan burina in adana ki , in hana ranar nan dukar min wannan fatar taki mai tsananin haske da shiga zuciya........"

Tunda Imtee take bata taɓa soyayya ba, bale har ace wai irin kalaman nan ba zasu shige zuciyarta ba

Kwarai suka shige zuciyarta da gudun gaske har ta ji numfashinta na karbar kalaman da kyau da kyau

A hankali ta zagaya ta saka hannu ta bude ta shiga motar hadi da rufewa sannan ta rintse ido tana sauke ajiyar zuciya

Wani farin ciki ya ringa ji a zuciyarsa da tunanin ashe ba zata masa taurin kai ba......? Ta yiwu itama ta gama kamuwa da kaunar tasa.............

Da kula ya ce" Shashekar me kike yi haka ? Me ya koro ki?"

Gaba daya ta manta cewar a gidan matar da take gudu yake aiki, sai kawai ta gyara zama irin hankalinta tashen nan ta shiga koro masa bayanan yadda suka yi da Anna, gaba daya ta karashe da fadin" Ban san ita bace, da ba zan taba yarda mu yi doguwar fira haka ba, ta yiwu ta mana min Numbar yan yankan kai a jikina ta yadda da sun gani zasu gane Ni? Dan Allah duba ka gani? Cewa ake yi dukiyar mutanen nan harda tsafi a cikinta!"

Ido ya fara zarowa jin kalaman ta, kafin ya ce" Kina nufin Anna ce ta yi maki magana da doguwar fira haka har ma tace ki shigo office din ta kika gudo?"

Imtee ta zuba masa ido ta kasa amsa shi, saboda a bayane yake yannayin maganarsa wata iri ce, ita gaba daya ma bata san wace Anna ba, sai kuma tunawa da ta yi cewar shi fa ma'aikaci ne a gidan mutanen nan sai ta ji jikinta ya yi sanyi

A hankali ya ce" Waye yace maki jita jita kowace ake kamawa?????, Dube Ni, fuskance ni ki ji, shin zaki iya yarda da maganata kuwa? Look at me NUR "

Duban nasa ta yi ido cikin ido, domin ya kama sunan da du idan aka fada sai ta tsayar da abinda take yi ko menene
Chapter 19 · 0% Book details